NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
SOYAYYA CE!
Alkalamin MaryamerhAbdulPage 8
"Ummm ya kike Humaira?".
Cikin i'ina ta iya maganar bayan Muryar Humaira ya karad'e wayar a k'irar da tayi mata karo na uku kenan. Tayi wautar k'iranta ta sani, dan basu saba waya tsakaninsu ba, bare yau k'iranta da yazo da sabon salo, taya zata k'irata dan tambayar yayanta? Me zata d'auketa? Duk tambayar nan bai zo kanta ba sai da taji amon muryarta ya karad'e kunnuwanta."Lafiya k'alau Aisha, yau an tuna dani ne warhaka? Yaushe rabon da muyi waya? Rabona dake tun ranar hutu".
Murmushi tayi wanda bai kai ga zuciya ba, a halin da take ciki yanzu bazata iya k'wak'waran murmushi ba ma bare dariya, zuciyarta a cunkushe yake tana neman dalilin da zai sa ta fashe da kuka ko malulun da ya daskare a zuciyarta zai narke ta samu sa'ida."Yi hak'uri, kin fad'o min a rai ne kawai na k'iraki, dan in ban k'ira yanzu ba zan sake mantawa laifin ya k'aru".
Murmushi Humaira tayi a nata b'angaren ta furta "kin kyauta" tana mai nuna jin dad'in k'iranta da tayi."Ya kowa a gida? Su mama da Mubarak?" Bata iya furta sunan Elmansoor ba dan nauyin hakan, basu saba irin wannan gaisuwar ba, taya zata fara yi mata shi a yau kwatsam? Abun bai bada ma'ana ba. Muryarta ne ya dawo da ita "kowa lafiya k'alau alhamdulillahi, ya naki mutanen gidan? Ya Mufeedah? Ita ma kinga bamuyi waya ba tun da kuka tafi Damaturu, wai ku bazaku iya hutu a Abuja ba sai kunje garin naku?".
Idanunta ta juya dan bata samu gamsashiyar amsa ba gashi tana neman jan ta da wani hirar da bata ra'ayi a wannan lokaci, dan dole ta amsata dan kada ta d'ago wani abun, basuyi hira mai yawa ba suka yi sallama ta katse wayar. Fuskar wayar ta kalla dan duba lokaci, a fili ta furta "11:05".
Layin Elmansoor ta dannawa k'ira tana mai fatan samun wayar a kunne, duk da tasan zai yi wuya hakan. "The number you're trying to call is switched off, please try again later" muryar na'urar da ke bada bayani a duk lokacin da ta k'ira wayarsa kenan a satin nan ya doki kunnuwanta. Hawaye masu zafi ne suka zubo mata.
Kwanaki uku take k'iran wayarsa a kashe, tun ranar da ta gama jarrabawa ta bar garin Abuja basu sake magana ba, bai nemeta ba ita ma hakan, bazata iya fad'an dalilin rashin samunsa ba, dan sunyi magana lafiya sukayi sallama yayi mata fatan isa Damaturu lafiya.
Tun ranar da ya je wurinta a gida bai sake komawa ba, bata nemi zuwansa ba ita ma har suka fara jarrabawa suka gama, bai nemi ganinta ba har ranar da ta k'ira ta sanar dashi tafiyarsu hutu. Shin mutumin nan na da isashen lafiya? Tana shakkun hakan.
"Lafiyansa k'alau" wani sashen zuciyarta ya sanar da ita, "sonki ne kawai baya yi" tunawa da hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka,
Kukan Aisha ne ya tada Mufeeda da ta dad'e da yin bacci. Da mamaki take kallonta dan kukan da take yi mai tsuma zuciya, hannunta ta rik'e tana kallonta cike da tausayawa da kuma fargaban abunda ya sameta.
"Lafiya Aisha? meh ya sameki kike kuka haka?".Rungume Mufeeda tayi tana mai cigaba da kukanta, dan kanta tayi shiru ba wai dan hak'urin da Mufeedah ke bata ba, saida ta tsagaita kukan ta iya cewa "Elmansoor ba sona yake ba, kinga ya kashe wayarshi tun da nazo bamuyi magana ba, sati kenan fa".
Jan majina tayi ta goge hawayenta da bayan hannu ta cigaba.
"Ya cuceni da yasa na fara sonshi, har cikin raina ina jin sonshi Mufeeda bansan me yasa ba, meh yasa yazo wurina yasan baya sona? Meh yasa ya barni na fara sonshi? Wa ya aiko shi yazo ya tarwatsa min farin-cikina?".
BẠN ĐANG ĐỌC
SOYAYYA CE
Lãng mạn"Zan dawo miki pretty, Elmansoor is yours, yours alone, banson kukan nan kina karya min zuciya in kinayi, let's be strong, ba'a tab'a samun abu meh kyau sai ansha wahala. Zan tafi in baki sararin yin duk yanda kikeso dan bazan iya ganinki haka ba Ai...