MATAN ALI

1.8K 90 25
                                    

MATAN ALI
(the most lovely story of nice family)

   BILKISU BILYAMIN.

   3 END.

    Sun dadi a haka yana rungume da ita tana maida ajiyar zuciya shikuma daman haka yakeso,kasanciwarta tare dashi a yanzo yafi mashi kumai dadi,lallai shi dan gatane a wajan Allah tunda abinda yake tunani yazai sada kanshi da ita,sai gashi tazo inda yake da kanta.

     "Kina iya tafiya dakin ki tunda kin gama abinda ya kawo ki"

   "Dan Allah to kayi hakuri ka kaini dakin saboda inajin tsoro wallahi"

   "Ai ba Nina kawo ki ba ko,bukatar kanki ce ta kawoki, kuma kikayi gamu da abinda kika zo nema"

    Duk bata fuskanci inda ya dusa ba ta dai kara rukun-kumeshi tace"Dan Allah ya Ali ka kaini dakina bazan iya wuce wannan katan falon ba ,zai iya kara biyune,ya illatani, yanzo ma bacin kazo da bansan iyakar abinda zai kara aika tawa a garine ba"

    Dariya yake san yayi amman kuma baisan ta raina shi.

     "dalla malama sakar man jiki mana"

    Dan sakinshi tayi amman ta rike hannunshi gam tace" wallahi na daina maka rashin kunya"

    "Ai ni daman Baki isa kiman rashin kunya ba yarinya,duk abinda kike kyaleki nake saboda bana san shiga shirgin yara irinki,saboda haka wuce dakin ki tun ban sa wanda ki neman tabaki ba ya kara kugwaigwai ta man ki"
    Kuka ta saka mashi,jin kukan yaki har cikin ranshi daga bisani yace"matsalar a aura maka kwaila kinan,tazo ta hanaka zaman lafiya"
    _Magan-ganunshi sun bata mata rai,amman bata da zabi sai abinda ya zabar mata a wannan lokacin, amman tana da kudurin sai ya maimaita fa kuda da yaran kuda, sannan zata fahimci abunda yake nufi,zai san kwaila_

    "muje in kaiki dakin kada ki daman a dakina,wai ma mai ya kawo ki ne"

    Banza tai dashi,saboda tana da haushin kwailar da yace mata"kurmace kinan?"

    "daman inasan inji gida gobe"

    "kauyan"

  "a'a Wajan Hajjata da Mena"

   "ina ta zama Hajjarki,ki ai gidanku na kauye,anzo birni anyi clean"

    Shiru tayi bata tanka shi ba step din suka fara hawa,yanayin makurewar da tai mashi suna tafiya yana ya'ba mata magana sai ka dauka wasu sabbin masoyane,Azeema ta fito neman abinda zata saka ma cikinta saboda ya addabeta da motsun kiran abinci, ta gansu a haka,wani malolon bakin ciki ya tukareta, _wai mai hakan ke nufi?ya saki jikinshi da ita ne har yana rakota dakinta, kuma suna makale da juna ga kuma yanayin kayan daki jikinta babu mutunci a garisu kumai ya bayyana_ rabasu tayi zata wuce yasa hannunshi na hagu wanda Deji bata kama ba ya tallafo kugun Azeema yace""mai ya fito daki waje yanzo?"

    Kai ta kauda ita a dole an mata laifi tace"abinci zanci"

    Cikin ya shafu yace"babyna kana ba momynka wahala ko,ta zama achichi"

   Sakin hannunshi Deji tayi zata wuce abunta saboda bazata dauki rainin hankalin ba,yasa hannu daya ya tallafo kugunta ita ma,sannan ya mannaa da gefin jikinshi.

    Yanayin Azeema da ya kuma kamar zata mutu dan bakin ciki da Deji ta gane sai ta kwantar da kanta saman kafadarshi sannan dukka hannuwanta biyu ta maidasu ta zagaye kugunshi.

     Iyakar kululuwar kishi Azeema ta kai,hannun Ali ta ture tayi gaba da katan cikinta wanda duk lokacin da ta haihu d'ane,kallan Deji Ali yayi yace"mai hakan ke nufi kikayi yanzo"

    "mai fa,ai kwaila bata iya kumai ba"

    Dariya ya saka,sosai ta saki baki tana kallanshi wannan shine karu na farko da ta taba ganun dariyarshi mai kyau da ibganci,a iyakar zaman da sukayi bata tunanin tamasan yanda yanayin hakuranshi suke,baki yasa ya hura mata idanuwa yace"yan mata yadai"

MATAN ALIWhere stories live. Discover now