BABI NA SHA BIYAR

1.9K 280 34
                                    

MAKIRCI KO ASIRI

Rubutawa
Yar_ficika

®NWA

Wattpad @yar_ficika
Blog
Phirdauceejeebo.blogspot.com

BABI NA SHA BIYAR

Wannan page d'in na kune yan Team d'in Ramlah, Ramlah na godiya sosai da irin k'aunar da kuke mata, ana tare♥ #1love #team MKA

Sha d'aya da rabi (11:30pm) suka shigo gida, ratsowa sukayi cikin parlour yana rungume da ita, basu lura da wanda take zaune ba jin maganar da sukayi, yasa suka tsaya..
"Sannunku da dawowa"
Ramlah ta fad'a tare da k'arasowa gabansu
"Yauwa"
Mufeedah ta fad'a tare da tab'e baki shiko Imran inda take bai kalla ba sai guntun tsakin da ya saki...

Murmushin takaici Ramlah tayi ta k'arasa gaban Imran kallonshi tayi sama da k'asa duk ya canja ba Imran d'in da tasani da bane, mai tausanta mai san ganinta cikin farin ciki mai san ganinta kusa dashi yau shine ya tsaneta ya tsani ganinta kusa dashi, wasu hawaye taji zasu zubo mata tayi saurin mai dasu tare da jin wani k'arfi da ya taso mata dan yau ko yane sai ta karb'i yancinta...
"Lafiya kikazo gabana kikaman tsaye"
Cewar Imran yana cika ya batsewa
D'agowa tayi ta kalleshi tace
"Yanzu abinda kayi ka kyauta? Baka gudun Allah yaman sakayya ko ka manta yau aiki nane? Ka d'auketa kafita da ita mikake nufi da hakan? Abinci na maka amma ko inda yake baka kalla ba sai jifana da kayi da k'ana nan maganganu dami wannan kucakar tafini? Wallahi bata fini da komai ba ka kalleta ka kalleni wallahi nafita komai dubi kanta kagani gashin doki ne fa bisa kanta"
D'an kwalinta ta warware ta girgiza kanta gashin ta ya zubo har gadon baya juyi tayi tace
"Ka kalleni ka kalleta dami ta fini, ko baka fad'a ba nasan kasan nafita da komai..."
Tsaye yayi ya daskare ya kasa koda motsa hannunshi ne...

Ihu Mufeedah ta saki tayi kan Ramlah, d'aga hannu tayi zata mareta rik'e hannun tayi tace
"Kada ki soma gigin wannan mummunan hannun naki zai tab'a fuskata, duk abinda zai man zan d'auka saboda miji nane Aljanna nake nema wajenshi amma ke baki isa kice zaki d'ora hannunki kaina ba duk randa ko kikayi gigin aikata haka wallahi sai kinyi danasani..."
Tana gama fad'an haka ta jefar da hannun Mufeedah....

Kallonshi tayi sama da k'asa tace
"Ka guji had'uwarka da Allah duk randa hakkina dana yaranka ya tashi kamaka wallahi sai ka tsani kanka..."
Tana fad'in haka tayi gaba, ji tayi ya fizgota da k'arfi sai da ta fad'a k'irjinshi....

"Ubanwa kike gayama magana?"
D'agowa tayi ta kalleshi tace
"Ba magana na gaya makaba na tunatar da kaine dan naga kamar ka manta miye adalci shiyasa nake tunatar da kai dan kasan mi kake ciki tun kafin lokaci ya k'ure ma..."
D'aga hannu yayi zai mareta, da sauri ta kalleshi tace
"Kada kasake wannan kuskuren na cewa zaka mareni, kada kaga ka mareni ban cema komai ba amma duk randa ka sake wannan mistake d'in sai ka gane kurenka.."
Tana fad'in haka ta fizge tayi d'akin yaranta.....

Ihu Mufeedah keyi tana zagin Ramlah ita ko bata juyo ba bare tasan da ita take..
Tsaye yayi kamar an dasa shi mamaki cike da ranshi tun da yake da Ramlah bata tab'a mashi gardama ba amma yau gashi ta tsaya gabanshi ta k'are mashi cin mutunci....

Harara Mufeedah ta watsa mashi tace
"Burinka ya cika matarka taman cin mutunci amma ka kasa d'aukar mataki"
"Kiyi hak'uri baby zanyi maganinta"
Tsawa ta daka mashi tace
"Rufe man baki kafin ka d'auki mataki ni zan d'auka.."
Tana fad'an haka ta ruga d'akinta binta yayi yana kira kafin ya k'arasa ta shige d'akin tare da rufe k'ofar ba yanda ya iya dole ya juya ya nufi d'akinshi cike da k'unar rai....

Tana shiga d'akin yaranta, ganin su kwance suna bacci, hawayen da suka gangaro mata ta goge, adu'a ta masu kana ta juya ta nufi d'akinta tana kai bakin k'ofa..
"Ammi"
Dasauri ta juyo ganin Haneefa da alamun ba bacci takeyi ba..
Dawowa tayi tace
"Miya hanaki bacci?"

"Taya zanyi bacci iyayena na cikin wani hali"
"Amma Haneefa kinsan fa dare yayi 12 fa kuma gobe kuna da makaranta"
Murmushi tayi tace
"Nasani Ammi, a yanzu ne ya kamata mukaima Allah kukanmu ba mu kwanta muna bacci ba.."
D'aga kanta tayi dan tasan gaskiya d'iyarta ta fad'a

Mik'ewa Haneefa tayi ta nufi toilet tana kai bakin kewaye ta juyo ta dubi Ramlah tace
"Ammi ki tashi kije ki gana da mahaliccinmu kinsan irin wannan lokacin da kanshi yake saukowa yana cewa ina masu neman biyan buk'ata in biya masu..."
Tana fad'in haka ta shige ban d'aki, kwarin guiwa Ramlah taji ta tashi ta nufi d'akinta tana shiga itama Alwalla tayi tazo ta tada sallah...

Hmmmmm in yan team d'in Ramlah nasan kunji dad'i akan yanda tayi k'ok'arin karb'an yancinta... dan haka one word about this chappy thnx y'all♥

Don't forget to vote comments nd share it really means a lot to me Nagode #ana tare #Team MKA

MAKIRCI KO ASIRI حيث تعيش القصص. اكتشف الآن