BABI NA ASHIRIN Da D'AYA

1.8K 194 2
                                    

MAKIRCI KO ASIRI

Rubutawa
Yar_ficika

®️NWA
Wattpad yar_ficika

BABI NA ASHIRIN DA D'AYA

    Haka aka cigaba da zaman karb'an gaisuwan Haneef, duk wanda yasan Ramlah da ya ganta yanzu sai yaga canji, wasu suna zaton mutuwar Haneef ce ta mayarda ita haka...
    Bayan sadakan bakwai, Ahmad ne zaune parlourn Imran, gaba d'aya ya tara Imran da Ramlah dan yanasan magana dasu, kallon Imran yayi yace
"Ina matarka?"
"Taje unguwa"
Ya bashi amsa. Ajiyan zuciya yayi yace
"Dama maganar da zanyi bata shafeta ba, zanyi magana ne akan kai da Ramlah da irin zaman da kukeyi..."
   Kallon Imran yayi yace
"Da kai zan fara saboda kaine namiji kuma ikon gidanka yana hannunka, gaskia nayi mamakin irin sakacin da kayi akan iyalenka idan wani yace zakayi haka wallahi ni zan fara k'aryatawa amma gashi bawani yabani labari ba ni nagani yanda ka maida gidanka, duk da ba laifinka amma akwai sakaci ka kuma san ba ruwan Allah sai ya kama ka da laifin daka aikata, a gabanka matarka ta zama silar rasa d'anka amma baka d'auki mataki ba kuma nasan bazaka d'auka ba bance kuma ka d'auka ba dan nasan bazaka d'auka ba, amma duk bawani abu ya jawo maka haka ba rashin dagewa da azkar, numfasawa yayi, ya cigaba kaji tsoron Allah ka dawo hayyacinka kayi adalci tsakanin matanka iyakar shawara da zan baka kenan..."
   Ramlah ya kalla yace
"Nasan ba amaki adalci ba amma ki dubi irin sanda mijinki yake maki ke da yaranki a da dakuma juyawar da ya maku yanzu kinsan ba laifinshi baneba kiyi hak'uri ki dage da ibada in shaa Allah komai zai koma kamar ba'ayi ba, kuma kiyi hak'uri da d'aukan mataki akan rasuwan Haneef kibar ma Allah ya saka maki karki manta Haneef bazai wuce ranan ba kawai dai Mufeedah ta zama sila, kiyi hak'uri nasan kinayi to ki k'ara akan wanda kikeyi..."

   Kanta k'asa tace
"In shaa Allah zan cigaba da adua kuma nabar maganar"
"Alhamdulillah"
   Abinda Ahmad ya furta kenan, kallon Imran yayi ko zaiyi magana amma baiyi ba kuma da alamu bashi da niyar yin magana, girgiza kanshi Ahmad yayi yace
"Akwai wani malami daura da akaman maganarshi adu'a yakeyi in shaa Allah zanje wajenshi zuwa jibi komi zaizo k'arshe.."
   "Allah shi yarda"
Cewar Ramlah., sallama ta yima Ahmad ta tashi ta koma d'aki, kallon Imran yayi yace
"Ranka ya dade zan wuce gida"
    Tashi yayi dan ya rakashi, suna isa k'ofar fita parlour sukaci karo da Mufeedah ta dawo, kallonta Ahmad yayi sama da k'asa, ya wurga mata harara. Gabanta ya fad'i ta rasa dalilin da yasa da taganshi take fad'uwan gaba, rab'asu tayi ta wuce.
   Imran ne ya washe baki
"Baby sannu da dawowa"
Inda yake bata kalla ba bare yasa ran zata amsa maahi. Tab'e baki Ahmad yayi ya wuce, suna fita haraban gidan, Ahmad ya dubeshi yace
"Yanzu haka matarka ke fita Imran? Wani irin freedom kaba yarinyar nan? Kalli yanda ta fita riga da wando ne fa jikinta amma kabarta ta fita haka anya Imran kwakwalwanka bai tabu ba?".
   B'ata fuska yayi dan baisan maganar. Murmushin takaici Ahmad yayi yace
    "Na tab'a maka yar gwal ko? Shiyasa kake b'ata fuska?"
   Shiru yayi bai bashi amsa ba, shima bai k'ara cewa komai ba ya isa gaban motarshi, ya shiga ya tada mota yabar haraban gidan ba tare da ya kalli inda Imran yake ba....

    Komawa yayi cikin gida, d'akin Mufeedah ya nufa, yana zuwa ya murd'a k'ofa, cikin rashin sa'a kulle ya tarda k'ofan, buga k'ofan yakeyi amma tak'i bud'e wa haka ya hak'ura ya koma d'akinshi....

                  BAYAN KWANA BIYU
  Ahmad ne ya shigo cikin gidan da sallama ba kowa parlour, waya ya zaro ya kira Ramlah bugu biyu ta d'auka.
"Gani parlour"
   Abinda yace kenan ya kashe waya, daga kitchen ta fito rik'e da flask d'in ruwan zafi.
"Ashe kina kitchen?"
Murmushi tayi tare da gaidashi, amsawa yayi fuska sake yace
"Ina Imran d'in?"
"Yana d'akin Mufeedah"
Tabashi amsa, waya ya zaro ya kira sai da ta kusa tsinkewa kana aka d'auka.
"Ina parlour"
  Yana fad'in haka ya kashe wayarshi, Jim kad'an sai gashi ya fito, da fara'a suka gaisa, inda Ramlah take bai kalla ba inda sabo ta riga da ta saba...
  "Ramlah zanje daura kamar yanda na gaya maku dan haka shiyasa nazo In sanar daku."
Haka kawai taji gabanta ya fad'i, jikinta sanyaye tace
"Allah ya maidoka lafiya"
Ta juya ta nufi d'akinta, amsawa yayi da
"Ameen"
     Hannun Imran yaja suka fita, saida suka isa bakin mota yace
Imran zan tafi kuma kasani tafiyan nan zanyi ta ne dan kai, inajin jikina ba dad'i amma daurewa zanyi in tafi saboda nasa raina da wannan tafiyan kuma inasan ka koma Imran d'inka na da, Ina san ka saka wannan a zuciyar ka Ramlah bata da kowa saini ni kad'ai na rage mata gashi nima zan tafi ba lallai baneba in dawo inasan kaman alk'awarin duk runtsi bazaka rabu da Ramlah ba, a lokacin da na barku Ramlah bata da kowa sai kai inaso kayi hak'uri ka rik'eta matsayin mata kuma matsayin k'anwa, dan nasan ko bayan raina watarana sai gaskia tayi halinta sai ka koma Imran d'inka na da, kaman alk'awarin zaka rik'e Ramlah da yaranta..."
    Jiki sanyaye ya d'ago ya kalleshi yace
"Na maka alk'awarin bazan rabu dasu ba zan zauna dasu duk da a yanzu babu wanda nafi tsana irinsu amma zan zauna dasu, kuma zakaje lafiya kadawo lafiya.."
   Hawayen dake mak'ale kan fuskan Imran suka gangaro, rungume juna sukayi sun kai minti biyar kana suka saki juna, shiga mota Ahmad yayi ya tada, lek'owa yayi ta window yace
  "Kace ma Princess, koda ban dawo ba ta cigaba daga inda na tsaya I know zata iya, I trust her..."
D'aga mashi kai yayi alamar "to", motarshi yama wuta ya bar haraban gidan, d'aga mashi hannu Imran ya dingayi har sai da yaga ya bar gidan kana ya sauke hannunshi ya koma cikin gida, jikinshi duk babu kwari......
Haka Ahmad ya hau hanyar daura sai fatan Allah ya kaishi lafiya ya mai doshi lafiya...

                    FLASH BACK
  Imran Sadeeq haiffen d'an katsina ne, a unguwar saulawa, maihaifiyar Imran ta haifi mata biyar amma babu wanda ya tsaya, suna da shekara uku suke fara wasu k'uraje daga nan sai su mutu, tun da tasamu cikin Imran take rok'on Allah yasa ya tsaya  harta haifeshi bata daina rok'on Allah cikin Imran na da wata biyar mahaifinshin ya kwanta ya rasu sanadiyar rashin lafiya da yayi, Imran har ya girma ya wuce shekarun da yaranta ke mutuwa, San duniya ta d'aukeshi ta d'aura  akan Imran amma duk da haka bata fasa bashi tarbiya ba, kuma ta bashi ilimin boko da na Allah. K'awancen Ahmad da Imran ya samo a saline tun suna yara unguwa d'aya suke, haka makaranta d'aya sukayi tun daga primary har zuwa jami'a dake cikin garin katsina...
Ahmad d'an k'anin baban Ramlah ne Alhaji Habeebu, iyayenshi sun rasu sanadiyar gobara da sukayi cikin dare lokacin Ahmad yana gidan yayan babanshi, a lokacin baisan mutuwa ba shiyasa mutuwar bata dameshi ba. Bayan rasuwan iyayenshi gaba d'aya rik'onshi ya koma wajen yayan babanshi, ba abinda ya nema ya rasa na rayuwa shiyasa bai San minene maraici ba...
Suna aji hud'u primary school shida Imran, Aisha matar Alhaji Habeebu ta haifi d'iyarta kyakyawa, wadda taci suna Ramlah tunda Imran ya ga Ramlah yace ya samu mata, duk idan ya dawo daga makaranta yana nan mak'ale da Ramlah bacci kawai ke rabashi da ita, shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin Ramlah da Imran ko hannun wa take da taga Imran ta dinga kuka kenan sai an sauke ta ta tafi wajenshi. haka Ramlah ta taso cikin so da k'auna kowa santa yake saboda Ramlah nada shiga rai, duk abinda Imran ya samo ramlah yake kawo mawa. tana girma shak'uwa na k'ara shiga tsakanin ta da Imran....
Imran na aji biyu jami'a lokacin Ramlah na ss2 lokacin gaba d'aya komai na budurwa ya gama fito mata, gakuma samari da suke kawo Mata hari, ganin haka yasa hankalin Imran ya tashi, samun Ahmad yayi ciki damuwa shi dai zai gaya ma Ramlah yana santa, dan gani ya keyi kamar za'a kwace mashi ita. Dariya Ahmad yayi har yana kama ciki yace
"Ai sai da nace ka gaya mata kace kafisan sai ta gama makaranta to yanzu ay gashi nan kanaji kana gani zata zama rabon wani.."
Bugu ya kai mashi Ahmad ya goce yana dariya.
"Ramlah ta wace ni kad'ai babu wanda ya isa ya mallaketa sai ni dan haka kasa a ranka yau zan gaya mata abinda ke cikin zuciya"
Dafashi Imran yayi yace
"Abinda ya kamata kayi kenan dan haka ina bayan ka d'ari bisa d'ari.."
Rungume juna sukayi suna dariya cikin so da k'auna.....

*********
Kwance take d'aki wayarta tayi ringing, yi tayi kamar bazata d'auka ba sai da wayan ya kusa tsinkewa kana ta d'auka ganin wanda ke kiranta ne yasa ta fad'ad'a murmushin ta d'auka tayi cikin shagwab'a tace
"Ya Imran Ina ka shige duk yau banga ka ba?"
Wani irin murmushi ya saki wanda shi kad'ai yasan fassaranshi yace
"Yi hak'uri angel mun fita ne da Ahmad amma after magrib zamu dawo so ki shirya ina da maganan da zan gaya maki.."
Bai jira mi tace ba ya kashe wayanshi, kan gado ta fad'a tare da sakin murmushi mai tarin ma'ana kala kala ita kanta tasan idan tana tare da Imran Wani irin yanayi take tsintar kanta dashi, wanda ita kanta batasa ma'anar shiba kawai ta barshi akan shak'uwa dake tsaninsu ne. Haka ta dinga juyi bisa gado tana murmushi da haka har bacci yayi gaba da ita.....

Don't forget to vote comments nd follow thnx y'all

MAKIRCI KO ASIRI حيث تعيش القصص. اكتشف الآن