page 17

5.9K 490 60
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

                    17

Bayan ta tsahirta kukan ta kalleahi cikeda kasala tace

"Yaa safwan zan shiga ciki kayi haquri, labarin Mqrigayiya ya d'agan hankali matuqa wlhy" riqo hannunta yae

"Pretty plss karki saka damuwa a ranki idan kikace haka zakiyi ya kikeso nida na santa nayi, take er uwata kumafa Allah kukan nan dakike har zuciyana nakejin zafinsa senakeji tamkar na zauna nima nayita kuka" murmushi ta qaqalo na qarfin,ta shagwab'e fuska lokaci d'aya ta zare hannunta a nashi

"To kuma ni yunwa nakeji zanje naci abinci" yanda tai magana kurin ya isheshi farin ciki

"Muje 10-10 na siya miki small chops kisha ice cream a havillah kusa dasune nan El-sudais road ba nisa" murmushi tae
."Daka barni tuwo na sanya akamun da miyan kuka, niya wadatar dani" sakar mata lallausan murmushi yae 

"Nifa banasan yanga yarinya  kuma Allah idan kikai qaton tunbi ba ruwana,wani wai tuwon miyan kuka sekaje a qauye" murmushi itama tae bata qarayin magana ba yaja suka tafi.....

Takaicine ya sanya hisham dukan staring motarsa da qarfi yace

"Jarababbe me san matan tsiya idanshi idan ganin mata wlhy Bazan bari ya shigewa Nafeesah ba ze rud'eta da kud'i mugun banza" nikuwa nace Allah sarki my Hisham....

   Washe gari koda taje zatabar wannan department zuwa wani unit daban na yara wannan ne ya sanya taji sauqi da dad'i a ranta koba komai  tasani cewar zata rage jin abinda takeji gameda Hisham sabida ta rabu dashi kenan,kuma inshaa Alllah bazata d'auki b'nagaren matan ba idan ta kammala  bautar qasar dazasu fara nanda watanni biyu sun gama cike mobalization form d'insh tuni.

*Bayan kwana biyu*

Yau ya kasance hutune ga Nafeesah bata zuwa gurin aiki, tana zaune a parlor itada shuraim tana duba masa Assighment d'insa da aka bashi daga school zuhrah ta shigo gidan kanta tsaye har cikin parlor da fara'a Nafeesah ta tarbeta ita d'inma kadaran kadahan ba laifi bata wani nuna damuwar taba bayan en gaishe daya kwana biyu zuhrah ta ture d'ankwalin kanta yazo har goshi tace

"Dama Daddy ne akace nanda sati biyu ze dawo shine nazo in miki gargad'i da karki kuskura kice zaki shiga tsakanin uwata da ubana sabida ni nan dakika ganni bazn saurara miki ba idan hakan tafaru, idan yazo zamu sanar masa kece kika zab'i dawowa nan gidan dan kanki kika kuma qwashe shuraim kince kin isarwa kanki, kema kuma haka zakice masa idan yazo d'in sabida gudun shigarki matsala damu baki d'aya, na rantse miki da Allah idan yadawo kuma  kikace mommy ce ta koreki keda mune wulaqantaki zamui" mamakin zuhra pheey keyi lokaci d'aya Hawaye ya soma zarya a Idanta,murya na rawa tace

"Zuhrah Nafeesanki ce fa? Ni kikewa haka zuhra? Kin mantani mena miki waye yake san shiga tsakanina dakene er uwata? Keda mommy kun sauya mun banmuku komai ba,dan Allah zuhrah ki gane gaskia ki dawo hanya, wlhy nime qaunar kice har abada"

Tsaki taja ta wurga mata harara

"Dakika gama so ki cinyemun mijina? Dakike so ki auren mijina munafuka, dakika rasa wanda kike sha'awa se mijina, wlhy da kunnena najiyoki kina adu'a Allah yacire mkki sha'awar sa banza muguwa butulu, wlhy keda mijina har abada gwara gawarki da inganki a d'akin mijina, kuma ke d'in nan ba tawa bace karki qara ambatarmun zamanki wata tawa jahila kawai dabatasan halacci ba dangin mayu shisa zuri'ar ku ke gudunku" kasa cewa da ita komai pheey tayi se sharar qwalla datakeyi a haka harta gama ta fice pheey batai magana ba.

*Bayan sati biyu*
Shaquwa me tsanani ta shige tsakanin  pheey da Safwan gartakai tayi sakewar dasuke wasa dashi suna dariya kamar cousines abokan wasa. Yauma kamar kullum waya sukeyi tana a kwance aka shigo cewar daddy yana kiranta acan gidan nasu zuhra alamun ya diro kenan sallama tamasa taje gidan a zaune ta tarar da kowa daddy bayan sun gaisa yace

"Nafeesah ki sani dake da duk wanda ke zaune anan nasan halin kowa, inaso ki dubi girman Allah karkimun qarya ki sanarmun meya faru kika bar nan gidan?" D'agowa tayi ta kalli mommh sannan ta mayarda kanta qasa batai magana ba ya qara cewa

"Allah nace miki Napheesa karki tsoron kowa se shi kawai, babu me ikon cuta miki arayuwa  seda yardar shi kumashi ba azzalumun sarki bane" gyaran zamanta ta kwashe komai game da yanda abin ya faru ta gayamai har zancen tana sha'awar mijin na zuhra da komai....jinjina kanshi yae yana me mamakin hauka irinta mata seacan yace

"Lallai Hajiya kin bani mamaki na zata kin sauya halayenki tuni ai ban zata haka kikeba har yanzu, babh wanda zanwa fad'a acikin ku amma lallai ne  na baku hukunci daidai da laifin ku,ku tashi ku bani wuri banda ke Nafeesah" sumsum har mommy sukai waje ya kalli Napheesa yace

"Nafee kin yarda ni mahaifinki ne zan iya yanke kowane irin hukunci akanki kuma kiyi biyayyah?" D'aga masa kai tayi alamar hakane yaci gaba

"To dukda nasan cewar dai zawara ita keda hukuncin zab'arwa kanta kijin aure amma dukda haka duba da yanayin da kike cki ina ganin cewar zanniya zabar miki wanda ya dace da rayuwar ki sabida haka na baki umarnin auren kijin zuhrah hisham kuma babu fashi bazanyi magana biyu ba, nine da kaina zanje in masa magana nakuma san bazeqi ba" qirjintane ya doka lokaci d'aya taji zufa yana tsatsafo mata haka murya na rawa ta furta

"Daddy dan Allah kai hakuri kazab'amun koma waye amma banda mijin zuhrah dan Allah" d'aga mata hannu yae sannan yace

"Napheesa bazan sauya hukuncina ba kozaki kwana anan ki tafi kawai kinji ba" jiki ba qwari ta miqe ta fice hankalinta duk a tace.

Koda ya kira Hisham yamai maganar kasa yi masa musu yae yanaso ya furta kalmar No amma bakinsa kawai keson furta kalmar sabida zuciyarsa taqi akinta da hakan, yayinda abubuwan dake kai tsaqon baqin ciki ko akasin hakan su kasa kai masa baqin ciki se farin cikin wannan maganar benasan ya furta kalmar amincewa da hakan ba tare da yin godiya me yawa!!!!! Inda daddy ya tsaida ranar biki wani watan nanda sati uku!!!!

Mom Nu'aiym

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now