MATAN ALI

1.4K 152 5
                                    

*MATAN ALI*
_(the most lovely story of nice family)_

®
Nagarta Writter's Association.

©
BILKISU BILYAMIN

*_Ina gaida masoyana na ciki dana waje,ina mai sanar da masu whatpad cewa na sake account idan sun tashi zasu iya karanta sabon littafina mai suna ASIBITIN MALAM BARA'U wata kila kafin ku ganshi a whatapp da aiki amman idan kina da whatpad dadinki sai ki karanta kawai basai kin tsumaye whatapp ba._*

*_Ina ma masoyana fatan alkairi da rayuwa ingantacciya_*

*_Vote and comment @Bilkisubilya_*



*295*


"kai!Auwal mai ya kawo ka nan,bayan munsan kana daya daga cikin masu gulmarmu mun zama yan iska,kuda mu yan iska ne munsan mutunci tunda gashi mun barka kana shan iskar duniya,duk hakan ya faru ne ta sanadiyyar munyi wasa tare, zuwa makarnta da cin abinci cikin kwano daya,wannan shine wani shudaddan lokaci ka zama abokina kuma dan uwana,amman duk da haka ka kiyayye shiga rayuwarmu,dan shiga rayuwarmu bazai maka kyau ba,saboda haka bace mana da gani,d'an gyaran keke"

"Nasan haka abokina,ni kaina ban taba zagin ku ba idan wani ya zage ku har cikin raina nake jin zagin,saboda kun kasanci Aminai na tun muna yara,abinda ya rabamu banbancin halayya kawai, amman har gobe ina sanku,kuma kuna sona kada ku dauki zugar wasu su sanya ku aykata ba dai dai ba akan wanda yake maku addua ta neman dacewa da kyakyawar rayuwa mai inganci,abinda ke tafi dani wata matashiya ce wadda gidansu yana jikin inda nake sana'ata tana san ganin ka Shamsu(shamo)" _babban cikinsu kinan mai bada oda abi shine shamo._

"Da fatan lafiya dai ko?"

"wallahi ban sani ba,kana iya tasuwa muje sai kuyi magana"

"Allah yasa baka cikin zagwan kasar da ake yunkurin ye mana,dan bazan taba la'akari da sanayya ba,kuma ma banga dalilin da wata zata zu neman irin mu ba"

"muje dai muji kawai dan nima bata fada man ba"

Tsaki shamo yayi yace"muje unkuma maganar banza ce wallahi sai ta gwammaci ba'a haife ta ba"

Sun isa inda motar Munnera take parke,cikin isa shamo ya tsaya daga gefi yace ta fito daga motar sai ta fadi abinda ya kawo ta.

Bata da wani zabi sai na fituwar tunda ita ke nema"sannu ko"

Fuskar shamo a daure yace"kima haka"

"aiki nake san saku in babu damuwa"

"in kuma akwai damuwar fa"

Murmushi tayi tadan kwantar da murya cikin yanayin lallami tace"nasan ma bazaku watsar da tayi na ba"

Fuskar shi ya sassauta daya ga ta kwanar da kanta yace"ina sauraranki"

_Bayani tai mashi na tanasan su shiga gidansu suyi ma Aminatu bara zana,su kuma zane mata ita sosai yanda zata Shiga taitayinta a matsayinta na kanwar mijinta ta hanata shakatawa,karshi har marin ta tayi wanda wannan marin shine sanadiyar da ta zuciya ta badakwangilar a hura mata ita_

Kai ya kauda yace idan aka kama mu fa,rayuwarmu ta tafi a banza saboda yan kudi da zaki bamu,ku zaki dauki duk wani abu da ya tasu?"

"zan tabbatar da hakan bai faru ba"

"idan ya farun fa"

"zan dauki alhakin kumai"

"babu damuwa ban adress din gidan,da yanda zamu shiga babu matsala"

Kwatancan gidan taimashi sannan tace"shiga gidan dai akwai matsala gaskiya dan bazai shigon maku ba ta katanga,sai dai kuna iya daure maigadin idan kuka fito ku kwanci shi"

"Idan kuma bamu samu damar daure shin bafa?"

"inaga zan aikishi kawai kafin ya dawo sai ku aiwatar da abinda kukaje yi"

"kina nufin da yamma ko da rana zamuje?"

"kamar wajan goma haka yayi na dare"

"babu damuwa zaki iya ganinmu kuda yaushi sannan nawa zaki bamu ladar aikin da zamuyi"

"zan bada dubu hamsin in babu damuwa"

"akwai damuwa saboda tayi mana kadan mu goma zamu shiga gidan dubu goma goma tayi mana kadan,idan kuma zaki sai mana kayan da zamu chaki to"

Jikkarata ta fiddo dauku dubu dari tace"dubu dari ta wadatar da ku ai"

"zamu manejanta kawai"

"sai na ganku,Allah yasa kada ku bada matsala"

"idan kinga an samu matsala to daga gareki ne"

"babu wata matsala daga bangare na"

kudin ya buga da tafukan hannunshi guda biyu yace"sai kin ganmu"ya fada da muryarshi da ta riga ta bude saboda mugun shan da sukeyi,bayani yayi ma 'yan uwanshi,sannan ya basu umarnin su kara shiryawa yau ne rana ta farko da zasu fara shiga gidan wani,saboda basu sata,barsu da fada dai kawai,da hayarsu suyi kisa amman basu shiga gida jen mutane.

Auwalu mai face ta dauka ta maidashi wajan sana'arshi sannan ta wurga mashi naira dubu biyar tace"gashi nan mai kashin tsiya,daga faci baka iya kumai ba,zuciya ta mutu,kaga inda jarumai suke can"

Kai ya girgiza,sannan ya duka ya dauki kudin yana Allah wadai da hali irin na Munnera,bayan ta isa gida tayi fakin kuta kan yan aikin gidansu bata bi ba ta nufi sashin mahaifiyarta sannan ta fada bisa kujera tace"wash momy wallahi na ji"

Uwar ta kalleta da kulawa tace "daga ina kika fito kuma yanzo"

"Alhaji ya dawo yana ta fada wai na barki kin fita salan wani ya ganki a gaya ma Alin ya rasa samun abinda yake nema daga bangaransu"

"ya yace game da rashin kuma wata gidan"

"yace ki kuma zai san yanda zaiyi,ki bashi lokaci kalilan zai ga yanda za'ayi"

"to inaga bari kawai in tashi in kuma gidan"

tashi tayi sannan ta isa inda mahaifiyar take tai mata peck a kumatu sannan tace"momy take care of ur self"

"i will insha Allahu,kada ki shiga wannan adai daita sahun ki bari Bala ya kaiki mana"

"ok to bari in mai magana,natafi momy"

"to Allah ya kyauta ki hakuri mugazuwa lokacin"

hannu ta daga alamar bye kinan,Bala driver tasa akai ma magana,da sauri ya fito da riga a hannu yana kukarin sawa saboda yasan halin yar mulkin,yanzo zata tara mai jama'a ,cikin girmamawa ya dan rankwafa yace"Hajiya barkada zuwa"

"idan ka gama sai da girman sai katashi ka maidani gida,tsohun kawai"

Ranshi ya baci sai dai babu yanda zaiyi, saboda karkashin ikon mahaifinta zasu ci abinci bai da wani zabi sai na maida maganar da yayi niyyar maida mata.


*_Kada a manta da danna ma'ballen voting, sannan kuma ayi comment yanda zan samu kwarin gwaiwar yin typing din,ngd masoyan littafin Ali mai mata hudu._*

*_Bilkisu Bilyamin_*

MATAN ALIWhere stories live. Discover now