page 21

7.3K 617 125
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

                                         21
"Amma bakya ganin kin d'auka da zafi sosai Nafeesah? akwai aure a tsakanin ku har yanzu banaso kiyi amfanin da damar yana bibiyarki yanzu kice zaki mai wulaqanci" kallon shi tayi yanzu kam cikeda b'acin rai tace

"Haba Yaa safwan,Ashe dai dama can ba sona kake ba kenan idan da kai me sonane kamar yanda ka fad'a matsayin qanwar ka nake marigayiya zaka so awa qanwarka haka kuma ta komawa wannan mijin? Ka sani yaa safwan nasan ni mummunace nakuma san nime baqin jini ce agun maza amma wlhyl azeem bazan tab'a komawa auren Hisham ba,dana qara aurar Hisham gwanda na mutu babu aure har abada" kallonta yayi adaidai lokacin daya paka 10-10 d'in yace

"Allah ya huci zuciyarki" bata ce masa komai ba ya fice daga motar ya siyo mata shawarma da burger da kuma chips ya dawo be magana yau kuma mutumina mulki akeji abubuwan sun motsa .....Haka pheey ta mugun shaqa  dayake mata tayin komawa Hisham wannan ya sanya kowa yayi tsit bame  wa wani magana har suka isa gidan su pheey,tattare nutsuwarshi yae ya kalleta

"Ga abubuwa nan kije kici ki kula da kanki plss zan kiraki idan na gama me nakeyi daganan gun Hajiya zan biya" kallonshi tae ta dauki ledojin batare datayi maganaba ta fita seta tafice daga motar ta ranqwafo

"Nagode sosai Yaa safwan ka gayarmun da Aunty shamcia da yarana" d'aga mata kanshi yae fuskarsa ba annuri ita kuwa ganin haka ta juya kawai tana mamakin sauyawar fuskarshi a lokaci d'aya kodai maganar datamai ne beji dad'i ba? Batada amsar wannan tambayar ya sanya tae zuru a d'akinta bayan ta koma ranta duk a jagule....

"Kinga Zuhrah nima nan duk abin duniya ya dameni idan na d'aga kaina na ganni anan gidan yayanku ji nake tamkar ya bud'e in shge tsabar kunya da takaici,Alhajinmu yace ba gidanshi dole na na zauna anan matar yaron nan kuma bataso nake zama mata anan ko kadan da kika sani,idan bayanan ko parlor naje seta shige d'akinta ita da yaranta su rufe arayuwa naga ci baya da bantab'a zata zanga irinshi ba!! Ko yayanku da baya magana yake matuqar qaunata na kula ya rage sosai kamar ma haushina yakeji dandai ina uwarsa ne babu yanda zeyi dani,kije kiji da taki matsalar nima inji da tawa ninan adu'a kawai nakeyi sabida na laluba naga ba wata nasara a wannan abin damukayi" shiru zuhra tae kantace

"Amma mommy kece fa kika kawomun yanda za'ayi yanzu kuma abubuwa sun dagule sekice inje inji da tawa matsalar me hakan yake nufi kenan mommy? Kin jazamun tashin hankalin mijina kuma shikenan ba ko magana me sanyi?"  Kallon banza uwar ta Mata kantace

"Ke zuhra wlhy zanci ubanki, banda raini ni zaki gayawa koriyar magana, duk ba akanki na shige wannan halin ba? Koba akanki na shiga matsanancin hali ba da komawa baya gani dabas yanzu agidan d'ana duk dan farin cikin ki? Karki so ki maidani sa'an ki wlhy" kuka zuhrah ta sanya ta tashi tafita tana kuka kai tsaye gidansu Baby ta wuce qawar ta dake zaman zawarci a gidansu bayan sun gaisa ta sanya mata kuka sannan ta kwashe komai ta gaya mata dafe baki tayi tace

"Kinga zuhra bafa wai abun kuka bane wannan, ke sharri. Namijine baki sani ba? Ki sani sbida yaga akwai igiyar aure a tsakanin sune yake so ya maidata yana sani yake miki wannan iskancin wlhy, shawara d'aya zan baki ki dena bari yana tarawa dake idan ma yqzo da buqatarshi ki fito kanki tsaye ki sanar masa bakya so ya rabu dake yaje gun wacce yake kiran sunanta yake mafarkai da ita ke bar kiji yasin zuhrah kima dena shiga sabgarshi zakiga ya dawo hayyacinsa iskancine dame ta fiki?/wannan yarinyar me munin tsiya banda diri meta ajiye wlhy zuhrah karki saurara masa rainin hankali yakeso yazo miki dashi" murmushi zuhra tae

"Kumafa hakane baby, ki barshi xamu dawo rashin mutunci tsakanina dashi wlhy tunda shiya siya nagodr miki qawata dama nasan ke kad'aice zaki nemomun mafita shisa na garzayo" murmushi ta mata suka tafa sannan ta masa sallama ta tafi....

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now