part 13

1.9K 99 6
                                    

*💝MUK'ADDARI💝13*
*SADAUKARWA GA FIDDAUSI SODANGI*
*BY 👄habiebah lurv👄*
Don't forget to follow and vote me on wattpad @habiebahlurv
Email me @habiebahlurv@gmail.com
*love u all♥*
                   🍁💧🍁
*____________________*
Cikin sa'a ammi ke tafiya batare da tahaduwa da kowaba, hakan yasa take tafiyan hankali kwance tanadan adduo'inta cikin zuciyarta. Saikusan 4 ammi ta'iso kyauyen dake kusa da nasu, karamin kyauyene sosea don mutanen ciki basufi a irgaba,,still rufaida na bacci batasan duk wannan hali da'ake ciki ba. Wani tsofo sosea ammi tagani yafito da sandarsa yana dogarawa  da'alama masallaci zai tafi,karasawa gurinshi ammi tayi , ta tsuguna  tanaimi alfarman ya taimaka mata da masauki  zuwa wayewar gari, batare daya kawo tunanin komai ba yay mata i'so har cikin gidanshi yakira matarsa yay mata bayani sannan cikin nuna kulawa matar tamawa ammi i'so cikin daki. Koda rufaida tatashi taga yanda suke ammi tatambaya tafada mata duk yanda akayi ,,bata damuba kokadan don dama i'ta zaman garin ya 'isheta..gara suje yanda ba'a sansuba suyi rayuwansu hankali kwance batare dawani cin mutunci ba. Bayan sun karya sunyi wanka sukama tsoho da matarsa godiya sosea  suka musu sallama sannan suka kama hanyar tasha. "To yanzu ammi wani gari zamu..." Rufaida ta tambayeta hanunta cikin na ammi suna tafiya. ."hmm..rufaida sai yanda Allah yayi nikaina bansa i'na zamuba. Shiru sukayi nadan wani lokaci sannan rufaida tace "ammi maizai hana mutafi KORMA  tunda shi yafita daga bangaren GOUBEY,,, kuma kinga garin bamutane sosea gashi ana zaman lpy." Shiru ammi tayi tana nazari cikin ranta, sannan daga bisani tace "to shknn...yanzu muje muhau motar garin. Lckly kuwa sauran mutum daya motan yacika,, haka suka shiga rufaida nazaune cinyar amminta mota tatashi suka tafi. Tafiyan yini guda sukayi kafin suka i'sa, sukadai aka i'jiye a bakin garin don sauran duk sai anyi gaba makotan garin zasu zauka. Da adduansu suka taka suka shiga cikin garin, garine maicike da ni'ima don haryafi wancan garin nasu. Duk yawwanci gidajen karane saiwani plathouse mai kyau ginin zamani kamar ba'a cikin kyauyeba.  Wani mutumi suka  hangi wannan kofar gida yana zaune kan kujera yayi crossing legs idonsa da farin glass irinna likitoci gakuma wani babban takarda yana karantawa .  " kinga ammi muje gurinshi ba...saiya taimaka mana..ko?." Zuwa gurinsa sukayi suka gaisa ammi tafara mishi gawabi...amma bata fad'a mishi actually abinda yasa suka baro garinsu...sosea ya tausaya musu dakansa yay musu iso harcikin gida aka basu masauki. Kwana biyu da zuwansu wannan mutumi DOCTOR KABIR yasa aka gina musu daki biyu gefen gidanshi aka kewaye masu da karare . duk wani abun amfani bawanda doc baisa musuba har katifa yasai masu, godiya ammi arinka yimasa harda kukanta na farin ciki.. bata taba tunanin haka za'a karbesu hanu bibbiyu ba. Rayuwansu suke cikin kwanciyar hankali basuda wani matsala yanzu ..sai tunani da ammi takeyi na fyaden da akama rufaida wanda duksanda tazo kwanciya saitayi shi...rufaida kam mancewa take da lamarin sai sa'i2 take tunowa...kuma har gobe batasan meye fyaden ba.
***a bangaren jawad kam  inbaka sanshi soseaba ba ganeshi zakayiba, don damuwa tasashi agaba yarame sosea yafuce daga gayyacinsa  . fitowarsa daga wanka kenan yaga pix dinsa kaca2 a TV ana cigiyarsa don yanzu kwanan shi biyar rabonsa da gida yana nan hotel baizuwa ko'ina ..gaduk wanda yaganshi ko yaji labarinsa za'abashi 50million .  a natse yagama shirinsa yadauki jakarsa da makullin motarsa yafice , wuta yayma motar yadauki hanyar barin gari don yakudiri niyyar gara yaje can niger yafuskanci wannan matsalar tunda baisan ta i'nda zaifara neman mahaifiyar sa ba.
Matukar wahala jawad yashata a driven daga kd niger,  kwanansa biyu kafin ya i'sa Niger don yana tsayawa idan gajiya takamasa yahuta.  Shiru yayi yana zaune cikin mota don koza'a yankashi baisan hanyar dazaibi yaje Niamey ba, yananan zaune cikin mota ya hangi wani buzu da ragumanshi dayawa yana tafiya. Gaisawa sukayi cikin hausar mutumin dabata fita sosea jawad ke tambayanshi hanyar dazaibi yaje Niamey.. Saida suka bata lokaci sosea yana mishi kwatance don akwai garuruwa sosea daga nan kafin aje Niamey. Godiya jawad yayi yashiga mota yadauki hanya.  Tafiya kawai yakeyi yana wuce garuruwa da kauyika yana lissafasu, don buzun yafada mishi adadin garuruwan dazai wuce kafin yaje Niamey. Karfe shida na yamma dai2 wannan lokaci yarage mishi saura gari daya tsakaninshi da wanda yake ciki yaje Niamey, dai2 jejin  kyauyen KORMA barayi suka fito da gudu sukayo kan motarsa, Dasauri yaci burki yadauki jakanshi  yafice daga motar. Binshi sukayi da guda shima yakara karfin gudunshi suka fantsama cikin jije. Bakaramin rudewa jawad yayi don harya manta aikin force yakeyi, bindigarsa ma dake cikin mata yamanta da i'ta saboda tunda yake barayi basu taba biyoshiba.  Tuntube yaci dawani katon icen bishiya take yakifa agurin jakar taican wani guri sukuma suka damkoshi suna tambayarshi jaka... Jawad bai i'ya tabuka komai ba don bakaramin biguwa yayi ba daya fadi. "Ina jaka.. Suka daka mishi tsawa..." Babu..." Yafada ..wani katon icce dayansu yadauka yabuga masa a kafarsa....take ya durkushe a gurin cikin tsananin azaba...bayanda basuyi dashiba amma yace babu don shima kansa baisan inda takeba...ganin basamu zasuyiba yasa suka watsa masa abu a idonsa suka  barshi gurin bayan sungama tattakashi. K'aran daya sakine lokacin da yaji azabar rad'ad'i a idonsa ne yasa tarazana daga inda take tafiya, take tsoro yashigeta jikinta har kyarma yakeyi.. "Wayyo Allah na ..dama ban fitoba.. dama ammi tace harna fita magrib tayi..." Rufaida tafada tana shirin yin kuka..a haka taci gaba da tafiyan tana tsoro hartazo dai2 saitin dayake kwance shame2 kamar gawa. Kamar ance hakalli gurin tahango mutum kwance jikinshi duk jini.. Wani mummunan bugawa kirjinta yayi sananin tsoro ya darsu cikin zuciyarta dasaura tafara ja baya tana mitstsike idanumta don tabbatar da abinda idanunta suke gani gaskiya ne kokuma gizone....
takai kusan  minti biyar tsaye gurin tana kallonsa sannan dai ta yarda hakanne, a hankali take takawa gurin don taimaka mishi saboda bai kamata kaga mutum cikin irin wannan yanayin kakyaleshi ba. Tsugunawa tayi gabansa tana karewa fuskarsa kallo , a hankali tafurta "bawan.. Allah.. "Muryanta na rawa. Motsi jawad yafayi jin mutum kusanshi, kokarin mikewa yafarayi dakyar ya'iya tashi yazauna,,kokarin bude idonsa yafara yi saidai me?...bayanda baiyi ba amma kyam idonsa kokadan yaki buduwa... " innalillahiwainnailaihirrajiun.. " kawai yake furtawa a fili.. Wani abune yadaki kirjin rufaida jin muryarsa wanda batasan meye shima. " What's happen to my eyes..SubhanAllah..." Gaba daya tausayinsa yakama rufaida ganin yanda ya kidime, cikin sanyi muryanta tace " meye yasameka,,,meye yasamu idon..?"  Abubuwan daya faru jawad ya fada mata sannan yakara dacewa "dan Allah kitaimaka min..plss..yanzu gacan motana a baya akwai kuma jakana nan kidubamin dan Allah." Jiki a sanyaye rufaida tashiga duba jakar, batasha wani wahala ba tasameshi bayan wani bishiya, taimaka mishi tayi dawani sanda ya mike tarike sandar suka tafi tana mishi jagora... Da sallamarta suka shiga gidan ammi dake zaune tsakar gida tana jiran dawowar rufaida tatashi da saura tana tambayar  "lpy rufaida, waye wannan kuma...."

_Karku manta fa rufaida batasan fuskan jawad, don  lokacin da'abin yafaru haryayi  yagama bata kalli fuskansa ba...jawad shiyasan  fuskan rufaida yau kuma ga jawad ba idon gani._

*💝habiebah lurv💝*

💝MUK'ADDARI💝Donde viven las historias. Descúbrelo ahora