*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)
*SIRRIN MIJINA*
*Billy Galadanchi*
Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)**Salon rubutun wannan littafin yasha banban da wanda na saba rubutawa, zakuci karo da kalmomi masu nauyi aciki wanda wasu zasu kalla a matsayin batsa,sedai kuma ba batsar bace haka salon rubutun yake saqon mu baze isa ba se dole ta wannan hanyar sabida haka dan Allah kar wacce ta zageni, idan kinji bazaki iya biba ki hakura da karbar saqon, Allah yaga zuciyata kuma kowa ya sanni bana wannan shashancin a books nawa sam.....sabida haka dan Allah banda zagi*
01
Cikeda nutsuwa Nafeesah ke tafiya cikin uniform d'inta kalan light and dark purpule na makaranta nursery da primary ta cement primary school dake jihar sokoto a unguwar Wurno road, sauri take janye da hannun qaninta shuraim yayanta sudais ya musu nisa acewarsa idan yayi late shi kadai za'a doka a school, duk yawan horn da ake rafka musu be saka ta tsaya ba seda tajiyo muryan qawarta Zuhrah tana kwalla mata kira sannan taja birki ta tsaya ta waigo tana kallon ta,washe baki zuhra qwasai tai sannan tace tana mata alama da hannu
"Kizo mana a diremu a school tare munyi late kuma naje gidanku mami tace kin wuce tuni" murmushi itama Nafeesah tayi sannan tajuya riqeda hannun qaninta shuraim suka shiga motar ta kalleta tace
"Aunty qwasai sarakan surutu kinji yanda harshenki ke tashi kuwa,kinfasan mami tace ba kyau mace magana tana d'aga murya ke bakya ji" tsaki taja tace
"Sunana Aunty qwasai kuwa fad'i ki qara,nifa Nafee nafiso ki gano cewar muryana Allah yamun shi a haka bawai nice nake rakad'i ba,kinga ni bama wannan kinsam wai jiya daddy ya dawo bari kiji tun daga kan Apple babu wani nau'in 'ya'yan itacen dabe kawo mana ba,bari ma kiga yau lunch box dina babu ne kurin babu aciki" inda sabo Nafeesah ta saba da wannan halin yawan surutun na qwasai se ttace a qoqarin kawarda zancen
"Kinyi home work da aka bamu na maths kuwa?" murmushi tayi
"kinsan ni sam bana wasa da home work,tuni nayishi wollah m" bata qara cewa komai ba har suka isa qwasai keta faman zuba, kai tsaye class takai shuraim dake nursery 3 ta wuce parimary 5 dama nanne class d'insu.....
Bayan da aka tashi break ma bakin Aunty qwasai be mutu ba, duk wani dan ajin dasuke dashiri seda ta bashi labarin tsarabar da daddy ya kawo musu daya dawo daga kaduna jiya, Nafeesah se faman hanata takeyi amma abin yaci tura kowa se kallonta yake tana zuba
"Mommy ma fad'a takeyi da daddynmu wai ze qara aure tace inka isa,bakiga yanda ta burgeni ba datamai masifan yanzu ai dolenshi jiya naji yana bata haquri akan ya fasa qarin auren" wani takai nafeesa taji
"Kekam zuhra wai duk hiran gidanku semunji ne ko waya tambayeki ne anan wurin?" gwalo ta mata
"Kurun dai kice bakyaso in gaya musu en Nepa sunzo sun gutsure wutar gidanku tun ranar juma'a,koki rantse ba'a gidanmu kikai gugan uniform naki ba? Tunda ban gaya ba aiba ruwanki dana mu gidan" takaici ya ishi Nafeesah dama gata da qarancin shekaru amma akwai hankali, batace komai ba tabar wurin yayinda d'aukacin yaran dake wurin suka kwashe da dariya abin yayiwa Nafeesah ciwo ya sanya ta fasa yin break gaba d'aya takoma class ta zauna tana kuka, a haka Nihla tazo ta sameta ta riqe mata hannu
"Pheey dan Allah idan Aunty qwasai tana sha'aninta kina zura mata ido,kinsan halin zuhra sarai duk sanda kike mata gyara lokacin take miki wani tonon sililin ni breakfast d'inma ki dena zuwa field nima zanna riqa tsayawa anan munayi a tare" share wayanta tayi abinka da yaro seta ware suka ci abincinsu a class suna hira, koda aka tashi jan hannun shuraim tayi suka nufi hanyar gawon nama inda dama nanne asalin unguwar su suda su Zuhrah gaba d'aya, can daga mota Aunty qwasai ta kware muryanta
YOU ARE READING
SIRRIN MIJINA
RomanceKo kad'an Nafeesah bataso idanta yake shiga cikin na Dr. Hisham, takasa gane inda zuciyarta ta dosa, menene amfanin wannan baqar rayuwar datakeso ta jefa kanta aciki, menene amfani wannan baqar zuciyar tata, ina amfanin rayuwar da shed'an yayi qawan...