BABI NA SHA SHIDA

2.6K 462 83
                                    

MAKIRCI KO ASIRI

Rubutawa
Yar_ficika

®NWA

Wattpad @yar_ficika
Blog
Phirdauceejeebo.blogspot.com

BABI NA SHA SHIDA

K'arfe bakwai dai dai tagama shirya yaranta suka mata sallama suka wuce school....
D'akinta ta shige tana shiga ta wuce toilet ta dad'e tana wanka kana ta fito...
Tsintar kanta tayi da sha'awar yin kwalliya ta b'ata lokaci wajen yin kwalliya tana gamawa ta wuce wardrobe, red super ta d'auko doguwar riga, ta saka rigar d'is ta zauna jikinta ta kafa d'aurin d'an kwali kai kace gwargwaro ne ta nad'a, feshe jikinta tayi da turararuka kala kala, ga sanyin AC, sai ya bada wani k'amshi mai sanyaya zuciya....
Kanta ta kalla a madubi murmushi ta saki wanda ita kanta tasan tayi kyau, (Nikaina sai da na firgita ganin kyan da tayi sai kace wata balaraba...), parlour ta nufa tana isa ta zauna kan 1seater ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya tana kallon MBC Bollywood....

K'arfe tara ya fito cikin shirin shi na tafiya office dai dai Mufeedah itama ta fito daga d'akinta murmushi ya sakar mata yace
"Good morning baby"
Inda yake bata kalla ba bare yasa ran zata amsa..
Yana d'agowa suka had'a ido da Ramlah, murmushi ta sakar mashi kauda kanshi yayi amma a ranshi yana yaba kyan da tayi
"Ina kwana"
Muryanta ta katse mashi tunanin da yakeyi
A tak'aice ya bata amsa da
"Lafiya"

Kallonta Mufeedah tayi, saida ta kusa fad'uwa ganin irin kyan da Ramlah tayi, kanta ta duba gani tayi Ramlah tafita komai ta mata tazara nesa ba kusa ba ji tayi kamar ta d'aura hannu bisa kai tasa ihu saboda takaici, harara ta bankama Ramlah tayi tsoki ta koma d'akinta...
"Your breakfast is ready"
Ya tsinkayo muryan Ramlah, bai tanka mata ba ya nufi dainning table, k'arasawa tayi dan tayi serving d'inshi, soyayyen dankali ne sai tea ta had'a mashi wanda yasha kayan yaji..
Tura mashi tayi gabanshi tace
"Ranka yadade gashi nan nasan kayi missing abinci na."
Tana fad'an haka ta kashe mashi ido tare da sakin murmushi, harara ya wurga mata tare da tsoki ya fara cin abinci, yana gamawa yayi hamdala, ya mik'e ya nufi d'akin Mufeefah...

Da sallama ya shiga d'akin, zaune take bakin gado tayi tagumi, bata amsa ba haka ba kuma ta d'ago ba..
Takowa yayi yazo gabanta hannunta ya cire, kwacewa tayi ta buga mashi tsoki..
Jawota yayi ya had'ata da k'irjinshi, kuka ta sakar mashi , gaba d'aya hankalinshi ya tashi
"Minene Baby kinsan bansan ganin kukanki.."
Hawaye ta share tace
"Kana gani jiya matarka taciman mutunci amma ka gagara rama man.."
Bayanta ya dunga bubbugawa yana bata hak'uri shi kanshi ya rasa ya akayi ya kasa hukunta Ramlah jiya da dare...
Hak'uri ya dinga bata da kyar ya samu tayi shiru, wasanni ta fara mashi daga nan komai ya canja...

Wanka ya fito yana tsane kanshi, hararta yayi yace
"Idan kikasa aka koran aiki yau sai kisan ya zakiyi damu.."
Dariya tayi tace
"Bama mai korarka.."
Shiryawa yayi ya fito dan wucewa aiki tare suka fito shida Mufeedah tana manne a k'irjinshi, parlour suka tarda Ramlah zaune tana jiran fitowarshi, wucewa sukayi inda take bai kalla ba, itako Mufeedah sai shigewa take jikinshi tana cewa
"Baby Allah kamar mu koma nifa ban gaji ba.."
Ta kalli inda Ramlah take ta kashe mata ido tana murmushin mugunta..
Hancinta yaja yace
"Idan na biye maki yau baki barina fita..."

Ramlah ji tayi kamar ta fashe da kuka, wannan wane irin bala'i ne haka aikinta ne fa amma yaje ya nemi wata, kukan dake neman kubce mata ta maidasu dan bata san Mufeedah ta gane halin da take ciki tayi dariya..
Murmushi ta k'ak'aro tace
"Harka fito?"
"Eh"
Ya bata amsa a tak'aice...

Kallon Mufeedah yayi yace
"Baby sai nadawo ko?"
Rungumeshi tayi tace
"Ka kabiyoman da shawarma"
"An gama"
Yace mata ya juya ya tafi..

Yakai bakin k'ofar fita parlour ya juyo muryanta tana cewa
"Allah ya kiyaye hanya ya baka sa'a ya had'aka da alkairin da ke cikin wannan ranar sharrin dake cikinta Allah ya nisanta ka dashi, ka tabbata halak d'inka zaka kawo mana idan baka samo ba ka dawo zamu hak'ura.."
Juyowa yayi ya kalleta, murmushi ta sakar mashi
"Nagode"
Yafad'a a hankali yana fad'a ya juya ya fice...

Juyawar da zatayi taga Mufeedah zata zuba abinci, dasauri ta k'arasa wajen ta d'auke warmer din tace
"Akanmi zaki tab'aman abinci?"
D'agowa Mufeedah tayi ta watsa mata harara tace
"Bangane ba?"
"Bazaki gane ba ai"
"Naga abinci kuma inajin yunwa mi zai hana bazan ciba.."
Dariya Ramlah tayi tace
"To naga bake na dafa mawa ba mijina na dafa mawa akanmi zakici"
Iya k'ulewa Mufeedah ta k'ule tace
"Kiban abinci inci"
"Bazan bada ba aikema macece ki shiga ki dafa da kanki"
Zagi ta maka mata tace
"Miye amfaninki gidan dama dan ki dafa mana abinci zakiban ko kuwa"
Shek'ek'e Ramla ta kalleta tace
"Bazan bada ba idan kin isa kizo ki karb'a"
Tana fad'an haka ra juya ta tafi, zagi Mufeedah ta dinga jifar Ramlah dashi, ko juyowa ba tayi ba bare ta tanka ta..
Haka ta k'araci masifarta taja k'afa ta koma d'aki dan yunwa takeji sosai...

Dan Allah kuna danna d'an star dinnan kuma ku shiga d'an akwatin nan ku aje ra'ayinku, wallah ra'ayinku shike k'ara mana k'arfin cigaba da typing idan kuma kukayi shiru sai muga kamar labarin bai maku dad'i... thnx y'all my sweetos

MAKIRCI KO ASIRI Onde histórias criam vida. Descubra agora