RIKICIN DUNIYA......

1.2K 67 6
                                    

[10/26, 6:54 PM] Apple: *MATAN ALI*
_(the most lovely story of nice family)_

®
Nagarta Writter's Association.

©
BILKISU BILYAMIN

*_Vote and comment dinku shi zai bani dama da kwaringwaiwar jin nishadin cigaba da aiku maku da MATAN ALI,sai kiga da yawa sunkaranta littafi,amman su kasa danna maballen da zasu voting din mutu, Vote me @Bilkisubilya._*

*294*

Gaba dayansu suka sunkuyar da kai kasa,saboda sun san gamansu da ita idan har suka sake suka hada ido da ita, akwai matsala babba a garesu dan sai sun gwammaci kida da karatu.

"sanin babu mai kwaba maku shiyasa kuka maida mana gida kamar gidan yan gada,har'ana jeyo shiwarku ku?saboda haka yau yine zanyi a gidan nan ,kuma ku tabbatar kunyi abinda na saka ku,in ba haka ba zakuyi a bakin aikinku daman ya kamata ace kunbar aiki a gidan nan zuwa yanzo"

Sun kwana da sanin kadan daga cikin aikinta ne,zata iya abinda yafi haka ma,saboda bata hada hanya da mutunci ba yayi gabas tayi amma.

Ciki ta shiga bayan ta kara jaddada masu abinda zasuyi,kawai dan ta kunta ta masu, bawai dan abinda ta fada gaskiya bane na gidan yana wari.

A hakimce ta iske mahaifiyarta cikin shagwaba ta isa wajanta ta fada mata ta saka kuka,hankalin Momy tashi take tambayarta.

"ki! lafiya kika shigo kamar an maki mutuwa?"

Kara rushewa tayi da kuka,lallashi Momy ta fara sannan tace maike faruwa ne wai,Alin yace ya sake ki ku wane aka ce make ya mutu?"

Kukan ta dan tsagaita sannan tace"Momy bazan iya zama wannan gidan ba,bai da mutunci, baya kaunata,kuma baya da wadda ya tsana a duk cikinmu sai ni,dukana yake kamar jakka,kwana biyu da ya wuce na tashi daga jinyar dukan da yayi man,dakyar masu gadi da yan aiki suka amsan a hannunshi"

A hargetse Momy take sauraran maganganun da 'yarta ta take shirya mata na karya,hankalin ta ya gama tashi da duk bayanin da yarinyarta ta tayi mata"bazan yadda ba wallahi aje a kashe man ke,wallahi wannan ai aikin banza ne aikin wofi,bari Dadyn naki ya dawo, gaskiya bazaki kuma ba,idan ya kiya kuwa sai dai aye wacce za'ayi,dan ba jaka muka aura mashi ba"

"Momy wallahi kada ki bari ace zan kuma gidan nan,dan sai dai a kawo maku gawata dan azzalumi ne"

Hannun momy ta kama tace _"momy please save my life"_

"kada ki damu,zan san yanda zanyi"

Kara rukunkume momy tayi tace _"Tnx you soo much"_

Key din motan Momy ta amsa,tace _mata zata dan shiga tayi shopping abubuwan da zatayi amfani dasu,tafiya tayi wajan ajiyar motoci,bayan ta gama jaddada ma 'yan aikin cewa kada ta dawo ta iske basu gama ba,_horn tayi ma maigadi,da gudu ya wangale mata gate ta fito,wani maifacen keke dake can karshan katangar gidansu taima horn da sauri ya iso yace"Hajiya gane, mai keke so?"

" shiga muje"

Mamaki ya tsaya yana yi tace"idan kagama wangale bakin kana iya shiga muje sakarai kazami kawai"

Babu kuzari ya shiga motar,saboda duk ya raina kanshi,a ranshi kuwa yake ayyana anya akwai alkairi a wannan gayyata da tai mashi,sai ya tsinci kanshi wajan tambayarta inda zasu nufa.

Cikin halin ko in kula tace"sai da ka zanyi in amsu kudin"

"ina da iyali, kuma suna bukatar taimaku na,kada kisalwantar da rayuwata dan Allah"

Dariya ta danyi a karu na farko tana Allah wadai da rashin ilimi a rayuwar wasu mutane,baki ta taba tace"ka taba makaranta kuwa?"

"ban taba ba hajiya"

MATAN ALIWhere stories live. Discover now