2. Aisha

2.6K 133 11
                                    

"Dan Allah ki tashi mu fita strolling"
Aisha ke maganar da Mufeeda bayan ta fito daga d'aki ta samu Mufeeda kwance akan kujerar falo tana karatun littafin hausa. Wuri ta samu a gefenta ta zauna ta cigaba da cewa
"Na gaji da zama wuri d'aya Allah" tana mai turo baki ta fad'i hakan.

Ko kallonta Mufeeda bata yi ba tana mik'a hannunta cikin bowl din da ke cike da magarya tana kaiwa bakinta, idanunta akan littafin da take karantawa ko kiftawa batayi, littafin ya tafi da ita da alama.

Aisha kallonta take yi tana mai tunanin abunda ya dace tayi mata a wannan lokaci dan ita ma taji kwatankacin b'acin ranta na k'in amsata. Mik'ewa tayi ta warce littafin sannan ta sa gudu ta shige dakinsu.

"Amma Aisha kin raina ni, zan ko b'ata miki rai yau d'in nan".
Ta mik'e rai a b'ace ta bi bayanta tana mai cigaba da mitar abinda Aisha tayi mata.

*****

Mintuna 20 suka fito kowacce sanye da abaya bak'i da takalmi lophos, babu abinda suka rik'e a hannunsu sai wayoyinsu da ke rufe da fancy covers masu adon stones sai shek'i suke.

D'akin Mama suka wuce dan sanar da ita fitan da zasuyi.
"Toh a dawo lafiya kuma kada kuyi nisa, kunga 4:30 ya gota" ta nuna agogon bangon da ke mak'ale a saman gadonta ta fad'i hakan.

Fitowa sukayi suna taku a hankali suna hira tsakaninsu kamar ba su sukayi fad'a ba.

Aisha da Mufeeda yara ne kaman tagwaye dan kamannin da sukeyi, saidai d'aya tafi kauri da haske, chocolate colour suke kuma kyawawa ne na k'in k'arawa. Mal. Musa shine asalin sunan kakan Aisha wanda aka fi sani da Nemi, matarshi d'aya da 'ya'ya uku.

Hajara itace farkon 'yarsa sai Abdullahi mahaifin Aisha kenan sannan Amina wacce ake k'ira Auta. Asalinsu 'yan garin Damaturu ne, a can aka haifesu suka taso cikin 'yan uwa. Akwai tazara mai yawa tsakanin yaran guda uku, dan Hajara na da shekara 9 sannan akayi mata k'ani Abdullahi, shi kuma na da shekara 11 saka yi masa k'anwa bayan an fidda tsammanin sake haihuwa.

Hajara na gama secondary school aka yi mata aure da Yunusa, auren soyayya sukayi dan sun had'u lokacin da yazo NYSC makarantarsu, d'an Kano ne, a lokacin tana aji 5 na gaba da firamare wato Ss2, bayan ya koma gida soyayyar bai tsaya anan ba yayi tattaki har zuwa wurin iyayenta dan neman izini, daga k'arshe iyayensa suka shiga maganar aka d'aura musu aure bayan kammala makarantarta. Abdullahi na junior class lokacin.

Mahaifinsu na da wadata, dan yana sauk'e duk wani hak'k'i da ke rataye a wuyarsa, na dangane da tufafi, abinci, magani, muhalli mai kyau da dai sauran abubuwa na rayuwa, suna da fahimtan juna tsakaninsu, gida ne da ke cike da soyayya, tausayi da kuma jin k'ai.

Lokacin da Abdullahi ya gama secondary school ya fito da sakamako mai kyau, hakan yasa aka nema masa university a can Kano B.U.K kenan, da taimakon mijin yayarsa ya samu admission inda ya samu gurbin karanta business administration.

Sosai Hajara tayi murnar dawowarsa Kano wurinta, a lokacin tana da yara biyu, namiji mai suna Nu'aim sai k'anwarsa Zainab.

Cikin shekaru hud'u da 'yan kai Abdullahi ya kammala karatunsa lafiya, ya dawo gida cike da murna da fatan samun sakamako mai kyau.

Mahaifinsa yayi murna sosai da dawowarsa, dan Abdullahi ne tilon d'ansa kuma yana matuk'ar k'aunarsa dan biyayyarsa garesa. Kud'i mai d'imbin yawa ya damk'awa Abdullahi dan yaja jari ya rik'e kansa, shi a nashi bai son d'ansa yayi aikin gomnati. Ra'ayinsu yazo d'aya da Abdullahi, tuni ya kama sana'a yana mai anfani da dabarun ilimin da ya karanto a makaranta.

Abdullahi yayi namijin k'ok'ari wurin tafiyar da kud'in yanda ya kamata, a lokaci k'alilan kudin yayi albarka ya fara sayan filaye yana sayarwa.

Bayan shekaru biyu da kammala makarantar Abdullahi Amina k'anwarsa ta gama nata makarantar, kamar yanda akayi wa Hajara aure haka ita ma aka umarceta ta fidda miji, batayi k'asa a gwiwa ba ta fito da gwaninta, anan Mahaifinsu ya umarci Abdullahi fitar da mata dan a had'a auren gaba d'aya ganin yana aikinsa zai iya rik'e kansa da matarsa.

Alankatafir Abdullahi yace baisan da zancen ba, shi bazaiyi aure ba, aka kad'a aka raya yace inaa shi bazaiyi aure ba, ya fad'i dalili kwak'k'wara yak'i bare a bashi lokaci, ganin bayi da dalili yasa iyayensa suka jajirce akan bakansu, sun nuna b'acin ransu sosai sannan ya amince da maganar auren, sai dai ya nemi alfarmar su kawo matar da zai aura dan bayi da wacce sukayi maganar aure, zai iya cewa ko budurwa bayi dashi.

Maman Abdullahi tayi murna sosai jin zancensa, dan dama akwai 'yar k'anin mijinta wacce ta kasance 'ya ga aminyarta da take masa hari tuntuni mai suna Asma'u.

Lokacin da aka tuntub'eshi da maganarta dan jin ra'ayinsa game da ita ya tabbatar musu bayi da matsala da zab'insu, bare Asma'u da ta kasance kamar k'anwarsa, ya amince d'ari bisa d'ari baiyi gardama ba.

Ba'a b'ata lokaci mai tsawo ba aka shiga hidimar biki, ranar juma'a aka d'aura aurensu bayan an sauk'o daga sallar juma'a. Sai dare aka kai kowacce d'akinta kamar yanda al'ada take. Amina k'anwar Abdullahi k'awa ce a wurin Asma'u ko ma ince aminai ne kaman yanda iyayensu mata suke.

Ba'ayi shekara ba asma'u ta gama kanainaye zuciyar Abdullahi kamar da yaddarsa akayi auren, da yake asma'u yarinya ce mai shiga ran mutum nan da nan Abdullahi ya dulmiya cikin kogin son matarsa.

Shekara d'ai-d'ai har uku ko b'ari babu wacce tayi acikinsu, ya kai ga dangin mijin Amina sun fara k'orafin ya auro juya, kwatsam rana tsaka Amina ta tashi ba lafiya, mijinta ya sungumeta ya kaita asibiti, anan ne aka tabbatar masa tana da ciki 2months, sunyi murna sosai Amina harda hawaye lokacin da ta k'ira aminiyarta ta sanar da ita abun farincikin da ya sameta, ta tayata murna sosai ita ma lokacin ciki ne manne k'asar mararta bata sani ba.

Wata tara cif da kwanaki Amina ta fara nak'uda da misalin k'arfe 3 na dare, ciwon nata yayi tsanani samnan mijinta ya samu motar da zai kai ta asibiti. Kafin su isa ta jikita jini ya b'alle mata, iya tsurewa mijinta ya tsure ganin halin da matarsa take ciki.

Suna isa aka shige da ita d'akin haihuwa, likitoci sunyi iya k'ok'arinsu ta haihu da kanta abun yaci tura, sai da akayi mata aiki sannan aka samu damar fidda 'yarta samb'aleliya, sai dai ita Amina lokacinta yayi ta koma gidanta na gaskiya.

~~~~~~~

Drop your comment,
Like and share with your love ones
Thank you.

SOYAYYA CETempat di mana cerita hidup. Terokai sekarang