BABI NA TARA

2.1K 180 17
                                    

MAKIRCI KO ASIRI
               
              Rubutawa
                     Yar_ficika

®NWA

Wattpad @yar_ficika
Blog
Phirdauceejeebo.blogspot.com

BABI NA TARA

Wannan BABIN nakune Ramlah Yusuf Ayagi Mufeedah Abubakar Dijah Waziri da Raheena Mamoudou #1love♥ #TEAM MKA

    Kallonta Lash tayi tace
"Bari na wuce kinsan da safe ake kamun fara dan haka yanzu daga nan can na nufa.."
  Rungemata Mufeedah tayi tace
"Shiyasa nake sanki Aminiyata samunki a rayuwata babban alkairi ne...
    Jakarta ta d'auka suka fito bakin kitchen suka had'u da Ramlah tana ganinsu ta washe baki kallon Mufeedah lash tayi tace
"Kar dai kiceman wannan ce kishiyar taki?"
   Tab'e baki tayi tace
"Itace"
Dariya Lash tayi tace
"Bakida kishiya wannan ay bata da maraba da mai aiki"
Shewa sukayi suka tab'a
   Lash takai dubanta ga Ramlah tace
"Hajiya ina fatan kin shirya kishi damu danmu kishi damu sai mutum ya shirya..."
Tana fad'an haka suka wurga mata harara suka fita..
  Jiki sanyaye Ramlah taja jiki ta koma kitchen..
   Suna fita ta kalli Ramlah tace
"Amma matar nan akwai kyau"
Tab'e baki tayi tace
"Tana da kyau"
  Dariya tayi tace
"Dakyar na iya kallonta na gaya mata magana dan kwarjini taman wallahi"
   Harararta tayi tace
"Malama ki wuce dan ki dawo da wuri"
   sallama ta mata tayi gaba....
                         ********
    Tafiya takeyi ciki  k'urmin daji ba gida gaba ba gida baya sai da tayi tafiya sosai kana ta iso bakin wata bukka, ita kad'ai ce bukka a wajen.
  "Gafaranku dai"
Abinda tace kenan
   Shigo daga ciki, shiga tayi tana kirari, takai minti goma da shiga kana ya mata izinin zama, waje tasamu ta zauna..
   "Allah ya taimaki boka"
Mutum ne bak'ik'irin idanuwanshi jajaye ya daka mata tsawa yace
"Ba'a kira mana Allah anan ko kin mance dokar wannan bukar ne?"
  Jiki na kyarma tace
"Aiman afuwa boka na mance ne"
  Kai ya d'aga mata batare da yayi magana ba..
  "Mike tafe dake?"
Zama ta gyara tace
"Boka ba zuwan kaina bane ba zuwan Mufeedah ne.."
Hak'oranshi ya washe wanda sukayi jawur yace
"Amarya zakice man lafiya take ko?"
Dariya tayi tace
"Lafiya lau"
Dama boka so take... ta kwashe komai ta gaya mashi...
   Wata irin dariya ya kwashe da ita yace
"Aikinta mai sauk'i ne ita kuma Haneefa ba zamu kasheta yanzu ba sai sun d'and'ani wahalar rayuwa kana daga baya zamu kaudasu d'aya bayan d'aya.."
  Baki Lash ta lashe tace
"Godiya muke boka"
    Wani magani ya d'auko a wata kwarya yace
"Kice mata wannan ta wanke gabanta dashi idan ta wanke ruwan ta mashi girki ta tabbata daidai shi tayi girkin dan ba'a buk'atar wani yaci girkin sai shi idan tayi yanda mukace to sai yanda tayi dashi, wata kwarya ya d'auko yace wannan kuma kwaryan ta saka a k'ark'ashin gadonshi to zai tsani Matarshi da yaranshi zaiji bai san ganinsu.."
    Godiya Lash ta mashi ta karb'a ta aje mashi rapper 1k guda yana gani ya washe jajawur d'in hak'oranshi..
   Sallama ta mashi ta fita, saida tayi tafiyar awa guda kana ta iso bakin titi mai napep ta tsaida tace
  "Katsina zaka kaini"
Kallonta yayi yace
"Hajiya katsina fa maimakon ki hau mota ko kin manta daga inda kike in kin manta bari na tuna maki charanci kike kuma da alama daga k'auyen d'an turu kike"
   Dariya tayi tace
"Ka kaini in baka dubu biyar.."
Baki ya washe yace
"Shigo muje.."
Shiga tayi suka tafi....
   Sai da yahau titi sosai ya juyo ya kalleta yace
"Amma malama mi yakaiki k'auyen d'an turu? Nidai a sanina babu gidaje sai bukkar boka dumbus kuma da alamu ke macen arzik'i ce nayi mamakin dana ganki kin fito daga k'auyen"
  Tsawa ta daka mashi tace
"Idan tambayoyi zakaman ajeni in sami wata.."
"Allah ya baki hak'uri"
Abinda yace kenan yaja bakinshi yayi shiru....

Ana wata ga wata shin Mufeedah zatayi nasaran raba Ramlah da farin cikinta? Dagaske Imran zai juyama Ramlah baya da yaran da yafiso a rayuwa? Ya makomar Mufeedah daga k'arshe? Ku cigaba da yar mutan katsinawa dan jin amsoshinku...

Don't forget to vote comments nd share tnx y'all

MAKIRCI KO ASIRI Место, где живут истории. Откройте их для себя