*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)
*SIRRIN MIJINA*
*Billy Galadanchi*
Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)**Wattpad @ 68billygaladanchi, follow and vote plss*
25
Wuraren 12 yabar office kamar ya da yasaba zuwa gidan cin lunch da qarfe d'aya yanaso yaje gun Nafeesah tukunna kan ya wuce gidan shisa yabar office d'in kafin 12 ma......Kai tsaye gidan ya shiga da sallamar sa ya tsaya tsakar gidana Aunty Amrah ya ci karo da ita tana fitowa daga ktchn suka gaisa tamai iso har cikin parlor d'in yayinda ta juya domin ta baro Pheey a ktchn tanaso ta sanar mata zuwanshi dukda ta tabbatar ta jiyo shi.....Sallama tayi tashigo parlor din sanye take da jar atamfa me ratsin fari aciki kadan tayi d'inkin riga da skirt skirt din da rigar tamkar ajikinta aka haliccesu tayi kyau matuqa ba d'ankwali akanta wannan ya tona asirin lallausan sumar kanta baqa wulik me sheqi wacce ta sakko har kusan gashin girarta tana neman had'ewa wani haske yaga ta masa a yau d'in nan colour d'inta asalin baqi me sheqi da kyau da tsantsi ga laushi se haskawa take, wani kalar baqine da pheey na en usulin hutu tabbas kalar fatar matar tasa ta tafi da imaninshi kasabcewar ba'a siyan ta a kanti wannan dashen na Allah ne kuma acikin dashen na ubangiji ma mafi kyau ne wannan d'in se wani coffee colour take masa a ido tana ebar masa hankali zuwa habuja da gudun fanfalaqi, miwewa yae ya rungumota gaba d'aya ya manna mata sumba a saman sumar kanta sannan ya dire duka hannayenshi saman chicks nata ya d'ago fuskarta xuwa fuskantar sa, beyi magana ba se kallonta yake yana zuba mata lallausan murmushi me qayatarwa,murmushin ta mayar masa
"Ina wuni yaa saff" langwab'ar da kanshi yae
"Afternoon pretty how r u doing?" Sauke qwayar idanta tayi qasa,ashe zataga gatan namiji har haka a rayuwarta dad'ine yake shirin sanyata kuka na haqiqa tanawa Saffwan so wanda bataji tana wa kanta irin shima,mutjm me qaunarka yafiye maka kowa shine namiji na farko bayan mahaifinta da yayanta daya tab'a sanya farin ciki a zuciyarta, qara d'ago fuskarta yae
"Heey pretty what's wrng?" Murmushi ta qaqaro wanda ina sena hawayen datake adanawa suka silalo mata wara idanshi yae....ya sanya hannu ya shafi qwllan
"Like seriously ur crykng pheey menene" murmushinta ta fad'ad'a
"Ba komai fa yaa saffwan, ganinka kawai seyake sanyani farin ciki, kuma se dad'i ya sanyani kuka amma ka yarda dani wlhy kukan dad'i nakeyi" rungumarta yae ya d'agata gaba d'aya yana zagaye d'akin da ita yana dariya seda ya gaji ya direta ya soma haki
"Pheey kinsan kinada nauyi wai tabb, shamsiyya na sam bata kaiki nauyi ba da ita na d'aga senay gudun awa biyu da ita ban gaji ba tsabar rashin nauyinta" murmushi ta sake masa lokaci d'aya taji wani abu ya dirar mata a qahon zuci wanda batasan ko meye ba shida kanshi ya kula da hakan...
"Bari inkawo maka ruwa" bece komai ya zauna ya kula so take ta d'auke wancen zancen shisa shima be matsa ba......Abinci ta gabatar masa da sancks tayi chicken bytes da kuma onion rings plus rice and stew with salad.... Se Fruity Zob'o dayasha had'i....wani dad'i ne ya ziyarcesa yanaso yaga ana kulawa dashi haka ba qaramin dadin yaji ba da kanta tae serving nasa zaman dirshan yae a qasa ya sanya hannu ya nuna kusa dashi
"Zonan pretty zoki zauna ki fuskanceni" ba musu ta zauna ya zaro lomar farko ya ziyarci bakinta dashi kawar da kanta tae cikeda kunya b'ata fuska yae
"Maza bud'e bakin ki nine yau zan ciyar dake menene amfanina aike er gata ce nida kaina zan baki abinci kici" cikeda kunya ta hangame baki ya zura mata tauna tashigayi a yangace ya shagala da kallon yanda dimples nata ya lob'awa duk yayin data tauna abincin na duka side din chicks nata, murmushi tae ganin yana kallonta ta sani ko tana school nutane nacewa da ita idana tana taunar abu tafi kyau dimples nata suna daukar hankali tasan shima wannan abin yake kallo da qyar ya saisaita kanshi yanda take taunar abincin a hankali ma ya burgeshi loma yakai bakinsa shima ya d'an sunkuyo da sauri
YOU ARE READING
SIRRIN MIJINA
RomanceKo kad'an Nafeesah bataso idanta yake shiga cikin na Dr. Hisham, takasa gane inda zuciyarta ta dosa, menene amfanin wannan baqar rayuwar datakeso ta jefa kanta aciki, menene amfani wannan baqar zuciyar tata, ina amfanin rayuwar da shed'an yayi qawan...