RASHIN TAUSAYI

1.3K 73 4
                                    

MATAN ALI
(the most lovely stroy of nice family)

BILKISU BILYAMIN

296

*LONDON*

Kan gadon shi ya fada yana jin wani bakon yanayi a jikinshi,wayan shi tayi ringin harta tsinki baya da wani kuzarin da zai iya daga wayar,wani sabon kukan ta fara, tana bukatar a kai mata agaji,kamar bazai dauka ba kuma sai yayi tunanin kila kiran mai mahimmanci ne,ba tare da ya duba ba ya kanga saman kunne yayi shiru yaji wake magana,sansanyar muryar da baya mantawa Itace tace _"i never expect this from you baby"_

Banza yayi da ita,amman kuma bai katse mata wayar ba,tasan kuma bazai maganar ba inba yaga dama ba tace _"baby please don't break my heart_ mana"

Banzan dai ya kara yi da ita babu wata alama da ta nuna mata zaiyi maganar ma,kuka ta saka mashi,je yayi bai kyauta mata ba, tunda ta karyu da ajinta ta neme shiri sai ya hakura,kamar mai maganar rada yace"zaki kashi man dodon kunne ne kike man kuka a cikin kunne?"

"ai kaine kayi banza dani kake amsa ni"

"ok ya isa,stop crying and mai ke damuwarki?

Ji tayi kamar ta hadeyi zuciya ta mutu,saboda bacin ran da Ali ke bata,bai masan matsalarta ba kinan,bai masan ya wulakanta ta wajan paty ba kinan,lallai Ali baida imani bai kuma da tausayin zuciyarta data mace wajan kaunarshi,amman yana tambayarta maye matsalarta,kuka ta kara sakawa tace"wallahi nasan ka daina sona baby,yanxo har ka manta abinda kayi mani a wajan bathday patyn..."

"wait?'yan mata kada ki bata ma kanki lokaci,kifa kinsan dan ki nazo wannan wajan kazaman yaran, kinsan bana hudda dasu, amman da kika ganne sai kika basar to a tunaninki zan iya san wannan yarinyar, _after all_ kinga yanda muka kwashi da ita amman kinje kin cuge waje daya kina _expecting_ dina inzo in baki hakuri ko in lallashi ke akan abinda gaban idanki kumai ya faru,to ba sai na maki bayanin kune waye ba,kin riga kinsani"

"to am sorry,kazo yanzo,ku inzo ne?"

mararshi ce ta wani murda,ga kanshi da yake juya mashi,wani irin amai na tasu mashi,yanayin da yake ji a jikinshi bai taba riskar kanshi a ciki ba,harwani zazzabi zazzabi ya sakku mashi cikin lokaci kalilan,da kyar ya iya ce mata"kada kizo,nima bazan zo ba,muyi waya later"

Kawai ya kashi wayanshi gaba daya saboda zata iya taimakawa wajan kara mashi rashin lafiyar da baisan musabbabin afkuwarta ba.

Wata irin muguwar sha'awa yake ji wadda hankalin shi ya gagara misalta irinta,dakyar ya tashi ya fito falo ya shiga kicin ya samu lemon samiya matsa cikin ruwan lipton ya kwankwada ya fito ya samu saman kujera ya kwanta,babu wani cigaba da ya samu,sai ma kara hauhawa da abin yake,mata ne a gidan shi amman ba na kusanta ba,kanshi yaji yayi mashi wani irin nauyi ga amai na tahu mashi ga wata irin juwa na dibarshi,a kwancin da yake.

Daga ita sai wata rigar bacci wadda tsirara take,ta fito falon,daya daga cikin kujerun ta samu ta zauna sannan ta wara kafafuwanta yanda zai iya ganu kalar pant din da ta sanya,duk a kukarinta najan hankalinshi,amman bata san bama ta ita yake ba,ta yanda zai i da wannan bakon yanayi yake ,dan bai masan da ita a wajan ba,amai ya dinga kwarawa babu kakkautawa,a rude ta tasu,ta isa wajanshi ta kama shi tace"man sannu,mai ya same ka kake amai haka"

Dakyar ya iya fizge hannunshi daga nata,ya fara bin bango domin ya isa daki amman hakan ya gagara,dole sai da taimakon ta ya sada kanshi da dakin baccin shi.

Saman gado ya fada,sanna ya dafe kanshi da mararshi dake barazanar fashiwa,toilet ta shiga ta hada mashi ruwan wanka domin ya gasa jikinsh, tana jin tsoron kada ace sanadiyyar maganin da ta saka mashi ya sanya shi wannan ciwan,ai kuwa da ta shiga ukku idan har ya gano ta,bayan ta fito tazo dai dai saitin fuskarshi da tayi jawur saboda azabar da yake sha tace"na hada maka ruwa ka shiga kadan watsa,zaka samu kwari a jikin ka"

MATAN ALINơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ