CHAPTER EIGHT

478 28 0
                                    


        S.A yace "Haba Aliyu meh haka? Kai da yakamata ka tsaya kaji meh yafaru before taking any action amma kawai sai ka fara zaneta, gaskia banji d'adin wannan abun ba, idan badan kai yayanta baneh Allah da sai mun b'ata"
   Aliyu hararan sa yayi yaja dogon tsaki yace
"Kaga please let me rest bana son wani headache"
"Ohk tunda haka kace, but please karka kuma dukan mun mata"
Aliyu a ransa yaji maganar amma ya dake yayi shigewar sa d'akin, S.A girgiza kai yayi shima yafita a gidan.....

       Fido zaune take akan gado tana shafa Robb ajikin ta dan ba karamin jin jiki tayi ba, wani farin ciki takeji koh ba komai tayima  Meena duka, gani take daga yau sun raba raini.
     Wayar ta neh ya dawo da ita daga dogon tunanin data fad'a, S.A tagani baro baro kan screen. "Yaa Salaaam" ta furta a hankali, zatayi receiving call d'in sai kuma ta fasa
"Mtswww yaga Aliyu yana duka nah ai da kunya, kai wlhy Yaya Aliyu yakawo mini cikas, ai wannan aji down neh" haka tabari wayan yata ringing bata d'aga ba...

    Can bayan ta kwanta taji message yashigo mata waya, ita duk a tunanin ta zataga number S.A, sai dai kuma code na Nigeria da tagani, bud'e wa tayi taga message:  _Mesa kike zuwa cikin mafarki nah and my thoughts every blessing day, WHY???????_

     Tsaki taja ta kunna data na wayar ta tana ganin trailer wani sabon film Haseena, sai can tak'ara jin message yashigo wayar ta. Bud'ewa tayi taga same number: _Kina saka ni cikin damuwa and dilemma, why HAYAATEE?_
  Wani dogon tsaki taja tace koma waye saidai ka cinye kanka tayi blocking number.........

    
       Tun daga lokacin Meena tana mugun shakkan Fido sabida tasan ba meh kwatar ta amma ta rantse da Allah duk ranar da suka koma gida Nigeria she must regret tab'a mata skin da tayi, ta ayyana a ranta har Aliyu bazata barshi ba tunda ya nuna mata a fili ba ita yakeso ba abunda yake cikin ta yakeso.

      Fido karatu take ba kama hannun yaro, takan bincike akan Issam wanda taji labari gidan su yanxu yana abuja. S.A kam ya koma Nigeria amma kullum suna cikin waya da Fido, yake ce mata tana dawowa za'ayi maganar auren su.. Itadai saidai tayi murmushi dan har ga Allah S.A yakai namijin dazata So shi!!!!!!!

        _Bayan Shekara d'aya_

     Nigeria

  Umaru Musu 'Yar aduwa Airport

      General Aliyu neh rik'e da kyakkyawan baby girl a hannun sa, gefen sa na dama Fido ce tasha bak'in sunshade, da doguwar riga ready made purple da flowers yellow tayi rolling da black veil da takalmi da jakanta shima black, ba karamin kyau tayi ba, sai nace weather UK ya karb'eta sosai, by his left kuma Meena ce tayi jiki sosai, sai wani shan k'amshi take tana hura hanci a dole ita meh miji da baby itama ba laifi ta k'ara haske duk da ma tun da fara ce, sai idon ta k'anana da yak'ara shiga ciki dan jikin da tayi..

     Shamcy da gudu tazo ta rungume Fido tace
"Wow sis kinyi kyau, gaskia UK ta karb'e ki sai kace ba karatu kikaje ba"
  Fido taja hancin ta tace
"You can at least say Welcome first!?"
"Sorry Sis! Welcome "
"Thanks"
      Shamcy ta gaishe da Meena wanda dakyar da amsa, ta gaishe da Yaya Aliyu ta karb'a babyn hannun sa tace
"Wow Mashaa Allah Yaya kuna kama da Basma amma hasken Anty Meena tabiyo"
"Ke ke ke ban daughter nah bana son jagwalgolo" cewar Meena. Shamcy jiki a sanyaye ta mik'a mata Basmah ta wuce wajen Fido da Yaya Khaleal.
Fido tayi dariya tace
"Maganin ki nan gaba ki k'ara kinji, da maitan ki na son yara d'in". Shamcy dai shuru tayi batace k'ala ba sai wani tura bakin da take.

Fido da Shamcy shiga motan Yaya Khaleal sukayi, su Aliyu kuma suka shiga motan Teema.

        Fido tana shiga parlour taga Inna da remote a hannu tana kallon B4U Movies, da gudu taje ta rungume ta tace
"Inna keda India sai kace kina jin yaren"
"Ja'iran yarinya ai kin tsorata ni ya kasar waje ya karatu?"
"Alhamdulillah Inna"
"Kai Mashaa Allah kin ganki kuwa, kin k'ara kyau lalle Aliyu yana kula dake sosai, tunda Allah yasa kin dawo sai maganar auren ku"
"Aure nah da waye kuma?"
"Kuji 'yar iskar yarinya, tambayata ma kike?"
"Kinga Inna I don't have time for this, let me freshen up"
  Barin ta tayi tashiga d'aki tayi wanka, bayan ta fito tayi sallah. Shamcy ta zauna kusa da ita tace
"Adda Fido ina tsarabar mu?"
"Mtswww ke kyale ni ba yau ba, ina SIM card da nace kimun register?"

HAYAATEEY (Completed✔)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang