BABI NA D'AYA

7K 376 52
                                    

MAKIRCI KO ASIRI

      ©Rubutawa
                Yar_ficika

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ban yarda wani ko wata ya juyaman labari ta wata siga ba batare da izinina ba..

Banyi wannan labarin dan cin fuskar wani ba duk wanda labarin yayi daidai da halinshi to yayi hakuri nidai nawa fad'akarwa ne....

Wannan labarin na sadaukar dashi ga Anty Maijidda Musa (Mama)

Littafin tukuici ne gareki Anty Amina Kaura

Now I know why you always asked me to be strong… because you knew that one day I would need the strength to bear your loss. I miss you Maama may Allah grant you jannatul firdausi 💔😭

21 September
Birthdays are nature's way of telling us to eat more cake. Birthdays are like boogers. The more you have the harder it is to breathe. Another year older, none the wiser. Birthdays are just finger posts on the road of getting old… I was born with a gift, the gift of awesomeness I'm not just a year older I'm also a year better and prettier. I know you're jealous. I'd like to thank my mom and dad for making this miracle possible. ITS MY BIRTHDAY🎂🎉

Boom! Yes, today is my birthday, Therefore I will be treated like a Queen👑💃

Wattpad @yar_ficika
Blog www.phirdauceejeebo.blogspot.com

Instagram: yar_ficika
Snapchat: phirdauceejeeb5
Twitter: Feedoh Deedoh
Skype: phirdaucee Jeeboh
Facebook: phirdaucee Jeeboh

®NWA

BABI NA D'AYA

    Shimfida
    Gidan Malam Bahaushe...
Idan akace gidan Malam Bahaushe gidane da kyar kasamu matar aure d'aya zaka iya samun sama da d'aya ga yara wasu zamansu lafiya da kishiyoyi wasu kuma zaka samu akasin haka...

    Zaune yake palour cikin lallausar kujera tagumi yayi gaba d'aya hankalinshi bai tare dashi, d'agowa tayi ta kalleshi girgiza kai tayi ta cigaba da shirya yaranta da zasu wuce islamiyya, tana gama shiryasu tabi kowaye ne da peck a kunci kallon babbar tayi tace
"Princess ki kula da k'annenki kinji ko?"
"To Ammi zan kula dasu"
"Kuje kar ku makara driver yana jiranku."
   Tafiya suka yi suna
"Daddy mun tafi."
Amma hankalinshi bai jikinshi.
   Mik'ewa tayi tsaye kayan dake jikinta sun bayyanar da cikar sura da zatin halittarta. Doguwa ce tana da d'an jiki sai dai ba sosai ba amma gabanta cike yake da dukiyar fulani bak'ace amma ba wulik ba idanuwanta farare ne gata da hips komai nata daidai ita.
   Matsawa tayi kusa dashi ta zauna, hannunshi ta janye daga tagumin da yayi d'agowa yayi ya kalleta tare da sakar mata murmushi kawar da kanta tayi gefe tace
"Tun yaushe nake binka ka gayaman damuwarka amma kak'i fad'aman shin ka mance matarka nake uwar yayanka ko kuma ban isa na san damuwarka ba?"
  Dasauri ya kalleta yace
"Ba haka bane ba bansan ya zaki d'auki abun bane ba"
  Tashi tayi taje gabanshi ta duk'a hannunshi ta kamo tace
"Ka fad'aman damuwarka kai tsaye ni kuma nayi alk'awarin zan baka goyon baya"

   D'agota yayi ya zaunar da ita kan cinyarshi,
"RAMLAH"
  Ya kira sunanta jikinta sanyaye ta amsa da
"Naam"
"Kiyi hak'uri akan abinda za kiji daga bakina banyi haka dan in b'ata maki ba ko kuma kin rageni da wani abu tsawon shekarun da mukayi tare wallahi baki tab'ayi man laifi ba duk abinda na umurceki shi kikeman tabbas samun irinki a wannan zamanin sai an bincika."
   Murmushi tayi tace
"Nagode kwarai da yabon ka a kaina mijina."
"Ramlah"
D'agowa tayi ta kalleshi batare da ta amsa ba sai kuma ta saukar da kanta ganin yanayin daya shiga,
"Aure nakesan na k'ara. Da sauri ta d'ago
"AURE?"
"Eh aure."
Ajiyar zuciya tayi ta saukar da kanta k'asa.
   Cikin kanta taji yana cewa
"Banyi niyar k'ara auren nan ba dan cin fuska ko kin rageni da wani abu ah ah kawai zan iya kiran wannan auren da auren k'addara dan Allah ki fahimci mi nake nufi."
  Kallonshi tayi ta sakar mashi murmushi tace
"Yanzu dan zaka k'ara aure shine ka kasa gayaman, haba Imran kaifa mijina ne kuma ay Allah ya hallata maka k'arin aure, muddin zakayi adalci a tsakaninmu wallahi ni banda matsala fatana dai ka kasance mai adalci Allah yasa ta gari zaka auro Allah kuma ya had'a arzik'inmu."
   Tun kafin ta k'are ya k'ank'ameta,
"Tabbas Ramlah ke Alheri ce (Biebee'n Feedoh) duk namijin daya sameki wallahi yayi sa'ar mata Allah ya saka da alheri ance Aljannar mace tana k'ark'ashin k'afar mijinta to nikam na d'aga maki k'afata."
   Dariya tayi tare da sauka k'asa tace
"Nagode mijina. A ina k'anwar tawa take? Kuma miye sunanta?"
"Nan garin take a nan goruba road kuma sunanta Mufeedah"
  Murmushi tayi wanda ita kanta batasan na miye ba. Tashi yayi yace
"Zan fita"
Mik'ewa tayi tsaye tace
"Sai kadawo Allah ya kiyaye hanya"
Tana kaiwa nan ta wuce dan batasan ya gane halin da take ciki.

     Tana shiga d'aki ta banko k'ofa fad'awa tayi kan gado ta fashe da kuka sai da tayi mai isarta taga ba maganin da zai mata ta mik'e ta nufi toilet  alwalla tayi ta fito tayi raka'a biyu tare da neman Allah ya bata juriya da dangana akan auren da mijinta zaiyi. Ta dad'e tana adua daga k'arshe ta shafa ta tashi ta nufi kitchen danyin girki kafin pikins d'inta su dawo.

MAKIRCI KO ASIRI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora