page 33

9.4K 665 97
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

  End

*Assalamu Alaikum ina baiwa d'aukacin mutane masu bin wannan book haquri akan rashin typing last page kamar yanda nai alqawari musamman mutanen wattpad, bada san raina bane ntwrk ne ya sanya wattpad dina yaqi gaba yaqi gaba har gogewa nayi na qara downloading wani amma yaqiyi seda na sake data zuwa Airtel sannan ya sakemun, ina fatan zakumun afuwa*

         33
Police ya kira cikin mintuna da basu wuce 30 ba segasu nan suka iso tare dasu zuhra harma da wannan qawar ta sa'ade....haka aka dinga case har kotu maganar acen dai aka yankewa sa'ade hukuncin daurin rai da rai aka kuma tursasa zaliha ta raka police gun boka aka kamashi shima aka garqame shi.......

    Pheey da Saffwan da shamsiyyah sune suka shige gaba gaba wurin ganin an samu daidaito tsakanin Hisham da Zuhrah inda suka dawo rayuwarsu me tsafta cikin aminci mommy da daddy sunga halacci awurin Nafeesah na sosai da sosai sun sanya musu albarka itada shamsiyyah ba adadi.....

*********
      A parlor saffwan yake zaune da Shamsiyya yana mata tsifa ta d'aura kanta a saman cinyarsa shi kuwa yana mata tsifar a hankali wai kartaji zafi.....cikin zolaya yace

"Very Own sumar kinnan yayi datti sosai duk kin gama b'atamun jikina da quran" turo baki tae a shagwab'e

"Haba Abul khair ni yaushe dudu na wanke kan, last week fa ka wanken kuma aka mun kitso dama babu wanda ya kaika hango dattin suma ai" murmushi yae

"Allah dai yasa ga zahiri nan duk jikina dattin kankine, ni muje na wanke miki ke kuma kimun wanka ki wankemun dattin da kika jona mun" bata kulashi ba dai harya kammala mata tsifar sukaje ya wanke ya busar mata da hand drayer se tsokanarta yake waime dattin kai,idan da sabo kuma ta saba da tsokanar dayake yawan mata halinsa ne neman magana seda ya daure mata gashin da ribon ya fesheshi da turarukan kai sannan yace

"Muje kimun wanka ko" dama jiranshi take ta kwasa a guje akan bazatayi wankan ba ta nufi hanyar waje, bin bayanta yae da gudun shima suka dunguna waje suna dariya acen suka had'u da nafeesah ta riqe shamsiyya tana dariya

"Oum saleem menene?" Qoqarin qwacewa take

" sakeni karya cafkeni Allah bazan ba" kan sui wani ynqurin ya qaraso yana qoqarin riqe shamsiyya bayan pheey ta koma tana qyalqyala dariya,ita kuwa ta tattareshi da hannanyenta

"Yaa Saff meye haka meta maka" dariya suke dukkansu suna haki...."Bauta ta sakani fa kuma shine ita bazata biyani ba, dattin kanta ta barbadeni dashi shine nace setamun wanka ta ciren dattin wai bazatayiba" dariya sosai ya baiwa pheey jin wannan abin sekacebyara shine suke gudu tace

"To kaje kayi da kanka mana Auntyna bazata wani cirema ka datti ba" hannu yasa ya janye pheey yana qoqarin damqo Napheesa suka juya aguje zuwa part d'in pheey dukkaninsu a parlor suka zube suna mayarda numfarfashi, ranqwashi saffwan ya kaiwa pheey

"Kega me anty  ko? Zaki fansheta ne danni yau dole se an ciremun dattin dake jikina,idan ba haka ba sedai ko wacce ta riqa zuwa salon nadena muku gyaran gashi" dariya suka saka masa dukkansu

"Munada komai na gyaran gashi a gidannan, kaga idan ma kace ka dena mana sena mata itama tamun nida Allah ya baiwa er uwa kyauta" Shamsiyya ta fad'a tana dariyar mugunta pheey ta masa gwalo ita kuma, qwafa yae ya miqe da sauri shamsiyya tasha gabanshi

"Wasa nake maka, muje na maka shi kenan" burge Pheey sukai tace lallai ga inda ake zuba love ko a gaban waye, tunda suka zama free dani nikuwa meze saka naji haushi nima in ware kawai a dama dani,kan wani yae magana yace

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now