page 14

6.8K 551 36
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

Wattpad 68billygaladanchi.

           14

Zaman dirshan tayi asaman kujerun da aka qawata wurin da patient ke zama ganin likita tayi, wani kukan takeso tay tun d'azu mutane sunyi yawan dabazata iya kukan ba sam yanzu kuwa sun d'ahirta sosai wanda ya bata damar fashewa da kuka iya qarfinta meta yuwa mommyn zuhrah zata koreta daga gidan dan taga daddy baya qasar? Menene laifin ta arayuwa?

"Allah ka kawomun agaji,Allah ka bani mesona,Allah ka tallafi maraicina ya Allah,Allah ya Allah ka dubawa maraici na ka agazamun" atagefen window dake wurin CMD ne na asibitin da kuma wasu mutum uku masu take masa baya,mantuwa yayi yatsaya domin baiwa d'aya daga cikinsu key na office d'inshi sabida ya d'akko masa...kallon d'ayan yayi bayan ya dakata da magana ya d'an d'aga masa hannu alamr yae shiru

"Malam sani kamar kuka nake jiyowa daga cikin d'akin nan" d'an russunawa yae yace

"Yallab'ai haka nima nakeji daga cikin gynae emergency din nan ne, kuma kamar kukan babba ma gashi yanzu hudu ta gota sukam ma ai sun jima da watsewa kamar ba kowa" 

"Jeka ka dubo seka sameni mota kaida Auwal"  har ya juya sekuma ya dawo ya qwalla masa kira yace

"Jeka mota ka kaimun jakana ungo key,bari zan duba da kaina" ya fad'a yana miqa masa russunawa yae ya karb'a sannan ya juya, a hankali ya tura k'ofar ya shiga wanda Nafeesah batama san da zuwan saba sunkuyawa yae har qasa sosai kusa da ita yace

"Baiwar Allah lapia dai?". D'ago jajayen idanuwanta tayi ta diresu a kansa atake ta miqe tace murya na rawa

" Barka da wuni yallab'ai" kasancewar tasanshi tunda shine chief medical doctor na asibitin gaba d'aya!!! Miqewa yayi shima kasancewar ya gane yarinyar yace

"Dr.Nafeesah u!! Why?" Kasacewar shi d'an boko gakuma gayu yana ratsa shi matashi ne shi d'an komanin shekaru 37 aduniya yanaji sosai da quruciyarsa ta shiga jerin matasa sa'a yaci dakuma qwarewar shi yakai wannan babban matsayin cikin qanqanin lokaci...sadda kanta tayi qasa sosai tace

"Kainane yake mun ciwo" kanllonta yayi ya gyara zaman madubin idanshi yad'an karkace kai sannan ya d'age girarshi d'aya abinda ya zame mai d'abiya lokaci d'aya ya d'age kafad'unshi duka biyu had'e da sanya hannayenshi duka biyu cikin aljihun wando suit baqaqe dake jikinshi

"Mesa zakiyi qarya?,ko yaro ne yake ciwon kai baze zauna anan yana rusar uban kuka shi kad'ai ba bare zankad'ed'iyar budurwa irinki, idan akan mutuwar mijinki ne ki sani haka Allah ya tsara kuma ba'a tab'a barin wani dan wani dan Allah kiyi haquri karki janyowa kanki wani ciwon" girgiza masa kanta tai alamar gamsuwa da bayanansa ta furta da qyar

"Nagode sir" be jira komai ba ya juya yabar wurin ita kuwa ta fito kai tsaye gidansu na iyayen su ta wuce dama ta sanya su Aunty Amrah su gyara mata shi tunda yake mommy ta koreta ita kanta zuhran batasan se meta mata ba ko wayarta bata d'agawa !!! Da sallama ta shiga suka gabatar mata da abincibta d'an tsakura kad'an taje ta watso ruwa tai sallah la'asar ta kwanta aikin kenan ba uban tunani bata samun ishashen bacci sam....hawaye ta somayi ita ba wani kudin ba yanzu data soma service kuma shikenan en kudin dazatana samu qarshen wata befi 20k ba, wannan housemanship datakene take samun uban kud'i da Allah yasanya en gidansu Mukhtar sun mata adalci ma an raba gado har ta samu gidaje kusan uku da mota daya sannan ga fili biyu ga maqudan kud'i aida ta kad'e gadan rashin mutumci mommy da shuraim ta had'o ta jiya taga wulaqanci kam....Sallamar Aunty amrah ne ya katse mata tinanin ta ta zauna kusa da ita tace

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now