21/06/2018
🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵*Labarin wata mata*
*Almost true life story*
Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐Page *1*
*Bismillahi Rahmanir Rahim.*
Alhamdulilah Ala kulli halin. Ina godiya da Allah da ya bani ikon fara wannan rubutun nawa na littafin *Koma kan mashekiya.*
Daga jin sunan littafin ma kasan abinda kake kokarin yiwa wani na mugunta shi zai koma kan ka.
Ina fatan abinda yake ciki na fadakar wa Allah bani ikon rubutawa sannan Allah yasa jama'a su fa'idantu da koyar war dake ciki.
Abinda yake ciki ba dai dai ba. Allah ya kawar da hannu na daga rubuta shi.
Alhamdulilah. Ina kara godiya da Allah da yake bani ikon isar da sakon da nake dasu.
*Inawa yan uwa musulmai barka da sallah da fatan anyi sallah lafiya. Allah ya amshi ibadun mu.*
*Ameen!******-----*****
Sanye take da katon ruwan kasan hijab din ta wanda ya rufe mata duk kan jikin ta.Fara ce, tana da idanu, me dogon hanci, tana da tsayi matsa kai ci.
Tafiya take cikin nustuwa, har ta iso kofar wani katon gida.
Da sallama ta shiga, ta gaida me gadin.
"Baba ina yini?"Cikin sakin fuska ya amsa, mata da
"Lafiya lou. Amina. Ya gidan da su Babar taki.""Suna nan kalou."
ta bashi amsa."Kwana biyu kin buya."
Mai gadin ya tambaye ta."Wallahi Baba makaranta ne shi yasa."
"Toh Allah bada sa'a.""Ameen ya Allah!"
Ta fada tana yin cikin gidan.A harabar gidan ta hango shi zaune akan kujera, hannun sa rike da jarida yana karantawa.
Dattijun mutun ne, fari da shi, wanda daga kallon sa kasan mutumin kirki ne, ga addini. Dan gefen sa alkur'ani ne.
Karasawa tayi wajen da sallama. 'Dagowa yayi ya amsa mata cikin sakin fuska.
Durkusawa tayi, a kasa, murmushin kan fuskar sane ya dado, yace,
"Sannu da zuwa.""Yauwah Abbah. Ina yini?"
ta gaida shi."Lafiya lou kuna lafiya?"
Ya tambaye ta."Lafiya Lou Alhamdulilah."
Ta fada tana mika masa."Daman goro ne, na ce, bari na kawo maka."
Ta mika masa,"Amina kenan bakya gajiya dai kullum cikin hidima."
Abba ai ba yawa, daman Farouk ne, ya ce, kana son goro shine nace bari na kawo maka."Murmushi yayi, ya ce
"Allah sarki. Allah yayi albarka."Kanta a kasa ta ce,
"Ameen Ameen!""Na zata lafiya Ahmad karatu zaki dauke kafa. Sai dai gashi baki manta da mu ba."
Murmushi tayi, ta girgiza kai.
"Haba Abba ai da Ahmad yana nan da baya nan duk daya ne a guri na. yadda kuke mahaifa a gun sa nima haka kuke a guna."Kai ya girgiza, ya ce,
"Allah sarki. To Allah dai yayi Albarka. Kuma gashi kinzo gidan ba kowa sai ma'aikata kawai.""To bafa na tafi in sunzo a gaishe dasu."
Ta fada yana mikewa.

YOU ARE READING
Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)
FanfictionLabari akan wata uwar miji wacce ta takurawa matar dan ta tin kan suyi aure. Komai ta tashi ta turo mata but sai ya kare akan ta. Shin uwar mijin na gane gaskiya ko kuwa? Mushiga ciki dan jin me ke akwai.