MATAN ALI

2K 114 11
                                    

MATAN ALI
(the most lovely story of nice family)

   BILKISU BILYAMIN

     2  END

     Yana bakin iya warshi wajan ganin bai nuna ma Azeema tsana ba,babu laifi yana kulawa da ita,kila duk tana samaun hakan ne saboda cikin dake jikinta,sannan gashi yana isar ta da bukatunshi,tunda yanzo babu na waje,sosai take juriya Akan shi.

      A bangaran Deji kuwa abubuwa sun fara tafiya dai dai saboda yanzo Ali yana binta da kallo,sannan yayi saukin dizge da hantara da kai mari da kwallo da mutum.

    Yau ma kamar kullum bayan ta Shiga daki ta zauna akan Gado sai tunanin abunda ya faru takeyi tana murmushi, wayar tace taji tana kara alamun kira dubawa tayi taga Aminatu ce,daga bangaran Aminatun tayi dariya tace"kaga matar yayana da fatan kin fara bamu kashi,in kuma fasaha ta kare sai ai man bayani"

    Dariya Deji ta saka sannan tace "hmmm bari kawai Aminatu,yayanki akwai mugun hali,kinga yanda yake kallan abubuwan arziki,amman daga karshi sai ya basar yama yi wurgi da spondin abinci,bayan kuma na dago yanda yake hadiye miyau"

   Dariya Ameenatu tayi  tace"to muguwa mai makwan ki bashi,tunda daman nashi ne"

    Tsaki Deji tayi sannan tace"zai zo hannu ne ai,an jima kuma da kalar shigar da zanyi mashi"

    "a dai taimaka kada a zauta man yaya ya dawo sai yanda akai dashi"

   "kinsan kima sai ya zama mijin hajiya Khadeeh"

    "muguwa  kawai,ta Allah ba taki ba"

       Dariya sukayi gaba dayansu sanna suka cigaba da hirar su ta duniya.

    Ommar ne ya shigo gidan bai iske kuwa ba,sai ya samu waje ya zauna yana kukarin kiran number Alin sai ga Azeema tana saukuwa,idanuwa  Ommar ya tsura mata yana mamakin kyan da ta kara da kuma kamar tana da ciki,kai ya kauda bayan ta zauna kujirar da take fuskantarshi tace"ya Ommar ina yini?"

    "lafiya Lau matar Ali"

    Dariya tayi sanna tace"ya Ommar momy fa?"

    "tana nan lafiya lau"

   "inasan inji in gaidata amman banajin dadi sosai wallahi"

   "ai gwamma ki zauna zuwa sanda zaki sauka"

   Idanuwa ta rufe tace"haba mana ya Ommar"

    Shima dariya yayi yana jin wani nishadi a zuciyarshi saboda dai daitawar Abokinshi da kanwarshi gata hadda ciki ma.

   Ali ne ya fito daga dakinshi ya iso ya zauna kujirar da Azeema take zauni da yake 2seta ce,duban shi ya kai kan Azeema yace"yan mata ya dai,ku akwai damuwa?"

    Dadi ya kamasu da ita da Ommar ,kai ta kada cikin nata salon tace"babu wata damuwa"

    "good haka nake san ji ai,babyn na motsi sosai kuwa?"

    Kai ta gyada,saboda haka nan sai taji tana kunyar yayanta Ommar.

   Fahimtar haka da Ali yayi sai yace"kafa takura mana malam"

    "eh ai naga alama Ali mai mata hudu a da amman yanzo ka zama angon Azeema da Deji"

    "aikai kana da damuwa wallahi ka cika surutu"

    "ka manta aku ne,karewar surutu"

    Daga saman beni take takuwa kamar wata hawainiya,kallanta Ali keyi kamar zai lasheta amman kuma jin kai irin nashi amman sai ya kauda kai,kanta tsaye itama ta raba kusa dashi ta zauna jiknta na gogar nashi,sun sashi tsakiya,sai da ta kara jingina da shi,sannan ta narki murya tace"yaOmmar ina yini?"

MATAN ALIWhere stories live. Discover now