*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)
*SIRRIN MIJINA*
*Billy Galadanchi*
Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)**wattpadd 68billygaladanchi*
*Nagode sosai da kyawawan addu'o inku agareni Allah yabar qauna*
27
Gabaki d'aya Saffwan kasa nutsuwa yae ganin shamsiyyah bata dawo ba, ya sani fushi tayi shi kuwa a tmrayuwa ya tsani fushin shamsiyyah macece mafi soyuwa a gareshi da har abada baze samu wacce tafiye masa itaba, miqewa yae yana ganin jiri ya soma daddafawa ya sakko har qasa ya nufi hanyar d'akinta na qasa, kai tsaye ciki ya shiga,ya tarar tana zaune kan kujerar dake gaban mirror zuwa yae ya sunkuya ta gaban ta yace
"Baby dan Allah kiyi hakuri bana fatar abinda zanyi da bakya so, nasan kinada hakuri dan Allah ki qara kuma ki dauki Nafeesah matsayin qaddaramu baki d'aya, Zan mata waya nace karta qara zuwa idan na warware zanna ziyartarta da kaina" Hawayen datake qoqarin riqewa ne ya silalo mata tace
"Banji dad'i ba ko kad'an dana maka tsaki Abul khair wlhy sharrin zuciyane, da kishin wannan matar naka dake d'awainiya dani dan Allah yaa safwann kai hakuri bazan qara ba, babu laifi ko kad'an awurin mace dan tazo duniya wa mijinta mara lapiya, nasani nayi saurin fushi dama ba aure a tsakanin ku ne amma da aurenku be kamata nayi hakan ba kayi hakuri" jan hannunta yae suka koma kan gado ya janyota jikinsa gaba d'aya ya sanya harshensa ya soma lashe mata hawayenta
"Ba komai Baby, ko abinda yafi tsaki kikamun bazanji komai ba, ke macece ta gari na tabbatar duk abinda ya sanya har kikai fushi toba ke bace da laifin nine, kinada halaye na gari nagartattu masu kyau wanda nake miki fatan su kaiki aljannah, abu d'aya nake roqo a wurinki shine ki rage yawan kishin nan idan baki sassautaba zakiga abubuwa zasu ta cab'e miki sabida wasu rigimar da zargin kinayin sune kurun bisa rashin hujja dan Allah ki daidai ta" rungumeshi ta qarayi
" Inshaa Allah i will for ever be a good wife to u my man" murmushi yae ya sani shamsiyyarsa daban ce yasani rashin shamsiyya agareshi babbar asara ce baze tab'a samun mace kamarta ba.....
Pheey tunda taje gida ta shiga hada hadar had'a masa kunun sanga sanga se yamma ta zauna, driver ta kira a waya dayake ta karbi lambarsa ya dauki iya garin kunun da kayan hadin tace akaiwa shamsiyya ta karbi lambar shamsiyya a hannun driver kanya isa ma ta kirata
"Anty shamsiiya barka da gida yame jiki?" Murmusawa tae sabida ta gane muryarta tace
"Lapia qalau Nafeesah ya qoqari, yazu driver ya kawo kaya yaya za'ayi dasu bayani ta mata na komai sannan sukawa juna sallama cikeda karamci, shamsiiya da kanta ta had'a komai taje ga mijinta seda yasha kunun ta tayashi wanka yayi da ruwan na sanga sanga tafasashe yar har sirace ma sannan ya dawo daki yae sallah yaji matuqar dad'in jikinsa tunda ya soma shan kunun yake had'a gumi yanajin sauqi na saukar masa a hankali....
"Waike Zuhrah tukunna ma kin qara zuwa gidan naki kinga halin da aikin yake ciki kuwa, ni senaga ma kamar kwata kwata bakwa waya da Hisham d'in" tab'e baki tayi
"Anty Angel wlhy banje ba, kumama Hisham aiki ya masa yawa kullum tiyata kullum CS yakan kirani amma busy yake arana befi so daya ya kiraniba ya dinga bada haquri kenan wai aiki" jinjina kai Anty Angel tayi
"Ki tashi mu tafi mu duba gidan, muna cikin gari d'aya zamu zauna bamuje munga yanda aiki ke tafiyaba, ai kyau komai yaje daidai da tsarin mu tunda yake Allah ya taimakemu mun kore waccen karuwar agidan" miqewa tayi
"To muje kam yafi Gaskia"
************
Mamakin duniya ya d'auke zuhrah da mari itada pheey ganin wata zuqeqiyar yarinya tayo rakiya daga cikin gidn tana dagawa baqin hannu har inda suka bar harabar gidan,yayinda suka bi motar da kallon mamaki kafin su nuyo zuwaga budurwar ta b'acewa ganin su.....da wani mamakin suka kalli suna sannan suka soma sassarfan shiga cikin gidan da iya qarfin su a parlor suka tadda Hisham yayi zaman dirshan a qasa yarinya ta zauna saman kujera tana yawo da zara zaran en yatsunta saman sumar kansa yayinda yake lumshe idanshi yana bude wa a hankali kukan kura zuhra tayi ta wurgar da ummi dake hannunta tayi kansu ta haye wuyan sa'ade ta shaqe ta
YOU ARE READING
SIRRIN MIJINA
RomanceKo kad'an Nafeesah bataso idanta yake shiga cikin na Dr. Hisham, takasa gane inda zuciyarta ta dosa, menene amfanin wannan baqar rayuwar datakeso ta jefa kanta aciki, menene amfani wannan baqar zuciyar tata, ina amfanin rayuwar da shed'an yayi qawan...