RIKICIN DUNIYA

1.5K 73 4
                                        

*MATAN ALI*
_(the most lovely story of nice family)_

          ®
Nagarta Writter's Association.

         ©
BILKISU BILYAMIN

      *_Ina gaida masoyana na ciki dana waje,ina mai sanar da masu whatpad cewa na sake account idan sun tashi zasu iya karanta sabon littafina mai suna ASIBITIN MALAM BARA'U wata kila kafin ku ganshi a whatapp da aiki amman idan kina da whatpad dadinki sai ki karanta kawai basai kin tsumaye whatapp ba._*

   *_Ina ma masoyana fatan alkairi da rayuwa ingantacciya_*

   *_Vote and comment @Bilkisubilya_*

       *293*

    Safa da marwa kawai Munnera takeyi saboda ta nemu hanyar da zata yi maganinta, saboda fitsararta tayi yawa bazata jure rainin hankalinta ba,har ma da Dejan gaba daya,dariya tayi da ta tunu wasu yaran bayan layinsu da suke fitenarnu,kuma yan sara suka ne,basu ganin mutuncin kuwa,saboda haka zata saka su suyi mata maganin su Deji da Aminatu,saboda taga kanta na rawa,za kumatayi gaggawar yin maganinta.

             Bata taba shiga adai daita sahu ba tunda tazo duniya sai yau,naira dubu daya ta fiddo ta mika ma mai a dai daita din,ya karkace domin ya fiddo mata canji yaga wayam ta kama gabanta,murna takama shi saboda yayi imani da Allah yau ya fito cikin sa'a,hamdala yayi ma Allah sannan ya tada ya kama gabanshi.

      Wata muguwar harara ta wurga ma maigadin gidan, sannan tace"munafuki kawai,d'an 'kauye"

       Kanshi a kasa,saboda bai manta kashidin ta na cewa kuda da wasa idan ya yarda suka kara hada ido ,sai yayi gidan wakafi,bayan tasa Daddynta ya kurashi inda aka fito,tafiya take cikin isa da jin kai,cin karu tayi da 'yan aikin su, suna fira hadda dariya,fuska ta tamke, sannan tace"sakarkarun banza da wofi,maye kuma na dariya,ku kuwa kuna nufin kun maida gidan gidan mahaukata"

        Gaba dayansu suka hada baki wajan fadin "ayi hakuri hajiya"

    Tsaki tayi sannan tace"tun da na dusu daga waje nake jin gidan na wari,saboda haka duk wani abo da kuka san yana gidan nan indai za'a iya daukarshi to a fiddo shi a wanke sannan a gyra kumai"

    "to!hajiya"

"kazamai kawai, yan kauyan"

_kadan ne dai ayi hakuri bana dan jin dadi wallahi yanzo ma haka nan na kukarta nayi maku,sai ai man aikim gafara._

*_it is me Bilkisu Bilyaminu_*

*MATAN ALI*
_(the most lovely story of nice family)_

          ®
Nagarta Writter's Association.

         ©
BILKISU BILYAMIN

   *_Vote and comment dinku shi zai bani dama da kwaringwaiwar jin nishadin cigaba da aiku maku da MATAN ALI,sai kiga da yawa sunkaranta littafi,amman su kasa danna maballen da zasu voting din mutu, Vote me @Bilkisubilya._*

       *294*

     Gaba dayansu suka sunkuyar da kai kasa,saboda sun san gamansu da ita idan har suka sake suka hada ido da ita, akwai matsala babba a garesu dan sai sun gwammaci kida da karatu.

    "sanin babu mai kwaba maku shiyasa kuka maida mana gida kamar gidan yan gada,har'ana jeyo shiwarku ku?saboda haka yau yine zanyi a gidan nan ,kuma ku tabbatar kunyi abinda na saka ku,in ba haka ba zakuyi a bakin aikinku daman ya kamata ace kunbar aiki a gidan nan zuwa yanzo"

     Sun kwana da sanin kadan daga cikin aikinta ne,zata iya abinda yafi haka ma,saboda bata hada hanya da mutunci ba yayi gabas tayi amma.

     Ciki ta shiga bayan ta kara jaddada masu abinda zasuyi,kawai dan ta kunta ta masu, bawai dan abinda ta fada gaskiya bane na gidan yana wari.

    A hakimce ta iske mahaifiyarta cikin shagwaba ta isa wajanta ta fada mata ta saka kuka,hankalin Momy tashi take tambayarta.

    "ki! lafiya kika shigo kamar an maki mutuwa?"

     Kara rushewa tayi da kuka,lallashi Momy ta fara sannan tace maike faruwa ne wai,Alin yace ya sake ki ku wane aka ce make ya mutu?"

     Kukan ta dan tsagaita sannan tace"Momy bazan iya zama wannan gidan ba,bai da mutunci, baya kaunata,kuma baya da wadda ya tsana a duk cikinmu sai ni,dukana yake kamar jakka,kwana biyu da ya wuce na tashi daga jinyar dukan da yayi man,dakyar masu gadi da yan aiki suka amsan a hannunshi"

     A hargetse Momy take sauraran maganganun da 'yarta ta take shirya mata na karya,hankalin ta ya gama tashi da duk bayanin da yarinyarta ta tayi mata"bazan yadda ba wallahi aje a kashe man ke,wallahi wannan ai aikin banza ne aikin wofi,bari Dadyn naki ya dawo, gaskiya bazaki kuma ba,idan ya kiya kuwa sai dai aye wacce za'ayi,dan ba jaka muka aura mashi ba"

     "Momy wallahi kada ki bari ace zan kuma gidan nan,dan sai dai a kawo maku gawata dan azzalumi ne"

     Hannun momy ta kama tace _"momy please save my life"_

     "kada ki damu,zan san yanda zanyi"

      Kara rukunkume momy tayi tace _"Tnx you soo much"_

    Key din motan Momy ta amsa,tace _mata zata dan shiga tayi shopping abubuwan da zatayi amfani dasu,tafiya tayi wajan ajiyar motoci,bayan ta gama jaddada ma 'yan aikin cewa kada ta dawo ta iske basu gama ba,_horn tayi ma maigadi,da gudu ya wangale mata gate ta fito,wani maifacen keke dake can karshan katangar gidansu taima horn da sauri ya iso yace"Hajiya gane, mai keke so?"

     " shiga muje"

     Mamaki ya tsaya yana yi tace"idan kagama wangale bakin kana iya shiga muje sakarai kazami kawai"

     Babu kuzari ya shiga motar,saboda duk ya raina kanshi,a ranshi kuwa yake ayyana anya akwai alkairi a wannan gayyata da tai mashi,sai ya tsinci kanshi wajan tambayarta inda zasu nufa.

      Cikin halin ko in kula tace"sai da ka zanyi in amsu kudin"

     "ina da iyali, kuma suna bukatar taimaku na,kada kisalwantar da rayuwata dan Allah"

      Dariya ta danyi a karu na farko tana Allah wadai da rashin ilimi a rayuwar wasu mutane,baki ta taba tace"ka taba makaranta kuwa?"

     "ban taba ba hajiya"

    "shiyasa kake aiki irin na jahilan farko,ya kake tunanin zan iya sai da wannan banzan kan naka inci na saida me?"

     bayanin abinda take so take mashi,sannan tace"yaje yakira mata daya daga cikinsu,zata jirashi a nan wajan data rigata tsaya"Hajiya mai ya hada ke da wadannan yaran, dan Allah ki fidda kanki daga cikin hatsarin yaran da suka addabi alumma da yawa"

    "zakayi abinda na saka ku zaka tsaya raina man hankali,ubana! tunda ni bansan dai dai ba ai gwara ka kuya man"

     "yi hauri ba nufina kinan ba"

    "to maza ka aiwatar da abinda na umurceka yanzo,kuma katabbatar kun tahu tare"

    tafiya yake yana tunanin jarumta da rashin hankalin wannan matashiyar yarinya wadda take neman jefa kanta cikin musiba da tashin hankali,dan ba tasan suwaye yaran bayan gidan sarki bane, da bata ku kusa da shiga shirginsu ba,amman zai kirawo mata su,shima yana mu'a mala da sune saboda da yawa cikinsu sun tasu cikin unguwar abokan juna ne,sun daina abota ne da yaga irin rayuwarsu shi kuma bazai iya ba,sai yakama sana'ar facin keke,a ganinshi hakan zai iya zaunar dashi lafiya,suna ta shaye shayensu ya iske su yace"shegu kundai ke shiga hankalinku ku?"

     wani daga cikinsu yace"malam ware tun bamu sauke maka hannun dama ba"

     Dariya Auwalu maifaci yayi yace"kai banza ne,sholin ke gaya maka karya"

     Adda ya zare yayu kan Auwalu gadan gadan daga can gefe wani da yake saman dakali zaune,yace"kai kure dakata mana"

    cak wanda aka kira da kure ya tsaya,ga alama wanda yayi maganar yana iko da dukkan wanda ke wajan"dawo ka zauna"

    ku mawa yayi yaci gaba da shan sholesho dinshi

*_Bilkisu Blyamin._*

MATAN ALIPříběhy, které tě pohltí. Začni objevovat