BABI NA SHA HUD'U

1.8K 198 29
                                    

MAKIRCI KO ASIRI

Rubutawa
Yar_ficika

®NWA

Wattpad @yar_ficika
Blog
Phirdauceejeebo.blogspot.com

BABI NA SHA HUD'U

Dariya yayi mai isarshi yace
"Wannan aikin mai sauki ne amma bari na duba nagani.."
Dariya tayi dan dama tasan duk idan tazo nan to buk'atarta ko wace iri ce zata biya...
Duk'ufa yayi yana bincike tunda ya duk'a bai d'ago ba sai k'asa da yake bugu yakai kusan minti talatin yana abu guda duk ya had'a zufa...

D'agowa yayi dasauri ya kalleta yace
"Akwai matsala"
Dubanshi tayi da alamar firgici a ranta tace
"Bangane mi kake fad'a ba.."

Zama ya gyara yace
"Gaskiya kashe Haneefa zaiyi matuk'ar wahala saboda duk abinda nayi sai inga wani haske na binta kiyi hak'uri kasheta zai iya zama barazana akanmu...."
Shiru tayi a ranta tana cewa
"Wannan wace irin yarinya ce haka?"
A sanyaye ta kalleshi tace
"To raba auren Ramlah da Imran fa?"
K'asa ya cigaba da bugawa dasauri ya kalleta yace
"Wannan wane irin aiki ne kika kawoman? To bari kiji auren Ramlah da Imran bazan iya kasheshi ba saboda tafimu bata bacci ita da d'iyarta suna kaima Allah kukansu idan har na matsa to nidake zamu rasa ranmu na gaya maki..."
Cikin tsananin firgici tace
"Katai makeni kasan dakai na dogara ko nawane zan biyaka indai buk'atata zata biya.."

Tsawar daya daka matane saida ta kusa sakin fitsari yace
"Bakiji mi nace maki ba? Idan muka matsa zamu iya rasa ranmu, basu barci kullum suna kaima Allah kukansu, shima Imran abinda yasa mukayi galaba akan shi saboda bai damu dayin azkar ba dan haka tashi kiban wuri ni inasan rayuwata...."
Kallonshi tayi da b'acin rai tace
"Kaban kunya ashe akwai abinda zai gagareka to in kai ya gagareka ni bazai gagareni ba namaka alk'awarin saina kashe Haneefa da hannuna na raba auren Imran da Ramlah..."
Tana kaiwa nan ta mik'e ta fita rai b'ace....
******
Yamma lik'is ta shigo gidan, bata tarda kowa parlour ba dan haka d'akinta ta nufa tana shiga tai wurgi da jikar hannunta ta fad'a kan gado, bata damu da tayi sallah ba, haka ta dinga juyi kan gado tana neman mafita dan gaskiya barin Haneefa a duniya ba babbar barazana bace ba a rayuwata...

Aiki suke ita da Haneefa a kitchen, dan yau zata karb'i girki suna aiki suna fira..
"Ammi mi zamu dafa ne yau?"
Murmushi tayi tace
"Favourite food din babanki"
Tab'e baki tayi tace
"Jallof rice ryt?"
Murmushi tayi tace
"Eh Mamana"

"D'auko kaza a fridge ki gyara kiyi pepper chicken"
Kazar ta d'auko ta wanke tasa a wuta, suna girki suna fira, dama kullum idan Haneefa tana gida to tare suke shiga kitchen dan tana koya mata abinci...
Guava juice suka had'a dayake fav drink din Imran d'in kenan, kafin kice mi gidan ya d'auki k'amshi, suna gamawa Haneefa ta jera komai a dainning table, shafa kanta Ramlah tayi tace
"Allah ya maki albarka"
"Amin"
Ta bata amsa...
"Bari naje nayi wanka"
Cewar Ramlah tana fad'an haka ta nufi d'akinta itama Haneefa d'akinsu ta nufa....

K'arfe takwas daidai ya shigo gida da sallama, tashi tayi da sauri taje ta tareshi da fara'a shiko ganinta ji yayi kamar an buga mashi guduma a k'irji...
"Sannu da zuwa Hayatee"
Yauwa ya fad'a kanshi gefe, jakar hannunshi zata karb'a ya dakatar da ita..
"Bawai na hanaki shiga harkata ba?"
"Kayi hak'uri"
Cewar Ramlah

"Mizaka farayi wanka ko abinci?"
Tsawa ya daka mata yace
"Waike dak'ik'iyar inace? Bakiji mi nace ba? Nace maki natsaneki bansan ganinki.."

"Kayi hak'uri naga yau aiki nane"
"Eh aikinki ne amma ki sani bazanci abincin naki ba..."

Zuciyarta wata k'una takeyi, daurewa takeyi take magana dan gab take da fashewa da kuka..
Duk'awa tayi ta rik'e k'afafuwanshi tace
"Dan Allah idan laifi na maka kayi hak'uri bazan iya d'aukar hukuncin daka yanke akai na ba yaman tsauri Imran.."
Tana fad'an haka ta fashe da kuka..
Hankad'eta yayi sai da kanta ya bugi tiles d'in parlour'n yace
"Ramlah ki fita harkana natsaneki bansan ganinki..."
Yana fad'an haka ya rab'ata ya wuce, ya nufi wajen Mufeedah wadda tun da Imran ya dawo ta fito, yana isowa wajenta ya rungumeta yace
"I miss you my babe"
Rungumeshi tayi tace
"Miss you more honey"

"Mi kika dafaman? Yunwa nakeji"
Tab'e baki tayi tace
"Ba abinda na dafa dan gaskiya bazan juri yin girki ba dan bashi nazoyi ba..."

Rungumeta yayi yace
"My babe duk yanda kikeso haka za'ayi, yanzu muje ki shirya muje muci abinci a restaurant .."

Da tsallenta ta shiga d'aki, binta yayi d'akin, can suka fito cikin shirin riga da wando, Mufeedah ta zubo gashin attach d'inta kai ko d'an kwalli, rab'a Ramlah sukayi suka wuce suna rungume da juna..
Har sun wuce Mufeedah ta dawo ta duk'a gabanta...
"Yakamata ki sassauta ma kanki ki kwashe kayanki kibar gidannan dan mai gidan yatsaneki.."
Murmushi Ramlah tayi tace
"Burinki kenan ko? To bazaki tab'a yin nasara ba in shaa Allah.."
Tana fad'an haka ta mik'e ta nufi d'akinta, k'afafuwanta Mufeedah taja tabi bayan Imran dake tsaye bakin mota yana jiranta....




Don't forget to vote comments nd share

MAKIRCI KO ASIRI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora