part 15

1.8K 94 3
                                    

*💝MUK'ADDARI💝15*
*SADAUKARWA GA FIDDAUSI SODANGI*
*BY 👄habiebah lurv👄*
Don't forget to follow and vote me on wattpad @habiebahlurv
Email me @habiebahlurv@gmail.com
Snapchat: habiebahlurv06
*Love u all♥*
                   🍁💧🍁
*_______________________*
      fita dashi kasar wajene shine kadai mafita , kuma a nanne kadai za'a samu  kwararrun likitocin dazasu mashi aiki."  Dogon numfashi ammi tasauke tana jinjina maganar doc. Kabir. "To yanzu kana kallon kamar  a nawa za'ai mashi aikin?." "Eh to , akwai wani abokina likita na babban  asibitin niamey ,, to munyi maganar dashi yake cemin a kalla zaikai milian ashirin. Nanata kudin kawai ammi take cikin ranta tana kada kai.." To doc ngde, duk abinda yasamude zakaji.." "To sknn Allah yataimaka, kuma nima insha Allah zantaimaka dawani abu. Haka sukayi sallama  doc yajuya yatafi gidansa. **bayan wata biyu.. Yau takama litinin, yaune kuma ranar da za'a fitar da jawad kasar waje don yimasa aikin idonsa, bayan kudin motarsa da aka sayar..dakuma wasu kudade da'aka samu gurin ammi da gidansu dakuma rakumansu.  Sosea hawaye yataru a idon rufaida zuciyarta tayi rauni ganin doc yakamo jawad zaisashi mota, jitake kamar inyatafi bazasu kara haduba..gashidai tun zuwanshi maganar datashiga tsakanimsu  baifi a girgaba..amma wani bangare na musamman take jinsa cikin ranta!..wanda batasan i'naneba!.  Jin anmawa motar key yasa tai saurin shigewa gida jinwasa hawaye dake neman sauka mata, kwanciya tayi a daki ta lumshe idonta  kamar maiyin bacci. Ammi kam saida motan tabacewa ganin kafin tashigo  gida zuciyarta cike da kewar jawad.   * * *bayan sati biyu * * * kamar daga nesa rufaida ke hango baffa mudi da kande kaya tusi2 a kansa suna tafe kande sai bala'i take, dasauri rufaida tashige bayan wani bishiya ta lafe kirjinta na tsananin bugu. Dai2 sunzo wucewa taji kande na cewa " wllh duk kai kaja mana, bakaje kama 'yar abokinka fyade ba wllh da yanzu munacan garinmu asirinmu a rufe ..amma yanzu kaja ankoremo muna yawon gararin neman gurin zama..." "Haba kande meyasa kike haka..keko'ina saikinyi tallen halinki na jaraba da bala'i. Tunda Yanzu kam munriga munbaro garin aisakiyi shiru da bakin ki  basai kinfada a nan wani yajiba bare har ahanamu gurin zama ba.. Kiyi Allah ki'iya bakinki karna karajin wannan maganar bakinki." "To ai shknn." Kande tafada cikeda shiwa.   Saida taga lallai sunwuce bata hangosu sannan tafito da guda tatafi gida tana haki  kamar zata shide...dasauri ammi tafito daga daki tarike rufaida tana tambayarta abinda yafaru. "Ammi..baffa...kande..."  Arude ammi ke kallonta jin abinda tafada tana kara  tambayarta ko kunnanta ne baiji dai2 ba. "Ammi sune wllh.. suna kalla.." Jan rufaida daki ammi tayi ta zaunarta har saida tadawo saiti sannan tafadawa ammi exactly abinda tagani dakuma abinda taji suna fada.  "Innalillahiwainnailaihirrajiun... Wannan wani irin jaraba ne, munbarmasu can sun biyomu nan...yanzu zaman nan ma zai gagaremu kenan , don idan har sukasan a garinnan muke saisun tona mana asirin dayake a lullube kuma sun yayada labarinmu..to yanzu yazamuyi rufaida.. Meye mafita.." Ammi takarasa maganar hawaye na gangarowa saga idonta. Itama rufaida kawai kuka tafara yi dontasan akwai matsala. Ranar ammi kwana tayi batayi bacci ba sai tunane2n yanda zasuyi take, tana ganin zaman niger kwata2 bazaiyi a gurinsu gwara sukoma Nigeria tana ganin takan zaifi musu kwanciyar hankali. Washe gari asubar fari ammi tahada masu kayansu , gari baigama wayewaba suka kama hanya suka bar garin da'yan sauran kudadensu.

Kuyi hakuri da wannan don Allah.. Wllh I'm very busy bansamun lokacin typing dayawa amma dazarar kamai yay dai2 zakurinka samun more typing..

*👄habiebah lurv👄*

💝MUK'ADDARI💝Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt