NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
SOYAYYA CE
ALKALAMIN MARYAMERHABDUL
1- ELMANSOORElmansoor jingine yake jikin mota yana waya, bazaka tab'a gane yanayin da yake ciki ba. Farinciki yake ko akasin haka, babu alamu a fuskarsa, ya dai yi shiru yana sauraran abinda ake sanar dashi a wayar.
Saurayi ne mai kimanin shekaru 27, ba bak'i bane sannan baza a kirashi fari ba, jinginuwan da yayi bai hana nuni da shi d'in mai tsawo bane, fuskarsa kuma dogon hancinsa zaka fara gani sannan ka kai ga idanuwansa wanda ya k'ara masa kyau, k'asumbarsa da ya sha gyara sai yalk'i yake ya k'ara bawa halittar fuskarsa fitowa da kyau.
Ya kai mintuna 5 tsaye da wayan a kunnensa sai dai yace um ko um um bai iya furta komai ba. Toh meh dama ake tsammani daga wurinsa bayan hakan? Yaro ga kyau, ga kudi, ga tak'ama da k'asaita, kallonsa farat d'aya zaka gano hakan.
Sanye yake da blue shirt mai zane fari sai wandon jeans da takalmansa masu nuni da gidan naira. Fahad ne ya fito daga gidan da yake facing Elmansoor, ba tare da yayi masa magana ba ya bud'e gidan gaba ya zauna.
Ba tare da ya kashe wayar ba ya shiga mazaunin driver ya fara driving a hankali, har a sannan bai furta ko da kalma d'aya ba yana sauraren d'aya b'angaren.
"Ni bana ma jinki fah"
Ya tab'e baki had'e da danna wayar ya kashe.Can ciki ya ja tsaki yana mai k'ara gudun motar nasa, babu wanda yayi magana cikin motar har ya isa bank yayi parking.
"Fahad zamu shiga ne ko kana jirana anan?"
Kallon fuskar Fahad yake yayi maganar, hannunsa sak'ale a mab'allin k'ofar motar."Dama da kace in rakaka ajiyeni zakayi a mota? ko dan an b'ata maka rai zaka huce kaina?"
Bai jira amsar Elmansoor ba ya fice had'e da rufe k'ofar.Kimanin awa d'aya sukayi a banki suka fito babu wanda yake yiwa d'an uwansa magana.
******
Wani tankamemen gida ya tsaya bayan ya yi horn a bakin gate. Sakanni kad'an mai gadi ya bude bayan ya tabbatar da yasan mai motar.
Kai tsaye ya shige cikin gidan bayan ya yi parking, ko jiran abokin nasa baiyi ba bare ya kulle motar. A main parlour ya had'u da momynsa na kallo, ya d'an russuna alamar girmamawa
"Sannu da hutawa mommy"
Ya furta yana mai k'awata fuskarsa da murmushin da bai kai ga zuciya ba. Bai tsaya wani hira da ita ba ya wuce d'akinsa.K'ofar d'akinsa Fahad ya kwankwasa yasa kai ba tare da ya bashi izini ba, sanin cewa ba amsawa zaiyi ba muddin yana wannan halin.
Wuri ya samu a gefensa ya zauna yana fuskantarsa
"Wai Elmansoor meh ya faru ne?"
Jin shirun da yayi ya bashi damar cigaba da magana
"Ka kirani d'azu lafiya k'alau, daga fitowana daga gida sai in ganka a murd'e, lafiyanka kuwa?"Kwanciya yayi yana mai juya masa baya ba tare da ya amsa masa tambayoyinsa ba. Tsaki Fahad yayi yana mai d'aura hannunsa a kafad'arsa had'e da juyo dashi dan su fuskanci juna.
"Common tell me, meh problem na Jamila this time?"
Kaman an mitsine shi ya zauna yana cewa "Problem nata daya, irin na kowace mace, bansan ko nine bana dacen 'yan mata ba"Yayi tsaki tare da dafe kansa da dukkan hannayensa. Fahad murmushi yayi mai sauti yana girgiza kai.
"Elmansoor ka koyi yanda ake canjawa tun wuri dan wallahi mata basu son irin halin nan naka, muddin kanason ka samu mace toh dole sai ka canja"."Fahad kafi kowa sanin waye Elmansoor Yuri, and am not willing to change, infact i promise myself to be that way har sai nayi aure, akan meh zan nunawa mace so tana waje? Bani da wannan lokacin. In na aureki baki ga na nuna miki so ba kiyi complain kina da gaskiya amma kina girlfriend dina sai kiyi ta min surutu, wai sai na kiraki kullum kuma kullum sai nace miki i love you, to hell with that idea, mata basu ganewa ko kad'an".
Fahad da yake yasan abokin nasa baiyi mamakin furucinsa ba bare yayi k'ok'arin fahimtar dashi abunda ya kasa ganewa.
"Allah ya bada sa'a toh".
Fuskantarsa yayi yana mai nazarin kalaman da yake son furtawa abokin nasa.Can ya nisa yace
"Kai ka fad'a mata ra'ayinka mana, in tana sonka ai zata gane, kuma ma ai gaskiyanta ne bata yi k'arya ba, ni banga laifinta dan tayi maka maganar rashin damuwan da baka yi da ita ba, ko ni nan bansan yanda kake sonta ba, ai ba a haka Elmansoor"Ganin alamar Elmansoor zai tanka yasa shi d'aga hannunsa dan dakatar dashi, "Kawai dai ka fad'a mata yanzu dan a samu zaman lafiya, ni ban ga laifinta ba, in akwai mai laifi anan toh kai ne, kuma ya zama dole ka gyara komai in kana sonta da gaske".
Kallon da Elmansoor ya watsawa Fahad kad'ai ya nuna k'in amincewar shawararsa.
"Wannan ai ba shawara bane so kake kawai ta raina ni, kai kasan meh kake cewa ma kuwa? Sai in zauna zaman yi mata jawabi? Akan meh?"Bai tambaya dan neman amsa ba, kwanciyarsa ya koma yana mai lumshe idanunsa, Fahad kuma wayarsa ya janyo yana mai gyara zamansa a gefen gadon.
~~~~~~~~
1sh chapter is here💃🏼
Kunsan Editing yafi sabon rubutu wahala? Ohh🤥 har naji kaman kada inyi aswear.
But ya na iya tunda na fara?
Sai dai please shower your love with comments on every line, vote and share with your love ones.Thank you 😘😘😘
MaryamerhAbdul 💯
YOU ARE READING
SOYAYYA CE
Romance"Zan dawo miki pretty, Elmansoor is yours, yours alone, banson kukan nan kina karya min zuciya in kinayi, let's be strong, ba'a tab'a samun abu meh kyau sai ansha wahala. Zan tafi in baki sararin yin duk yanda kikeso dan bazan iya ganinki haka ba Ai...