page 7

8K 457 23
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

Wattpad@68billygaladanchi
Vote! Vote for me plsss.

                   07

Seda yagama yimata lilis sannan ya shurata gefe ya wuce, da qyar ta tashi a wurin ta shiga cikin dakinta,yau kukan ma ta kasayi, se numfarfashi datake saukewa a hankali....Akwai yara biyu wanda suke mata aiki a gidan, d'ayar zatayi shekaru 40 yayinda d'ayar yarinya ce iya kacinta 14yrs a duniya, Babbqr me suna Amratu itace taje ta sameta a d'aki da ruwan dunmi me rub a ciki da towel, batare data nuna boye komai ba ta kalleta tace

"kiyi hakuri Nafeesah, ita rayuwar aure dakike ganin ta rayuwace me cikeda rud'u da kuma d'inbin qalubale, yana cikin manya manyan jarabawowin da mahaliccinmu ke mana domin jaraba imanin mu, lallai kin kasance mace me haquri amma cikin mata mara sa'ar samun miji na gari abin dogaro,ina kulawa da yanin zaman ki da kijinki tunkan yanzu, ina kuma tausayawa rayuwarki matuqa, abu d'aya nakeso shine ki riqe Allah ki jajirce wurin yawaita adu'o i da istigfari ba qaqqautawa, karki zamto cikin irin matan nan marasa hankali, wanda sam su duniyar suka saka a gaba, ina kula dake Nafeesah bayaga sallar farillah bakya d'oriya da nafila ko d'aya,sannan bakya yawaita tsawaita adu'a idan kin idar da sallah, sa'o'i ashirin da hud'u mahalicci ya baki a cikin kowane wunin sa me albarka, wanda albarkar sa ta sanya baki taba ji ya wuce kuma ya dawo ba, idan wuni ya tafi aka kwana an wuce wurin har abada, menene ze hana ke kuwa kiyi amfani da wannan damar wurin ceto rayuwarki da kanki acikin lokacin ki daure bayan kowace sallar Farilla dabata wuce daukarki mintuna 15 kiyi Nafila ta mintuna goma, adu'o'in samun nasara daneman yafiyar Allah kiyi acikin mintuna goma idan hada mintuna 45 kenan sun isheki akowace sallah idan kin samu lokaci da damar yin hakan, mintuna nawa dududu zaki baiwa mahaliccinki acikkn awa 24 daya azurtaki dashi akowa ne wuni, kike shaqar numfashi batare dakin biyashi sisin kwabon ki ba? Kike tafiya da qafafuwan daya azurtaki dasu a kyauta duk kanin abinda ya baki a kyauta ne, kuma yace ki bauta masa ya baki lada, ki kuma roqesa ze karba miki, ki kuma yi ibada a qara miki nauyin mizaninki na ayyukan alkhairi daze kaiki ga dacewa  rana gobe qiyama, ya kamata ki farka ki gane kina cikin jarabawar mahaliccinmu sabida bakida kwanciyar hankalin aure, ga uwa uba bakida uwa bakida uba, qaninki ne kurin shima baya hannunki yaya kike ganin rayuwarki take a wannan bigire, tasowarki haka kurin be isa nusar dake dinbin rashin dakike ciki ba? Inaso dan Allah ki dinga ibada Nafeesah kallon qanwa nake miki uwa d'aya uba d'aya banda haka banda mugun nufi a kanki wlhy" hawayen satake ta tarewa ne ya silalo mata,yauce rana ta farko a rayuwarta da wani ya tunasar da ita gameda wacece ita, matsayinta na musulma tanada magnin dukkanin matsalolinta amma take wasa, zata roqi Allah daga yanzu ya yaye mata sha'awar Dr.Hisham dake d'awainiya da ita ya kuma shiryar mata da mijinta domin sune abubuwa guda biyu dake hanata sukuni a duniyarta,lumshe idanta tayi hawayen ya qarasa sakkowa ta saukesu a hankali akan amratu

"Nagode sosai Aunty Amrah, Allah ya bar qauna yakuma saka miki da mafificin alkhairinshi, kece mutumi ta farko data tunasar dani wacece ni a duniyar nan, ina miki kallon babbar har kullum, Allahu ya tallafi bayanki kamar yanda kikamun" riqe hannunta tayi tace "Bari na gasa miki jikinki, sannan inaso muyi wata magana dake me muhimmanci bayan hakan" bata ce komai harseda ta soma gasa mata jikin cikim nutsuwa ta soma magana

"Mafiya yawancin lokutan da uwar d'akina zuhra ke zuwa gidannan se inji bakuda wata magana seta hirar jajircewar gwarzon mijinta a saman shinfid'ar auren su, wanda yakanja hankalinki matuqa ki nutsu kina sauraren daddad'an labarin datake baki da har yake sanya wasu lokutan bayan tabar gidan nan sekinyi wankan tsarki!!!!!" Da sauri Ta d'ago ta kalli Amratu domin kuwa yawan ruwan datake fitarwa yayinda take kwasar dad'in hirar da zuhrah ke bata kansa ta gagara yadda da kanta akan tayi tsarki kawai harsetayi wankan tsarkin gaba d'aya take gane cewar tana cini tsarki wadatacce, wannan kuwa magana ce wacce bata tab'a gayawa kowa itaba se zuciyarta to ya akayi Amrah ta sani? Murmushi amra tayi sanda take daddana towel din me zafi saman kuncin ta daya dan kumbra sannan tace

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now