ASIRI YA FALLASA

1.6K 180 23
                                    

MATAN ALI
(the most lovely stroy of nice family)

BILKISU BILYAMIN

      299

   Umarni Alhaji yayi ma Mahmud daya shiga ya duba mashi su,saman ya haura ya kwankwasa dakin da baisan na waye ba,amman sai yayi sa'a aka ce ya shigo,da sauri ya karasa gabansu ya jawo Aminatu ya rungume yace"ba suyi maku kumai badai ko?"

    "sun mana dan banzan duka mana,Yaya Mahmud,sun aske mana kai"

    Ta fashe da wani irin kuka mai tada hankali,kara rungumeta Mahmud yayi yace"dan gashi mai sauke ne,tunda basu yi yinkurin rapen dinku ba"

   "basu yi ba,kawai sunci magani na zasuyi,suna nuna kamar wani laifi nai masu,bayan kuma wallahi ban san su ba"

   "to shikinan muje kasa Alhaji yana jiranmu"wallahi ban iya tafiya, saboda munyi tsallan kwadi yafi sau talatin cikin dakin nan"

   Zaunar da ita yayi bakin gado sannan ya kuma kusa da Deji yace"matar Yaya sannu?

   Kai ta kauda ta daga kai alamar yauwa,saboda ita kadai tasan azabar da take sha.

   Kasa ya sauka ya fada ma Alhaji halin da suke ciki
,salati Alhajn yayi sanna ya haura saman da kanshi ya shiga dakin ya iske su cikin mawuyacin hali,ya tausaya masu sosai da sosai,musamman Deji da marukan da tasha sun kunbura kyarkyawar fuskarta,har idanuwanta sun shige ba'a ganinsu sosai.

    "ina dayar abokiyar zamanku take?"

    "bamu sani ba muma,dan yanzo ta dawo babu dadiwa"

    Mahmud ya ba umarni yaje ya duba ita wani hali take ciki,kada ace itama anyi mata wani abun.

      Kofar dakin ta yaje ya buga mata sai gata ta bude kofar tana hamma tace" lafiya kake buga min kofa"

    Ya musa fuska yayi yace"lafiya kalau kizo Alhaji yana neman ki"

    Juyawa yayi ya koma,itama tabi bayan shi suka Isa har dakin, babu batun gaisuwa ko alamar ladabi atatare da ita tace"ance kana nema na?"

    Kallanta Alhaji yayi saboda baiyi mamaki ba,duba da yanayin da ta fito ma kawai ya isa ya fahimar dashi anyi asarar tarbiya yace"eh haka ne,kina ina har haka ya faru da yan'uwan ke, ke kuma kina ina? naga alamar basu miki komai ba"

    Tace" ni ban ma San abunda ya faru ba"

    Alhaji yace"yan sara suka ne suka shigo suka yiwa su Aminatu da Khadija wannan barnar"

     Baki ta taba tace"ayya!Allah ya kiyaye gaba"

    da fadar haka ta juya ta koma dakin ta,saboda babu wani dalili da zaisa tasaya tana jin abinda ita ta bada kwangilar yinsa kuma gaban idanta kumai ya faru.

     Girgiza kai Alhaji yayi"yace Allah ya rufa mana asiri, sanann yace mahmud ya taimaks ma  Aminatu,su fito da Deji a kaisu Asibiti.

    A hankali suka fito harabar gidan Alhaji ya kira mai gadin gidan yace ya bude kofa zasu asibiti, mai gadin yace" Yawwa Alhaji batun yaran nan da suka shigo gidan nan,nasan su a bayan layin nan suke dan ina ganin su,Alhaji yace Alhamdulillah shigo mota mu tafi dakai kaima daga asibiti sai mu wuce police station yadda za'a kamo min wadan nan yan banzan yaran"amsawa yayi da to maigadin sannan suka tafi.

*LONDON A KASAR PARIS*

     Tura kofar dakin Munayya  yayi yana kare mata kallo, itama zuba mashi ido tayi tana kallon shi,saboda batasanabindayakaqoshidakinta ba kuma,tura kofar dakin yayi ya rufe da karfi, sannan ya jinginadajikin bango,mugun kallo ya watsa mata sannan yace"inakika san slimy"

MATAN ALIWhere stories live. Discover now