*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)
*SIRRIN MIJINA*
*Billy Galadanchi*
Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*02
Kwanciya yayi sosai a saman kujerar dake juyi dashi cikin office d'insa, sam duk yanda ya yakice tunanin Aunty k'wasai a kanshi abun yaci tura, sosai yarinyar take burgeshi har mamakin kanshi yakeyi yanda surutun nata ma yake burgeshi dukda kasancewarshi sam bame san surutu ba ko kad'an....Haka kwanaki suka shede watanni ma suka kwaranya daga K'wasai har Pheey babu wanda ya tab'a koda tunawa da Hisham,yayinda shi kuwa yanacen yana tattalin soyayyar K'wasai data masa katutu gashi dai ya kasa komawa wurinsu,dukda yake duk qarshen wata yakanje duba store na magungunan makarantar kasancewar basa so a nemi koda magani daya a rasa....Yaudai gabaki d'aya Dr.Hisham mafarkai yae tayi da Zuhrah aciki, wannan ya sanya daga b'angaren shi yana watsa ruwa ya nufi cikin gidan, qanwarshi zaneera ya qwallawa kira ta fito da shirin ta na zuwa office ya kalleta yace
"Akwai d'alibarku fatima bintu zuhra, ina san a nemomin tarihinta sa asalinta kuma da cikakken adireshin gidansu" agogon hannunta ta kalla sannan tace
"Dr. Nayi letti amma ai Fatima Bintu zuhra kokai kasan gidan su, qanwar abokinka ne fa" da mamaki ya kalleta yace
"Wanne kenan daga ciki?" jalaludden mana dan gidan tsohon minister" dafe kanshi yayi yana dariya yace
"Lallai akwai aiki dama qanwar jalal ce, ke Aunty k'wasai ake kiran wannan" murmushi zanerah tai
" Yaa hisham ka manta tun shekaru biyu da suka wuce kamun waya akan yaa Jalal ze kawo qanwarshi da qawarta er maqotansu a school din mu a basu dukkan kulawa lokacin kaje wani course india to ai sune" jinjina kanshi yayi yace
"To naji kije kawai" murmushi tai
"Dr. Kodai kana ciki?" harara ya wurga mata ta kame kanta ta wuce tana mamakin shi, wannan yarinyar sarakan rakad'i da hauka shi kuwa meye ruwanshi da ita?". Shikam kai tsaye batare dayaci komai ba ya juya zuwa office inda yake babban likita a uduth...
Da yamma duk yawan gajiyan dayayi seda ya biya gawon nama gidansu jalal, yayita neman wayanshi bata zuwa dama, Ba kowa agidan se raba idanu yake,dama babu yara qwasai ce auta kuma an zama en mata se yaran yaa muhammad idan sunzo kuma yau basuzo ba kasancewar ana islamiyya yau talata, qara gwada wayan yayi shiru bata tafiya gashi kuma ya hango motar jalal a farfajiyar gidan, tsaki ya dire yace a sarari
"Barin haqura kurun" juyawan dazeyi yaci karo da Zuhrah da pheey ansha kwalliya ana takawa a hankali, be dauke idanshi daga kallon zuhrah ba har suka qaraso wurin shi, Pheey ce tadan russuna tace
"Ina wuni?" batare data kalleshi ba harga Allah susu biyun babu wanda ya gane shi"
"Lapia lau en mata,zuhra zo mana" se a sannan ta d'ago ta kalleshi batare data ganeshi ba tace
"Ina wuni? Ansata yayi yace
"Yayanki jalal fa yana nan?" kallonshi take kamar tasan fuskar "Ea yana nan a b'angarensu seda nakai mar abincinshi da magani sannan na wuce na dubo mamansu pheey dabata lapia shi dinma baida lapia zazzabin cizon sauro tun kwana biyar data wuce?" murmushi ya sub'uce masa kalli wannan karambanin dan Allah wannan ai itace redio me jini ya fada a zuci, a sarari kuwa se yace
"Kimun iso wurinshi idan ba damuwa" kan tayi magana se gani tayi Aunty Angel mijinta ya diresu gida itada yara aida gudunta ta kwasa aguje taje ta fad'a jikinta wai adole oyoyo take mata ga Angel da cikin yama shiga watan haihuwarshi ko yanzu dan bata jin dadine ya kawo ta gida, mari ta sauke mata cikin fusata
YOU ARE READING
SIRRIN MIJINA
RomanceKo kad'an Nafeesah bataso idanta yake shiga cikin na Dr. Hisham, takasa gane inda zuciyarta ta dosa, menene amfanin wannan baqar rayuwar datakeso ta jefa kanta aciki, menene amfani wannan baqar zuciyar tata, ina amfanin rayuwar da shed'an yayi qawan...