SOYAYYA DA SHAKUWA

1.7K 93 28
                                    

MATAN ALI
(the most lovely stroy of nice family)

BILKISU BILYAMIN

      300

     Ku inda take bai kalla ba tunda yasan a matsayin da ya a jeta,bayan sun sauka suka fito gaba dayansu,daman Mahmud yazo daukansu,gaba daya suka rankaya suka nufi gidan Ali.

     Peter yau yayi bajinta wajan shirya ma oganshi abubuwan da yasan yana bukats,bayan yasha na maguzawa wajan Munnera,akan yayi girki saboda kanin ubanshi zai dawo gida.

    Bai kulata ba saboda fitinarta tana bashi mamaki,mace kamarta tana da mugayan dabi'u Allah dai yasa ta sanadiyyar wannan abin da tayi ma su Small Hajiya Ali ya karya mata kafa daya,ya kuma gurji bakin tsiwarta da yayi murna yayi farin ciki mara iyaka.

     Horn akayi maigadin ya bude yana daga ma Ali hannu cikin farin ciki,saboda murnar dawowar mai gidanshi,duk da bai cika hudda dasu ba amman yana masu alheri maitsoka,da sauri ya isa yace"barka da zuwa maigida"

    Hannu Ali ya bashi yace"mun same ku lafiya?"

     "lafiya lau Alhamdullhi"

    "yayi kyau,Allah ya taimaka"

    Peter ne da sauran ma'aikatan gidan suke mashi sannu da zuwa, cikin farin ciki,hannu kawai ya daga masu,ya kama hanyar shiga cikin gida,yan take mashi baya suna bayanshi,Azeema da Munayya,har zai taka step din da zai sada shi da cikin falon gidan ya juyu ya kare ma Munayya kallo,sannan,saikuma ya basar,wani sashi na zuciyar shi yace kada yama barta ta shiga gidan,tunda ta riga ta gama zaman gidan,sai dai kuma yana san ya fita zargin  kada Alhaji yaga laifinshi.
     
       Dakin shi ya fada, suma suka haura sama,domin sauke gajiyar da suka debo,waya Munayya ta dauka,takwala ma Slimy kira bugu ukku a na hudu ta dauka cikin farin ciki Munsyya take ce mata"munfa iso nageria yar iska"

    "haba dai kamar daga sama babu wani sanarwa zaku dawo"

    "ai ne ban ma san zamu tahu din ba sai yau da zamu bar kasar"

    "Ali kinan namijin duniya,kuna fama da miskilanci da takama"

    "ki bari kawai ga mugun ta,ai ni nasha wahala kawata,bari idan na huta zan kara nemanki tunda kince gidanmu baya zu wuwa a wajanki"

   "ai wallahi kuwa,dan ban masan yasan kin san ni wallahi"

    "ina saura kuma,ya riga da ya san kumai,abinda zan baki labari kinan anjima idan na huta"

     Wayan ta kashe ta kwabe kayan jikinta ta fada toilet,ta sakar ma kanta ruwa masu sanyi,jin faduwar gaba take bata san dalilin hakan ba.

    Azeema kuwa tana shiga daki,ta fada saman gado ta cigaba da mugun baccin da ya zama sabanta yanzo,duk bayan minti kadan sai taji bacci na fizgarta,to yanzo ma dai yaci karfinta yinshi take babu sauki.

   Wanka ya shiga sanna,ya saka jallabiya fara kal kamar hakuri,sannan ya fito daining area,dan tsakura abinci yayi saboda daman ba gwanin chusa abinci bane,kallan cikin ido suka yi da munnera wadda shigowarta kinan cikin gidan,karar wayar dake gefinshi ya tsaida shi daga mugun kallan tsanar da yake aika mata, dashi ita ma tana maida mashi martani,duk da dai ya burgeta yadan kara kiba kuma yayi haske.

      Bata taba tsamanin ma za taji ya burgeta ba,saboda ita kanta ta tsane shi, tsana bama yar kadan ba,bata ga dalilin da zai dinga jin kai ba,da daukar kanshi wata tsiya, amman kallan yau kadai yasa ta danji zata iya zama dashi.

      Tsaki tayi ta haye sama abinta,cikin girmamawa ya daga wayar,daga daya bangaran akai magana"da fatan kun sauka lafiya?"

     "lafiya lau Alhji,na dan tsaya watsa ruwa ne shiyasa ban shigo ba"

MATAN ALINơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ