"Mr. Elmansoor Yuri, wai haka yarinyar ta dameka ban sani ba? Na d'auka tun satin da ya gabata muka rufe babinta, ashe tana nan cikin ranka har yanzu, ni ta ina kake sa ran zan fara nemanta cikin garin Abuja? Who told you ma a Abuja take zama? Dan kawai ka ganta a makarantarsu zai iya yiwuwa makarantar kawai take zuwa in anyi hutu ta koma gida, meh yasa kake wahalar dani akan mace, mata nawa a garin nan ka samo wata mana".
Fahad ke wannan zance ba tare da ya nuna damuwa a tare dashi ba, zaune yake a kujerar teburinsa wanda yake damk'e da files da komfutarsa da yake aiki ciki, hankalinsa bai wurin Elmansoor da yake zaune a kujerar mazaunin bak'i da ke fuskantar Fahad.
"Ya Rabbi" Elmansoor ya furta a k'asan mak'oshi yana mai shafa fuskarsa da hannunsa had'e da jan numfashi ya sauk'e.
Dubansa Fahad yake yana karantar damuwar da ke fuskarsa, can ya nisa ya matsar da komfutar gefe ya ajiye hannunsa dukka biyu saman teburin bayan ya had'esu wuri guda.
"Lets talk dude, naga alamar ka fara zaucewa"
Idanu Elmansoor ya zuba masa ba tare da ya amsa ba, bai tab'a samun matsala akan mace ba sai wannan da bai ma san sunanta ba, anya lafiyansa? Daga ganin hoton yarinya shikenan sai ta canja masa tunani da komai?"Ban tab'a ganinka haka ba Elmansoor, yakamata in bawa Aisha kyauta mai tsoka dan naga alamar ta sauya maka kwanya tun kafin kayi magana da ita".
Murmushi yake sakar masa yayi wannan furucin, tabbas yau zai iya shan naushi wurin abokin nasa in ya gano shirinsa, sosai yayi mamakinsa da ya sake dawo da maganar Aisha, duk miskilancinsa ya ajiye gefe yana neman hanya d'aya da zai samu Aisha.A yau da yayi tattaki zuwa ofishin Fahad yaje ne dan ya yanke shawarar tambayar k'anwarsa abu game da ita, anan ne Fahad yace girma zai zube shi ba dashi wannan aika-aikar ba.
Tun ranar da ya samo layin nan guda hud'u yake k'ok'arin karantar abokin nasa, bai son hali irin nasa, yafi kyautata zaton bai samu mace da ya sha wahala akanta ba shiyasa yake sakainar kashi dasu.
"Aisha? Wacece Aisha kuma?"
Fuskarsa bayyane da alamar tambaya, idanunsa na kan Fahad ko kiftawa baya yi yana mai jiran amsarsa.Kai tsaye ya amsa masa tambayarsa yana mai kawar da kai dan dariyar da yake kunshewa kada ya fito.
"Yarinyar taka mana da ka dameni akanta".Mik'ewa yayi tsaye ya zagayo inda yake
"Wai dama ka samu layin yarinyar nan shine kake wahalar dani haka? Aisha? Sunanta kenan?".Fahad bai iya amsawa ba ya fashe da dariya yana nuna Elmansoor, sosai yake dariyar yana buga teburinsa. Lumshe ido yayi ya koma mazauninsa yana jin kaman ya hau Fahad da duka, dan yana son yarinya shikenan sai ya zama masa abun dariya? Har zai masa wasa da sunan k'arya dan kawai yaga ya zai yi? Meh zai yi wa Fahad ya gane abunda yake ji can cikin k'albinsa?
Kamar daga sama yaji muryar Fahad na cewa
"Sunanta Aisha, tana da cousin sister Mufeeda, kamanninsu d'aya sai ka gansu, numban ne aka samu matsala, Aisha hud'u na samu cikin wayanta...""Tsaya Fahad, wai da gaske kake ko kuma kawai kana wasa da hankalina ne ka samo labari irin haka? Me yasa kake min haka ne?".
"Ahh, da gaske nake mana" wayarsa ya mik'a masa yana cigaba da cewa "ga numbers d'in guda hud'u, dukka suna whatsapp, biyu sun d'aura hotonsu akai, d'aya hoton namiji naga ta saka d'ayar kuwa bana iya ganin DPnta, nafi kyautata zaton ita ce, dan Aisha Skul naga Humairah tayi saving".
YOU ARE READING
SOYAYYA CE
Romance"Zan dawo miki pretty, Elmansoor is yours, yours alone, banson kukan nan kina karya min zuciya in kinayi, let's be strong, ba'a tab'a samun abu meh kyau sai ansha wahala. Zan tafi in baki sararin yin duk yanda kikeso dan bazan iya ganinki haka ba Ai...