BABI NA SHA BAKWAI

1.4K 168 10
                                    

MAKIRCI KO ASIRI

Rubutawa
Yar_ficika

®️NWA
Wattpad yar_ficika

BABI NA SHA BAKWAI

Assalamu Alaikum, my beautiful people, ni nasan mai laifi ce wajenku amma nasan zaku yiman uzuri saboda wani dan tsaiko da aka samu in shaa Allah yanzu zaku dinga ganin post akai akai😍 i love you y'all♥️

'Yan team din Ramlah I hope kun shirya ganin yanda zata ida kasancewa tsakanin Ramlah da Mufeedah 'yar ruwan zafi, kowa zaiyi winning, Mufeen nasan dai ke kadai ce Team din Takwararki amma bari inbi bayanki muzama mu biyu lolzz..

Tana shiga d'aki ta fara kai kawo cikin d'akin dan yau Ramlah ta mata abinda sai ta wulakanta ta wallahi dan taga ta d'aga mata k'afa shine harta samu wuri haka yau ita take gaya ma magana ta hana abinci...
Dogon tsaki taja ta zauna gefen gado tagumi tayi tana sak'awa da warwarewa numfashi taja tare da sakin wata irin dariya tace
"Yau zaki raina kanki Ramlah saina sa an k'ask'antar dake kinsan ba bakin komai kike ba.."
Tana gama fad'in haka ta tashi taja k'afa ta nufi k'ofa dan yunwar da takeji idan ta zauna zata iya illatata gara ta mik'e ko tea ne ta hada...

Bakin kitchen suka had'u da Ramlah, ban kad'arta tayi inda take Ramlah bata kalla ba ta girgiza kai ta wuce, tsoki tayi tace
"Mutum idan ya isa ya tanka mana"
Kallonta Ramlah tayi shek'ek'e tace
"Ai idan kare na haushi shi kad'ai baka biye mashi..."
D'aga hannu tayi zata mare ta, rik'e hannun tayi tace
"Ko amafarki kada ki fara wannan gangancin dan duk randa hannunki yakai jikina na maki alkawarin asibiti zaki kwana...."
Tana fad'an haka ta jefar da hannunta tayi gaba..
Ji tayi kamar ta fashe da kuka irin cin mutuncin da Ramlah ta ke mata ya fara isanta gashi boka ya gagara yi mata komai, tsaki taja ta shiga kitchen warmers din ta fara budewa taga ko da abinci babu komai cikinsu harma an wankesu, ba yanda ta iya illa ta had'a tea kawai...
Tea tahada mai kauri taje daining ta d'auki bread ta nufi d'akinta. Tana shan tea tana kitsa makirci da zata had'ama Ramlah wajen mijinta....

MAKIRCI KO ASIRI Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ