"Ina jinka".
Ta furta tana mai gyara zamanta akan gadon d'akin, hankalinta da dukkan nutsuwarta ta mik'a masa kamar yanda ya buk'ata."Kinsan dalilin da yasa na k'iraki, so nake muyi maganar da zata sa mu saita tunanin Elmansoor, abokina ne, na sanshi fiye da sanin da kikayi masa, gani nayi abunda aka sha yi yana neman maimaita kansa duk da a wannan karon ya banbanta daga wurin nasa".
Shiru yayi bai cigaba da yi mata bayanin da ya d'auko ba, ya zai fara mata bayani a dagule kuma ya tsaya a tsakiyar hanya? Duba fuskar wayar tayi ko wayar ce ta tsinke bata lura ba.
"Ban gane ba, kayi min yanda zan gane Fahad"
Ta furta bayan ta mayar da wayar kunnenta.Numfashi ya sauk'e kana ya cigaba da maganar, zuciyarsa na wasu-wasin hukuncin da ya yanke ba tare da sanin abokin nasa ba, anya ya kyauta masa? Wani sashen na zuciyarsa na nuna masa dacewar hakan.
"Abubuwan da ke faruwa tsakaninki da Elmansoor nakeson gyarawa, gani nayi dukkanku babu mai shirin gyarawa, naga rashin dacewar hakan shine na kawo d'auki amma ta wurinki, dan ina da tabbas da abokin nawa, kece dai ban sani ba".
Idanunta ta juya kamar yanda take juya maganarsa a k'asan zuciyarta.
"Bazan ce ban gane maganarka ba Fahad, amma ina son gane abubuwa dangane da abokin naka, gaskiya ina mamakinsa, bazan b'oye maka ba ina shakkun son da yake cewa yana min, asalinsa haka yake ko kuwa ni kad'ai yake yiwa haka?"."Meh yake miki wanda ban sani ba? Ki sanar dani".
"Bai k'irana, bai min hiran da zamu fahimci juna, komai nashi daban kawai, ya zaka so mutum kana fatan aurensa ka kasa bashi daman ya fahimceka kai ma ka fahimcesa? Meh anfanin furtawa juna kalmar so in fahimtar juna bazata biyo baya ba? Da wurin babana yazo kawai aka aura min shi bansan da maganarsa ba akan haka, dan ban ga anfanin soyayyar ba".Murmushi Fahad ya sake yana mai jinjina irin tunaninta a shekarun da take dashi.
"Malama Aisha kenan, duk cikin 'yan matansa ke kad'..."
"'Yan matansa kuma?". Ta katseshi muryarta na rawa tana mai ware idanunta, zuciyarta kuma na sanar da ita kinyi kuskure, dama namiji kamar sa dole ya ajiyesu da yawa. Hawaye ta ji yana barazanar zubo mata tayi saurin sharewa da bayan hannunta.Dariya ne ya kubce masa, muryarta kad'ai ya tabbatar masa kishin ne ya motsa, shi ko bai fad'a da wani manufa ba sai don yayi mata bayanin da bata sani ba game da Elmansoor.
"Haka kike da kishi?" Ya furta bayan ya tsagaita dariyar.
"Mamaki dai nayi ba kishi ba, taya mutum irin sa zai iya tara 'yan mata"."Ok, ba wai ina nufin yanzu haka yana dasu ba, ina nufin duk 'yan matan da yayi babu wacce ta tab'a tunani irin naki, kuma ina kyautata zaton kece kad'ai zaki iya zama dashi a hakan, clear your mind".
"Ban gane ba, asali haka yake?"."Eh toh zan iya ce miki haka yake in rashin magana ne, amma rashin kulawa ne gaskiya ba halinsa bane, babu d'an Adam a duniya da Allah bai sawa feelings ba sai dai na wani yafi na wani, ra'ayinsa dai da wasu dalilansa suka sa ya zama haka, kowacce mace yake wa haka kuma dukkansu dalilin rabuwansu kenan rashin damuwa dasu".
"Zan iya sanin dalilan nasa? I want him to change".
"Kafin nan, ina son ki yadda da abu d'aya, Elmansoor na sonki, ni nasan meh na gani yasa na fad'i haka. Jiya kafin in k'iraki ta wayan Mufeedah ni kad'ai nasan abunda ya faru wanda ko da wasa bai tab'a yi akan wata mace ba sai akanki, dalilina ma kenan na k'iranki yau, banson kiyi tunani irin na sauran na tafiya".
ESTÁS LEYENDO
SOYAYYA CE
Romance"Zan dawo miki pretty, Elmansoor is yours, yours alone, banson kukan nan kina karya min zuciya in kinayi, let's be strong, ba'a tab'a samun abu meh kyau sai ansha wahala. Zan tafi in baki sararin yin duk yanda kikeso dan bazan iya ganinki haka ba Ai...