AKWAI ILLAH

2.1K 55 11
                                    

Assalamu alaikum

Hello lovelies, hope everything is fine with you???

Na dawo da alk'alamina, ban muku al'k'awarin samun post kullum ba, amma sau uku a sati in na samu dama bazai gagara ba.

Ba labari ne na soyayya ba, labari ne da zai zo muku da abubuwa daban-daban. Ta'addanci, tawakkali, taurin kai, son kai da dai sauran sark'ak'iyar da alk'alamina kad'ai zai iya warware muku.

Labari ne k'irk'ararre, ban yi sa dan cin zarafin kowa ba, idan ya ci karo da rayuwar wani/wata akasi aka samu.

A sha karatu lafiya!!!

MAIDUGURI BORNO STATE 8:50

"Duk da rayuwa tana cigaba da juyani yanda taso, ban fasa jin sassauci cikin lamurana ba tunda na riski labarin salwantar Kaltum".

Murmushi take sakarwa kanta tana k'arewa surar jikinta kallo a doguwar mirror [standing mirror] d'in da ke mak'ale jikin bangon fankacecen d'akinta.

Juyi tayi mai ban sha'awa tana k'ara fad'ad'a murmushinta.

"wayyo ni Fanne dad'ina, ko ba komai zan fara sabuwar rayuwa, ga dukkan alamu Na'eem ya k'yasa cikin kwanakin nan. Meh yafi min hakan dad'i? Duniya juyi-juyi".

D'ago kanta tayi tana daidaita dubanta akan k'aton hotonta da wata matashiyar budurwa, wanda a kallo d'aya zaka bawa kowaccensu shekaru ashirin da 'yan kai.

Murmushinta bai gushe daga fuskarta ba ta shafa hoton tana mai kad'e jikin, duk da ba k'ura ko kad'an a jiki.

"Allah sarki Kaltum aminiya, ina rasa dalilin da yasa wani lokaci nake jin ina tausaya miki a cikin zuciyata, bayan kwata-kwata bai dace inyi hakan ba, farinciki da annashuwa yakamata in dauwama a ciki, rashinki a gareni alkhairi ne, meh nake k'aruwa dashi a wurinki a lokacin da muke tare? Meh kike saka min dashi a duk lokacin da alhairaina suka yawaita gareki? Sam babu komai, sai bak'in ciki da tashin hankali"

A lokaci d'aya annashuwar fuskarta ya kau, ta shimfid'a b'acin rai da tantsar tsanar da take yi mata.

"Na tsaneki, na tsani duk wanda zai baki farinciki, na tsani murmushinki, na tsani..."

Bata samu damar k'arashe zancenta ba sakamakon k'arar wayarta da ya katseta.

Nauyayyar numfashi ta sauk'e tana mai kai dubanta kan gado inda wayar ke ruri.

Hannunta da ke kan hoton ta janye sai dai cikin rashin sa'a, hoton ya gauce yana barazanar fad'owa. A hanzarce ta cafke sannan ta janyo wayar tana duba mai k'iran nata.

"Na'eem!"

Ta karanta a fili tana mai wadata fuskarta da murmushi, bata d'auki wayar ba sai da ta kalli hoton hannunta, ta kad'a gashin idanunta murmushi bai bar leb'b'anta da ke wadace da jan baki mai d'aukan hankali ba.

"Bai kamata in rasa ki kuma in rasa hotonki ba Kaltum".

Danna wayar tayi ta mak'ala a kunnenta tana mai lumshe idanunta.

SOYAYYA CEWhere stories live. Discover now