SOYAYYA GAMUN JINI

1.4K 84 8
                                    

MATAN ALI
(the most lovely stroy of nice family)

BILKISU BILYAMIN

297

Karu na farko da matan gidanshi suka sa mahaifinshi ya fara jin haushinsa,shiyasa babu rage babu raguwa tsakaninsu,ai kuma ya kara tunasar dashi akan mahimmancin amana da adalci,tashi yayi ya shiga bayi ya hada ruwan mai zafin gaske,wanda a tunaninshi zai iya kuna mata gaban ta ya hada,sungumarta yayi kamar ya dauki kashi,haka yake ya mutsa fuska,ya jefa ta cikin ruwan,wata kara ta saki mai wahala,saboda a tunaninta ma ta kune,da sauri ya dawo ya kara dan nata cikin kwamin wankan.

"Dalla malama kada ki daukan sakarai,bayan na hada maki ruwan zaki fita,dan kin raina man wayau"

"ai ruwan yayi zafi Man"

Bakinta ya dalle sannan yace"wai ke wace irin mayya ce,da baki jin kashedi, ina ga kun hada iri da fir'auna saboda taurin kanki,kada in kara jin kin kirani da Man,inba haka ba kuma rai zai baci"

Kuka take tana musul musul domin ta kwaci kanta daga wannan mugunta ta Ali,amman ta kasa,bata da wani zabi sai na hakura idan ma kasheta zai sai ya bada himma,kusan minti biyar yana danne da ita cikin ruwan,sannan yace"da fatan zafin ruwan yayi maki yanda ya kamata"

Zuge wajan ke mata,amman bai hana ta matse ba, ta fito dakyar tace"eh babu laifi harma yasu yayi sanyi ma,zafinshi bai kai yanda nake so ba"

Rankwashi ya aza mata bisa kai yace"mayya kawai,ai su nai ya babbake kawai,a huta da jaraba,ni bansan wace kaddara take bibiyata ba da har tsautsai yasa nayi wani abu dake,duk ma yanda akai akwai wani abu,za kuma ki bane harma ki lalace in dai akwai hannunki a tursasa ne ga kusanarki da nayi"

Tawel dinshi ta daura sannan ta nufi gado zata yaye bedshet din yace mata"malama kama hanyar dakin ki kawai kada in kara ganin gilmawarki cikin gidan nan,dan zan iya karya ki,saboda bakin cikin na hada jiki dake"

Dariya ta saka tace"ai baza ma ka ganne ba, saboda baccin gajiya zanje in kwasa,gwarzan namiji yayi aiki a kaina,ai sai na hada da magunguna ma"

Da sauri ta fita tana dariya tana shiga ta maida makulle ta rufe,tasaka jallabiya ta sha paracetamol tabi lafiyar gadonta cike da farin cikin, yanda ta murzu wajan Ali, lallai jarumin maza ta aura,idan aka auna yawan awanin da sukayi ba tare da ya gaji ba,duk da ta saka mashi magani bata tsamaci karfinshi zai kai haka ba,amman sai gashi ta raina kanta duk kuwa da irin jarabar ta.

*NIGERIA GIDA*

Yanzo dai kinga mun gama duk wasu yan kananun turanci da zaki dan iya jefawa a magana, sannan kuma idan aka fada zaki iya ganewa ko?"

"sosai ma sister Amina tuna,ai babu abinda zan iya ce maki sai godiya,da dinbin taimakon da kika yiman,Allah ya bani abinda zan sakamaki dashi"

"wait! malama baki da abin saka man inba ki kula da yayana ba,ki shagwaba man shi sosai,ki kuma zubu mana yara masu kyau irin ki"

"indan yara ne har sai kunci a barshi haka malama"

Gaba daya suka saka dariya hadda tabawa, kamar daman can tare suka tasu,shakuwa da soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Aminatu da Deji,har ya kai suna kwana daki daya,Deji ta waye ta kara zama yar gayu fatar jikinta tayi kyau da santse,sosai Aminatu ta kuya mata abubuwa,sannan ta kai ta _women center_ ta kuyi abubuwan gyaran jiki,da kuma yanayin tafiya da yanda zata tare mai gidanta,da yanda zata kulada shi, da danginsu girki da kuma,yanda zata dinga magana a gaban maigidanta,duk ta iya sai yan abubuwa kalilan wanda saurane ga duniyar Deji ta yanzo.

"ne fa yunwa nake ji Aunty Deji"

"bari in kawo mana abinci,da munci sai mu kuma sama kawai mungama da kasa dai yau"

MATAN ALIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt