page 15

6.3K 507 43
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

         15
Kallon sosai Shamcya tawa Safwan tace cikeda kulawa

"My very own wai lapia kuwa tunda ka dawo gidannan baka cikin walwalar ka" d'an d'go kanshi yae da murmushi d'auke a fuskarsa yace

" Ba komai Very own me kika gani?" Gyara d'an kwalinta tae

"Ba haka bane nadaiga tunda ka shigo bakamun ko murmurshi ba, bama haka dakai nawan" ta d'age mishi girarta d'aya "kodai da wata a qasa ne" dariya ya kwashe dashi

"Sam ba komai a qasa tawan kawai dai akwai wani abinne dabe shafeki ba danake nazari a kanshi kuma nima bawai ya shafan bane nayi katsalan dan ne kurun kuma se tausayi ya aureni gaba d'aya i feel like help and st things out" jinjina kanta tasan hin Dr. Da mayar da damuwar wani tasa banda haka menene yasameshi haka kawai tasan baze raba nasaba da wannan yarinyar dabataga fuskarta d'azu ba...miqewa tayi da qaton cikinta daya mata gingirim tayi hanyar ciki domin zuwa watso ruwa,dariya ya mata yace

"Very Own wannan cikkn naki yana bani dariya sosai wlhy, kinga yan kika botse sekace me yara goma aciki" harar shi tae da wasa

"Allah ma daya taimakeni har yanzu baka fini kyawun kallo ba a fuska" murmushi yae ya miqe yazo ya rungumeta ta baya

"Very Own Allah ya saukeki lapia kud'in dazan kashe a bikin sunan nan Allah ne kad'ai yasan adadinsu inshaa Allah" manna mata sunba yayi a wuya ya saketa yana dariya

"Raguwa daga miki dan guntun sumba harkin soma shirin narkewa ajikina" batai magana se murmushi yanayin barkwancin mijinta yana burgeta sedai lokaci d'aya wasu lokutan idan kuma ya soma rikicinsa har tsoro yake bata....

Kasa nutsuwa zuhra tae da saqon nin data aikawa Pheey da hannunta, mesa take zargin er uwarta? Anya kuwa hanyar da mommy ke d'orata akai me b'ullewa ce? To amma kuma ai uwartace yaya zata cutar da ita? Sam bazata cuceta ba ko kad'an!!! In hakane kenan mommy dagaske take pheey nasan hisham, kumama har taji tana gayawa wata qawarta idan ta auri hisham seta koreta agidam to akan me ita kuwa pheey zata mata haka? Tunani dai barkatai takeyi tarasa madafa arayuwar ta,tana cikin babban tashin hankali mara misaltuwa tana qaunar pheey kuma tanaso ta saka mata da alkhairi amma rabata da Hisham tamkar rabata da rayuwarta me kumama ai mommyn ta bazatawa pheey qaryaba in hakane bazata qara had'a wata huld'a da ita ba amma bazata kuma zaginta ba inshaa Allah..a haka Hisham yashigo ya sameta se sallama yakeyi amma sam batasan da zuwan shi a duniyarta ba sam! Dafa kafad'ar ta yae

"Baby zuhrah lapia dai" kallonshi tayi lokaci d'aya ta narke fuska se hawaye

"Yaa Hisham dan Allah ka taimakamun na janye zancen wannan auren danake cewa kayida nafeesah wlhy na fasa wannan qudurin" mamakin ta yakeyi murmushi dai ya sakar mata

"Baby kenan nifa dama bance dake zan tab'a auren watama ba Nafeesah ba, banida tsarin mata biyu har abada basa gabana banida wurin ajiye su babu wata mace me waki gurbi azuciyata duk kin cike fam!! Bame wani hurumin ki katantane,bame matsuguni sabida dukkanin wani space kin mamayeshi kaf! Mezan yi da nafeesah baya naci ni Hisham da idan ma kishiya zan kiki sena auro wannan er uwartaki er baq'a, koba zancen baqi bama ni banasan mace me jiki ke kin sani zuhrah dan allah ki saki ranki kuma ki mayrada lamuranki gun mahalicci babu wata wacce zata shiga tsakanin zaman mu har gaban abada kinji ko?" Murmushi tay had'e da qanqameshi tana mejin dad'in kalamanshi har ranta, harshe ya sanya ya soma lasar mata kuncinta dake saukar da qwallah....

     Kwance Nafeesah take tana tunanin motarta gashi dai har gari ya waye amma ba'a kawo mata motar ta ba, kuma batada lambar CMD d'in nasu bare ta tambaya,miqewa tai ta sab'a jakarta ta fito da lab ct nasu a hannu ta kalli Aunty Amrah

"Motana har yanzu zanje na hau adaidaita kurun sauri  nake zanyi late" kallonta tae

"To Allah dai yasa lapia, Allah ya kaiki lapia mezan d'aura ne agidan yau" lumshe qananun lumsassun cat eye  d'inta tayi ta murmusa har kuncinta d'aya ya lob'a sanda take furta tuwon miyan kuka nakeso Aunty Amrah kuma dan Allah ki had'amun zob'o na kwana bi'u ban shaba ki sanya masa mnt lf da cucmber me yawa, kuma adafa da b'awon abarba"

"Inshaa Allah zanyi komai daidai Nafeesah".

A wahalce ta qaraso bakin titin sabisa batajin dad'in jikinta agabanta taga wata mota qirar benz fara qal me bak'in gilashi,zafin qasan daya samu taimakon wanzuwa sosai sakamakon AC dake hura sanyi aciki tare yake da wani dadd'an qamshi me sanyi, lumshe idonta tayi ta yamutsa fuska sosai har kumatunta duka biyu suka lob'a taja baya ganin yana shirin murje mata en yatsunta na qafa, murmushin sa ya fad'ad'a tunkan ya  sauke glass d'in sannan ya saukar yace yana had'e hannayenshi duka biyu wuri d'aya

" Tuba nake ranki ya dad'e yau nazo da kaina in direki har wurin aiki" sauke mata lumsassun idanuwanta tayk cikeda da kasala sannan ta sauke masa wani lallausan murmushi

"Ina kwana sir" shine abinda ta fad'a tana me qara langab'a r da kanta

"Lapia lau, Bismillah shigo muje mana" ba musu ta shige gaban motar ta d'an kishingid'a ta lumshe idanta

"Kalli gajeran hancinta kina wani yanga yar lukuta dake" murmushi ta sakar masa

"Naji dai ni nasan hancin nan nawa wlhy d'aid'aikun mutanene keda irinshi a duniya kuma me tsada ne sabida bakowa keda irinsa ba" dariya yae har qatuwar wushiryarshi ta bayyana yace

"Lallai ma lukuta anyi baki, waye ze siya wannan hancin da tsada, dama bakin dake d'an tsurut dashi kikace ko kuma wannan idan naki masu kama da idan bacci always amma zancen gaskia wannan gajeren hancin ko dubu daya yamun tsada" shagwab'e fuska tayi

"Allah nifa na tsani ake zagarmun hancina, kumama kaima kasan kallo d'aya za'ayi mana asan mafika kyau banda tsawon hanci ma menene kake taqama dashi" adaidai lokacin dasuka sauka harabar da CMD kurun aka tanadarwa dan ajiye motar sa

"Kyaji dashi dai,bansan sanda kika quramun ido ba har kika gano inada tsawon hanci nifa banson kallo"  yafad'a yanata faman qyalqyala dariya sosai ita d'inma dariya tayi suka bude mab'allan motar atare suka fito suna kwasar dariya....mutuwar tsaye Dr. Hisham yae yana mamakin ganin su a tare kuma a mota d'aya me hakan yake nufi? Inama Nafeesah tasan CMD da har zasuzo office confortable a mota d'aya bama wannan ba ji yanda suke tiqar dariya kamar sunyi shekaru goma da sanin juna!!!!! Da qyar ya saisai ta nutsuwarsa ya gayarda CMD tunda yake basuda nisa da juna ya kama gabansa.....ita kuwa ko ajikinta tamai godiya tabi bayan oganta tana sauri!!!

  A office taje ta sameshi  take mai godiyar saqon jiya
"Menene had'inki da CMD da zaki shigo motarshi zuwa office ke ina taki motar? Kuma bakya gudun zagi acikin asibiti ace wani abinne a tsakaninku,kallo tuhuma ta masa

" Abinda yake tsakanina dashi abune wanda ni kad'ai ya shafa gaskia be shafe kaba,sannan zancen zagi a i kullum se an sakemu bama gudunshi sam, karka damu" shiru yae be qara magana ba amma gaba daya har aka tashi office jikinshi a mace yake yama kasa ya tsare seyaga barinta asibitin ilai kuwa tare da CMD suka fita!!!! Wannan abin ya tsaya masa arai yarasa dalili, yau kam har zuhran sa seda ta gano yana cikin samu.

Mom Nu'aiym

Vote plss.

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now