BABI NA SHA D'AYA

1.8K 172 19
                                    

MAKIRCI KO ASIRI

Rubutawa
Yar_ficika

®NWA

Wattpad @yar_ficika
Blog
Phirdauceejeebo.blogspot.com

BABI NA SHA D'AYA

K'arfe bakwai ta tashi ta nufi d'akinta, tana shiga ta wuce inda ta aje maganin d'auka tayi ta nufi toilet wanke gabanta tayi tas kana ta d'auki ruwan maganin ta nufi kitchen dashi, tana isa k'ofar kitchen taci karo da Ramlah na shirya breakfast, wani takaici taji, komawa tayi d'akinta ta adana ruwan, saida ta tabbatar Ramlah ta gama ta koma wajen yaranta dan suyi shirin makaranta, da sauri ta nufi kitchen ta d'ora taliya dan danan ta had'a taliya, tuni kitchen ya d'auki k'amshi dan ta saka kayan k'amshi sosai yanda bazai gane akwai wani abu....
Mintuna kad'an ta juye taliyan cikin warmers ta ta had'a mashi tea da yaji kayan k'amshi shima tea sai data zuba ruwan tsarkinta, komai na mutum guda tayi kana ta kwasa ta nufi d'akinshi dashi tana mai neman Allah ya bata nasara yaci abincin nan...

Tana shiga d'aki ta tar da yana bacci, a hankali ta yaye blanket d'in daya rufa, iska take hura mashi a gashin kanshi har sai daya bud'e idonshi, idonshi bisa fuskarta tana sakar mashi murmushi, shima murmushin yake mata, hannu ta mik'a mashi ba musu ya mik'o mata ta kamashi, bakin toilet ta kaishi ta kalleshi tace
"Kayi wanka kazo ga breakfast d'inka yau girkina zakaci.."
Tana magana tana kashe mashi ido..
"Angama amaryata"
Ya fad'a yana dariya...

Fitowa yayi yana tsane jikinshi da towel k'arasowa tayi ta k'arba ta tayashi gogewa, da taimakonta Imran ya shirya, yana gama shiri tace
"Ga abinci"
Kallonta yayi da mamaki yace
"Abinci kuma? Ayba nan nake cin abinci ba"
"Nasani amma yau nan zakaci"
Ta fad'a tana b'ata rai, babu yanda ya iya illa yabi umurninta...
Zama yayi ta zuba mashi taliya, ta had'a mashi tea ta mik'a mashi gabanshi, ba musu ya faracin abincin yanaci yana zuba mata santi saida ya cinye tas ya sha tea, wani irin farin ciki Mufeedah take ciki wanda bata iya misaltashi...
Yana gama cin abinci yaji kanshi yayi nauyi jikinshi duk ya mutu kallonta yayi yace
"Bari nad'an kwanta"
Kafin ta amsashi har ya fad'a kan gado..

Mik'ewa tayi tazo wajenshi ta tab'ashi amma ina yayi nisa, tsalle tayi tana rawa tace
"Yau zan fara aikina da alama maganin nan yayi aiki.."
*******
K'arfe shida ya tashi ji yake jikinshi duk ya mashi wani iri toilet ya shiga yayi wanka ya d'auro alwalla, zuwa yayi ya tada sallah sai da yayi azahar kana ya maida la'asar, shigowa tayi cikin k'ana nan kaya riga da wando (kamar sanda ta sa wando lolzz), yana ganinta yaji duk k'uncin da yake ciki ya yaye, ware mata hannu yayi da yar kisisinarta ta isa wajenshi rungumeta yayi tare da a jiyar zuciya..
"Shine baki tadani nayi sallah ba"
Cewar Imran yana d'ago Mufeedah daga k'irjinshi
Fari ta mashi da ido tace
"Kasan idan mutum na bacci ba'a ta dashi"
(Niko nace inji wane malamin ya gaya mata haka ai sallah na gaba da komai..)
"Bari naje naga Ahmad"
Shagwab'ewa tayi tace
"Nidai ba inda zaka"
Jawota yayi yace
"Ba dad'ewa zanyi ba yanzu zan dawo kinji my babe.."
D'aga mashi kai tayi...

A tare suka fito a parlour suka had'u dasu Ramlah ji yayi gabanshi ya fad'i wani irin tsanarta yaji da yaran kwatakwata bai san ganinsu, d'auke kanshi yayi daga inda suke..
"Sannu da fitowa"
Cewar Ramlah
Shiru yayi bai tanka ba kuma bai kalli inda suke ba, murmushi Mufeedah tayi tace
"Baby ana magana fa"
Naji abinda yace kenan
Mukhtar ne ya ruga wajenshi ya rungume shi yana Daddy, jefar dashi yayi kan carpet har saida kanshi ya fashe yana huci...
Dasauri Ramlah ta k'araso tace
"Imran lafiyarka kuwa?"
Harara ya wurga mata yace
"Natsaneku dagake har shegun yaranki, ki gaya masu su daina shiga harkata kuma kada ubanda ya k'ara kirana Daddy Wallahi na tsani ganinku gidannan ji nake kamar in bud'e idona inga kun mutu.."
Wani irin kuka Ramlah ta saki tare da rungume Mukhtar shima kukan yake, ganin haka yasa Haneef fashewa da kuka..

K'arasowa Haneefa tayi tace
"Daddy mikake shirinyi? Kamanta suwaye mu? Yaranka ne dakafi k'auna sai kuma Ammi da duk duniya kake cewa baka da kamart...."
Tsawar daya daka matane yasa sauran maganar tamak'ale..
"Nace na tsaneku bansan ganinku ko bakiji bane ba?"
Gabanshi Mufeedah ta k'araso tace
"Calm down my baby abun duk bai kai haka ba, kayi hak'uri inma wani laifin suka maka kayafe masu..."
Hararta yayi yaja hannunta suka fita suka bar parlour'n, rungume yaranta Ramlah tayi tana kuka suma kukan sukeyi banda Haneefa da idonta yayi ja kamar garwashi saboda tsananin b'acin rai....

Dont forget to Vote Comments nd share

MAKIRCI KO ASIRI Where stories live. Discover now