part 11

1.9K 121 2
                                    

*💝MUK'ADDARI💝11*
*SADAUKARWA GA FIDDAUSI SODANGI*
*BY 👄habiebah lurv👄*
Don't forget to follow and vote me on wattpad @habiebahlurv
Email me @habiebahlurv@gmail.com
Love u all♥
                🍁💧🍁
*____________________*
Da sauri ammi ta kwantarta tafara kokarin cire mata hijab ganin yanda gumi yake sauko mata, sakar mata hijab tayi tafara ja baya tana girgiza kai ganin jikinta babu riga "ina riganki rufaida?,, yana ina?...waya cire maki?...meye faru dake?" Cikin ficewar hankali da kidima ammi ke maganar .."Allah yasa bawani mummunan abune yafaru da keba rufaida... Kiyi magana don Allah.. " ganin ammi na kuka yasa rufaida ma fashewa da kuka tana tunanin duk yanda akayi wani mummunan abune yafaru da i'ta. Dakyau ta'iya kamo hanun ammi ta daura gabanta tace "ammi nanne,,zafi yakemin..." Tafada cikin matsanancin kuka. "Meye a nan din.." Matar baffa mudi tafada cikin sonjin abinda yafaru, tana adduan Allah yasa abun kunyarne.  Rufaida bata kulataba saida ammi takara refitting question din sannan tace .."shiya samin ...wani abu." "Shiwa." Matar baffa tafada cikin zakuwa "wani.." "Lahailahaillalla muhammadan dan amina da abdallah..." Kande tafara salati tana tafa hanu zuciyarta fal murna yauga rufaida tayi abun kunya. "To burinki yacika taje tayi abun kunya,, Kinturata yawon iskanci kuma taje anyagata bako sisi tadawo maki wani katon banza ya farkata gaki gata ea yanzu saikusan yanda zakuyi.kuma kisani sai zaman garinnan ya gagareku dake da shegiyar 'yar taki."  Tunda baffa yafara magana harya gama ammi batasan abinda yake cewaba, don tana fahimtar Repin din rufaida akai hankalinta yabar jikinta bata gane komai sai juyawa dataga ko'ina yanayi.  Naja kam natsakar gida tana kuka shabe2 harda majina don duk abinda ke faruwa tana ji kuma tana nadamar zuwa wannan gari. "Ninaja maki rufaida.. Nice sanadi ...nice sila..kiyafemin rufaida ammi kiyafemin ..nayi danasanin tafiyar nan..." Kara fashewa tayi da kuka tana hango kalu bale a rayawar rufaida na gaba wanda kuma i'tace sila. Har yanzu RUFAIDA batasan manufar wannan abunba, amma gadukkan alamu ba'abu bane mai kyauba,, hakan yasa hakara sauti kukanta tana tausayawa kanta. Kukanta ne yadawo da ammi, kamar wanda aka tsikara tatashi ta goyi rufaida tadau jakar kudinta tafice. "Kinga bi bayanta kiga ina zasu.." Baffa mudi yafadawa matarsa kande cikin rad'a, dasauri i'tama tafice tabi bayansu.
Medium hospital dinsu dake garin ammi takaita , ba b'ata lokaci aka karbeta likita yashiga dubata, almost 2hours doc nakan rufaida yana mata aiki don ciwo kan jawad yaji mata shi. Ammi gaba daya hankalin ta baya tare da ita takasa zaune takasa tsaye sai zirga2 takeyi, sai kusan 5 doc yafito ya umarci ammi data bishi office dinsa. Cikin natsuwa doc yay mata bayanin lalurarta  dakuma yanda zasubi da ita har dinkin ya warke..tunda yafara magana ammi ke sharar kwalla "wai yau rufaidanta akama fyade, yarinya karama...innalillahiwainnailaihirrajiun... Wannan wani irin rashin imani ne.." A sannu doc yake kwantar mata da hankali har hawayenta suka tsaya amma zuciyanta kamar anamata barin wuta don zafi da zogi datake mata.  satinsu biyu asibiti aka basu sallama don saida rufaida tawarke gaba daya tafiyanta yako normal. Labarin fyaden rufaida yakarade gari, mutane daddaya ne basu saniba don baffa mudi da kande duk wanda suka samu saisun fada masa har asibiti mutane kezuwa dubasu don gulma dakuma gaskata zancen. Lokacin da labarin ya iske yarima Faisal yayi kuka iyaka kuka kamar ransa zaifita, bacci kaurace masa yake ko wani dare tunani kawai yake inama zaiga wanda yama rufaidansa wannan danyen aikin..dasaiya wulakantasa !, ya tozartasa,! Yaci masa mutunci. Tunda suka dawo gida rufaida bata kara taka koda kofar gida ba don surutun da sukejima kadai ya'i'sa basai tafita an nunata da yatsa an tsankwameta ba. Akai2 baffa da matarsa suke zuwa cuke ciwa ammi mutunci suna tara mata jama'a , wannan shine babban abinda ke damunta don harta fara tunanin barin garin.
***a bangaren jawad kuwa rashin kwanciyar hankali ne tai mashi sallama, don kullum yana cikin mafarkin rufaida haka take zuwa mashi tana kuka kamar ranta zaifita. Cikin sati buyunnan kullum jawad saiya je gurin daya barta kwance ko Allah zaisa ya ganta amma shiru duk sanda yaje saiyasha kukansa kafin yadawo.. Yana ganin yabatama yarinya karama rayuwan ta, ya cuceta..ya zalunceta i'nama zaiganta yanemi yafiyarta. Cikin karamin lokaci yarame kullum yana cikin tunani.
Gaba daya chollegues dinsa sungagara gane Kansa, bayanda basuyiba akan yafada masu damuwarshi  amma yaki ca yake masu ba abinda ke damunsa. Sun kammaka duk wani aiki dazasuyi Satinsu uku suka fara shirin dawowa ,,,ranar Friday kuwa flight dinsu yadaga daga niger zuwa Nigeria. Bakaramin murna momy da ikram sukayi yiba na dawowan jawad, barin ma ikram datayi balain missing dinshi . delicious momy tahada masa da favorite food dinshi  saida tacika masa dining da warmers .  **a week later abun jawad kara gaba yakeyi don duk hankalinsa baya kan kowa yakoma kan rufaida hartakai baya wani cin abinci gurin aiki ma bazuwa yakeyi soseaba yajefa  kanshi cikin damuwa duk abin duniya ya dameshi.  Wani zazzafan aiki momy take kullawa a kanshi wanda tana tunanin indai har wannan tarkon yafada to sungama da jawad don duk dukiyarsa zata dawo hanunta. Ikram tashiga damuwa ganin yanzu jawad baidamu da itaba baya kulata don ko dakinsa taje saiyace tafita bayason damuwa hakan yasa itama   kullum jikinta a sanyaye duk rawan kanta ya ragu. Yau takama Saturday misalin karfe goma jawad yashirya cikin kananan kaya yayi matukar kyau zai kaimawa Hamid ziyara yashigo gurin momy zai mata sallama . a hankali yaji magana na tashi a bedroom din momy da'alamu sirri akeyi, harya daura hanunsa kan handle din kokar yasauke yana sauraron maganar da akeyi.  "Ke ikram!, kitsaya ki saurareni." Momy tadaka mata tsawa, " ya i'na fada maki abunda zakiyi kina bijiremin, kinga wannan itace damarmu ta karshe gurin mallakan dukiyan jawad, idan har tasubuce mana to ni bansan wani hanya dazamubiba. Tunda ke a matsayinki na 'ya mace kinkasa daukar hankalin sa, kinkasa bashi kanki bare kisamu ciki muyu amfani da wannan dama ya aureki kin kasa ...to wllh wllh idan kika batamin wannan shirin Allah saikin barmin gida kinkoma can matsiyacin gidan ubanki..wllh kinji na rantse."  "To fisabilillahi momy don bake kika haifeshiba sai kirinka mishi mugunta, ni gaskiya mo..."  Gwabje mata baki momy tayi saida yakawo jiki.. "Ke dan uwarki a i'na kikaji bani na haifi jawad ba!?,, a 'ina kikaji dan kan uwarki." Tsawan da momy tayi yayi balain gigita ikram a kidime tace "abakin ...Umma na naji..tana fada.." Wani ashar momy ta mulmulo ta kwad'a "zan gamu da i'ta, zata fadamin dan ubanta, wato shirrina take barbadawa ko.."
Ko i'na na jikinsa rawa yakeyi, kansa balain sara masa yakeyi , kafafunsa neman gaza daukansa sukeyi , dakyar ya i'ya jan jikinsa yafita yakoma part dinsa yasama kofar key yafadi kasa gaba daya hankalinsa tafiya yayi baisan inda kansa yakeba.

Don't forget to follow and vote

*👄habiebah lurv👄*

💝MUK'ADDARI💝Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz