*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)
*SIRRIN MIJINA*
*Billy Galadanchi*
Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*24
Wani kuntane lullub'e Nafeesah dabtasan tana dashi ba se yau,ta sauke qwayar idanta a qasa dukda yake dama babu wadatar haske a wurin, ta kasa koda kwakwaran motsi hannunta ya kama ya soma murza mata en yatsunta a hankali cikin wata murya me sanyi dabatasan yana dashi yace
"Nafeesah namiki laifi,namiki shishigi daban sanar dake kokuma na nemi izininki kafin najega zancen aurenki ba, amma dan Allah kiyi hakuri sankine ya janyomun hakan,banida yanda zanyi arayuwa idan banyi shigar sauri ba wani ne ze rigani,faruwar hakan kuma tamkar rushewar rayuwata ne,kuma najene kurin neman aurenki se sukace a daura kiyi haquri" murmushi tasake masa dukda hawayen idanta be dena saukaba tace
"Ba komai yaa safwan baka mun laifin komai sema taimakona dakayi nagode sosai da wannan soyayyar daka nunamun nima ina qaunar ka" janyota ta qarayi ajikinsa ya sanya lallausan harshensa ya shiga lasar hawayen nata daga qarshe ya sanya bakinshi ya damqe lips nata duka biyu ya tsotsa sannan ya janye bakinshi ya qara maida yadan ciji lip dinta na qasa passionatley dan qara tayi "Auuchh" shi kuwa yae dariya......
Yaudai Saffwan beje gida ba se after 9 na dare wanda yae mugun d'aga hankalin Shamsiya tare da wani zazzafan kishi dake shirin illata rayuwarta gani take tamkar yana can gun Nafeesah tunda sukai waya da yamman dayake cewa za'a daura aurenshi be qara nemanta ba mutumin da yake iya kiranta duk bayan 30mns lallai ta yarda kishiya musiba ce tayi kuka tamkar ba gobe duk ta rame a wuni d'aya!!!
Da sallamarshi yashigo gidan shirun dayajine ya tabbatar masa cewar yaran sa duk sunyi bacci wrist watch d'inshi ya kaiwa kallo yaga 9:43pm qirjinsane ya doka ya tabbatar yanada aiki a gabanshi yau sabida qure mutum me hankali da haquri ba kyau ya amincewa kanshi yau ya tab'o mace mafi soyuwa agareshi sabida ko qara nemanta beyiba dukda yake dai cajin sane ya qare kuma a office bega chager dinsa ba ya nema!!! Kai tsaye d'akinta ya wuce ya tarar ta idar da sallah tana zaune saman sallaya d'inta zama yayi a gefen gadon yayjn da ta miqe ta linke sallaya ta sakaya murmushi me ciwo a fuskarta tace
"Sannu da zuwa Abul khair ina cikin damuwa ka jima baka dawo ba kuma ba waya" riqota yae ya d'orata kan cinyarsa ya zare hijabin jikinta ya d'aura lips d'insa a gefen wuyanta ya sumbaceta
"Kiyi haquri very own wlhy cajin wayanane ya d'auke kuma sena jima ban dawo ba motar ne ya samu matsala a hanya" kallon shi tayi ido cikin ido ta miqe daga kan cinyar sa....
"Very Own sam bakai kyau da fad'ar maganar daba gaskia bace bakayi kyau ba sam kuma bata karb'ekaba sabida baka sababa sam, Yanayin Qamshin jikinka kawai ya isa shaida akan ka gauraya mun jikinka dana wata bani ba" ta qarashe maganar cikin toshe baki sabida kukan dake shirin qwace mata tasowa yae ya birkitota ta fuskancesa
"Haba shamsiyyah? Kalli yanda kikai ramar kwanta d'aya kacal inata ga sauran ranaku masu zuwa, haba shamsiyya na, ban sanki da hakaba kinsan banida ta biyun ki a duniyar nan wlhh ina matuqar qaunarki auren Nafeesah qaddara tace babu yanda zamuyi, kuma wayana ki duba wlhy babu cajine amma kina raina" d'ago jajayen rinannun idanuwan tae ta kalleshi
"Ba komai Abul khair kurin dai wlhy da ciwo yaa safwan, da zafi kishiyar nan wlhy banaso hakuri kurun zanyi" rungumeta yae tsam yana babbuga bayan ta a hankali bayan yae wanka yaci abinci ma seda ya tara da ita sabida ya samu ya gusar mata da hankali da duk wata damuwa hakan kuwa akayi baiwar Allah seta manta da komai suka yi baccin su cikkn jin dadi da qaunar juna......
Hisham koda yaje gidan sa ya shaqa ba kad'an ba, qwaqwaran bincike ya tabbatar masa Nafeesah aure tayi idan abinda yakeji gameda Nafeesah shine sha'awa ba soba kamar yanda ta fad'a lallai yana cikin masifa zuciyars harta soma kora masa shawarar ya soma neman matan banza koze had'u dame ni'imarta amma Allah ya ceceshi be gamsu da wannan shawarar ba..... Tunani farko daya zo masa shine kurun ya qara aure!!! Ya shafawa pheey lapiya dan ta masa nisa baze iya bin matar wanin saba dan Haka ya dauki danganar musulunci.
Phey a wannan ranar kasa bacci,duk da babu patient da yawa amma sam ta kasa runtsawa zuciyar ta na gun Saffwan tana matuqar qaunar sa, duk juyin dazatayi seta tunano wannan d'an cizon daya mata lip har cikin ribs nata take jin wani iri dabata tab'a tsintar irin wannan yanayin tare da kowa ba se saffwan dinta, juyi ta shashi har safe.......
Tunda safwan ya fito zejw office yakasa haqura seda biya gun Nafeesah, har cikin gidan ya shiga da sallamar sa Amrah ta masa iso har cikin gidan har dakin pheey aganin ai mijinta ne, Lokacin da pheey tajiyo sallamar Amrah tana ban d'aki bata tab'a tsammanin cewar wai Saff zeyi qarfin halin wuce parlor har zuwa bed room nata ba, iya cinya towel dinta yake tana riqe da matajin kai tana taje kanta ta fito bata kula dashiba sam ta soma shirin zama kan dressing chair domin shiri ata mirror ta hango mutumin qara ta qwalla tamiqe domin qurewa cikin ban dakin shammatarta yae ya cafko ta,kunya kamar ta kasheta ta runtse idanta,dariya yae yace
"Ihun me kike Sweery? Sabida mijinki yazo gareki, aunty Amrah ce tace na shigo kina wanka idan kin fito na baki aikin daze mayar dake ban d'akin yin wanka mafi tsafta" sarai ta gane idan ya dosa ta soma qoqarin janye jikinta daga nashi gaba d'aya riqon sosai ya mata ya lalubo kakinta ya zura a nashi kasa koda qwaqwaran motsi tayi haka ya dinga tsotasr bakin seda dan kanshi ya isheshi sannan ya sake bakin ya kai hannunshi a saman dukiyar fulaninta daya d'ayan hannunshi na saman qugunta a ta baya ya matse ta a jikinsa, wani yanayine nafisa ta tsinci kanta aciki me wuyar fassara ta kasa qwace kanta daga jikin saffwan bazata kuma iya daurewa kanta yanayin datake ciki ba!!! Cikin raunin murya tace
"Kayi haquri yaa saffwan ba kyau fa" dariya ma ta bashi ya matse dukiyar fulanin sosai seda tae qara sannan ya saketa yaja baya zuwa bakin gadon
"Oya ki sanya kayanki muje parlor" maqe kafad'a tae
"Niseka fita zan saka kayan waini wama yace kashigomun har nan?" Cikeda shagwab'a tae maganar miqewa yae yayo kanta da gudu tayi ban d'aki tana dariya shi kuwa ya koma parlor d'in yana murmushi yana mamakin kunya irin na nafeesah aure kusan biyu amma kunya ya miki yawa har haka"
Yaudai Hisham ya shirya zuwa gidansu wata nurse dake aiki anan tare dasu yanayin jikin yarinyar irin na napheesa ne sedai Tafi Nafeesah kyau nesa ma ba kusa ba, shiba fuskar ba ba abinda yake buqata irin ya kwanta da ita yaji irin gard'in Nafeesah!!! Yasni tunda suke kamanceceniya ta hanyar jiki dole dad'in su yazo d'aya da wannan yaje gidan kuma cikin lokacin dabefi mintuna goma ba ta amince masa har tana zagwad'i.....tana shiga cikin gidan ta tafe da uwarta tace
"Hajjaju erki tayi muji fa, Babban likita yasin acewarsa ma ze turo wanj satin, oganmu fa a wurkn aiki, shekaru kusan 6 muna wuri daya yanzu yazo da zancen aurena,Allah hajjaju zakici kaji ( mahaifiyarsu suke kira hajjaju kowama haka yake kiranta).... Ihu yasomayi tace
" Bazan bari wannan ya wuce mu, gobe zanje gun me wankan maniyyi a gama mana dashi,ya sunan sa?" Tafawa suka qarayi tace
"Sunansa Hisham" rawar tsohuwar banzar tashigayi tace
"Wayaga Gimbiya Sa'ade da Hisham tabb wlhg en baqin ciki sedai su mutu,suna raye zasuganki da auren gata ehe!!!!!
Zuhra dai bata yiwa Hisham magana har girki tadenayi dashi shi kuwa hankalinsa baya kanta yanzu ta Sa'ade yakeyi ji yake tamkar yae kururuwa akan san ya sauya takalmin shuri.
Nagode da comments en wattpad kuna qoqari sosai.
Mutanen whatssapp ma ba'a barku a baya ba Allh sassaka da alkhairi.
Mom Nu'aiym
YOU ARE READING
SIRRIN MIJINA
RomanceKo kad'an Nafeesah bataso idanta yake shiga cikin na Dr. Hisham, takasa gane inda zuciyarta ta dosa, menene amfanin wannan baqar rayuwar datakeso ta jefa kanta aciki, menene amfani wannan baqar zuciyar tata, ina amfanin rayuwar da shed'an yayi qawan...