*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)
*SIRRIN MIJINA*
*Billy Galadanchi*
Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*Wattpad 68billygaladanchi.
16
Shamsiya kallon sosai tawa mijinta se fara'a yakeyi tace dashi
"Very Own waimene yau se fara'a kake ko zamuje shopping ne" d'an murmushi yae
"Ea mana zamu iya zuwa amma ba'a aljihuna ba sam, sedai ki kaini ki siyamun abin dad'i a 10 10 tunda na miki fara'a se faman washe baki kike kamar gonar auduga me qaton ciki" dariya tayi
"Kaika sani dai ni muje inda gaske kake zaka ci abin dad'in" d'age girarshi yae
"D'aki wai? Zanci abin dad'i kam sosai ma" tagano abinda yake nufi tace dashi
"Rabu dani dan Allah, jidai shawarma nakeao inci kuma gaskia katashi muje" miqewa yae yana dariya yana mata waqa
" Er fara me qaton ciki, komai kikaso nizan miki tunda kin iya soyayya haka tashi muje yawon kwad'ayi kai" har yana rawa dariya ta tuntsire dashi tace Allah zanga ranar da zaka tsufa Very Own, yanzu harka had'a waqa haka kumafa har rawa kake" d'aukarta yayi gaba d'aya yace
"Barin rage miki hanya Very Own cikin nan na en gomane inshaa Allah" dariya tai
"En goma habyby sekace wani akuya gaskia ni d'ayane kuma me kama dakai"
"Hm hm ni Haris da Humaira sun isheni wannan cikin idan kin haifa na bar miki,kinga fine boi kinaso erki tai kama dani" dariya tayi
"Se boi kam, wayaga boi zuqeqe dakai kace wani boi, banda hancin nanma bazanso princess ko prince na suyi kamada kaiba da qaton kunnenka a wurin" direta yayi ya ranqwasheta da wasabta kwasa aguje haka suka soma zagayan parlor din sune har tsakar gidan har suka zo bayan gida suna gudu, tuntub'e Shamsiya tai ta fad'i a kife wanda ya mugun d'agawa Safwan Hankali da gudu yae kanta ba shiri, d'agata yae ya qura mata ido harta soma gumi, murmushin qarfin hali tayi tace
"Nika dubamun d'an yatsana kaji, wataqil qumbana ya fita dena kallona haka" bataji komai ba acikin kuwa se raunin d'an yatsa da kanshi yakaita yamata dressing wurkn se ihu take yana tausayinta yana kuma daria, bayan isha ya tsala wanka yace ze fita ta kafe seta bishi tasha mamakin ganin ya dage bazeje da itaba yabata mamaki sanin data masa baida wurin zuwa daya wuce gun hajiyarsa dan haka dazaran ze fitan dare tace zataje tare suke zuwa gun hajiyarsa mabera suje su dawo, batai magana ba dai ta qyaleshi ya fice abinshi yana mata rawa da qawa haris na kwasar dariya ita kuwa take tashiga damuwar inda zashi bayan baya zaman majalisa office kad'ai ke rabasu.....
Kai tsaye gidan su Nafeesah ya nufa seda ya isa sannan ya mata waya
"Hello Sir"
Kwaikwaiyara maganarta yae
"Hello ma" shima yae muryan mata dariya tayi
"Barka da dare yallab'ai" sosa kanshi yae ya gincira cikin sit din motar
"Hajiya ni banason gulma kin wani maqale murya zo wajen gidanku gani nazo mu gaisa" dariya tayi
"Haba sir maqale murya kuma" katse wayan yae batare dayace komai ba aramshi yana mamakin yanayin dad'in muryan Nafeesah ikon Allah mutum idan Allah yamai wata baiwa seka zata shiya halicci kanshi yanzu dai ji muryan Nafeesah sekace ba acikin wannan kumatun me kamar fankasau take huro shiba.... Shigowa tayi mota da sallama tana zaunawa ya kalleta
"Wlhy Allah Nafeesah kizo ki soma gyming irin wannan lukutewar da kike yanzu sabida Allah kalli kina zama kin lutse mun mota" takaicin shi taji amma se tai murmushi batayi magana ba
YOU ARE READING
SIRRIN MIJINA
RomanceKo kad'an Nafeesah bataso idanta yake shiga cikin na Dr. Hisham, takasa gane inda zuciyarta ta dosa, menene amfanin wannan baqar rayuwar datakeso ta jefa kanta aciki, menene amfani wannan baqar zuciyar tata, ina amfanin rayuwar da shed'an yayi qawan...