KUMIN NISAN TAFIYA

3.2K 131 66
                                    

MATAN ALI
(the most lovely story of nice family)

BILKISU BILYAMINU

Godiya mai dinbin yawa ga dukkanin masoyan littafin MATAN ALI,naji dad'in yanda kuka nuna Kauna a garene da soyayya Allah ya biyaku da mafificin alkairinsa,wannan ne shafin karshe,sai mun hadu a littafi nagaba MIJINA HASKEN RAYUWATA

5 END

Kai ya dafe yana tunanin sufa mata duk yanda zakai masu sai sun kawo maka raini da izgilanci, musamman idan suka ga abinda kake takama dashi,to ne kham bazan yadda da raini ba, _a zuciyata naci ina sauran raini tunda kuma anga idi zundir._

Dakinshi ya kuma ya dauki keys dinshi ya nufi gidan Hajjarshi kwana daya baije ya duba ta ba,sai yake jin duk bai kyauta ba,parking space ya nufa ya fada motarshi ya danna horn mai gadi ya bude nashi ya nufi family house dinsu.

A falo ya iske su gaba dayansu Mahmud,Ameenatu,Hajja suna fira,da sallama ya idasa shiga falon, ya samu kujerar dake kusa da Hajja ya zauna yace"Hajjana barka da yamma"

"sannu dai Babana"

"yawwa,nayi missing dinki fa"

"ai naga alama tunda gaka tunda sassafi"

Kai ya shafa yace"kaina na dan cewo ne sai nasha magane,nadan kwanta"

Karaf Ameenatu tayi tace"Allah Hajja ya Ali tunda ya samu ya kura wadannan kadangarun barikin hankalinshi ya kwanta yake mana asha ruwan tsuntsaye a gidan nan"

Harara ya watsa mata,kai ta dauke tana dariya ciki ciki,Mahmud ne yace"big broda ai wallai kasan kai aure,gaba daya matanka na bugawa a duniya ne,suna da kyau,wannan yar kauyan ma naga yanzo ta wani waye kamar yar shugaban kasa,ni wallahi ranar nan ban gane ta ba,sai da na tsaya nayi mata kallan kurilla"

Tsaki Ali yayi ya kara tamke fuska yace"Ke tashi ki kawo man ruwa mai sanyi,kuda baku iya kumai ba sai surutu da fadi ba'a tambayi kuba"

Ganin babu wasa yasa ta tashi da sauri ta nufi kicin,shi kuma Mahmud ankara yayi da katubarar da yayi wajan furta kallan kurilla yasa ya dan sosa kiya yace"Hajja bari in dan fita gari"

"a dawo lafiya, amman kada ka kuskura ka dadi"

"to bazan dadi ba,Ya Ali na barka lafiya"

Banza yayi dashi bai tankashi ba,Hajja tace"yanzu daga zuwanka ka tarwatsa man yara muna fira"

Dariya yayi ya tashi daga kujirar da yake ya kuma bisa tata ya dura kanshi saman kafadarta yace"ai sai kiyi firar dani ai"

"kai din da kake miskili mutum in zai karace surutunshi baka wani responding mashi sosai"

Dariya ya karayi yace"to yi hakuri ina jinki,zanyi sosai"

Ita ma dariyar tayi ta shafa kanshi tace"ya zamanka da iyalin naka yanzo,da fatan dai a wajan ka an samu cigaba"

Kafada ya daga yace"not much dai"

"ban gani not much dai ba,kana nufin har yanzo jiya e'yau"

"no,an samu cigaba kasu 70 daga cikin 100"

Duka ta kaimashi tace"ansamu salama zakace, bawai not much ba,kuma nasan daga wajanka ne Allah"

"Babu ruwana Hajja wannan diyar take yar kauye ce da matsalar"

"bana tsammanin Khadeeja tana da matsala gaskiya, yarinya mai hakali da tunani ni kham ban yadda ba"

"ai na dadi da sanin kinfi san yaran nan dani yanzo"

"eh din,aikai nake ma kara Babana"

Kamu telah mencapai bab terakhir yang dipublikasikan.

⏰ Terakhir diperbarui: Jun 03, 2019 ⏰

Tambahkan cerita ini ke Perpustakaan untuk mendapatkan notifikasi saat ada bab baru!

MATAN ALITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang