11-12

1.8K 145 6
                                    

Da sauri umma ta riqota ta fada jikinta cikin matsinancin hali
suma kansu likitocin a rude suke.musamman bakori tunda ya dora hannunsa a qirjinta ya soma girgixa kansa
umma na kuka tana fadin tafowarku batamin rana ba domin kunqara rikita alamarin kun janyomin tashin hankali burina a yanxu fulani tatashi
Dr. Amir yace umma ai haka shiyafi dacewa akan idan taji gobe bakisan yanda xata kasance ba
umma batace komai ba tasoma matsar hawaye tana kallon fulani dake kwance
bakori ya fita jim kadan sai gashi dauke da allurai har kusan kala hudu
cikin lokaci qanqani yayi matasu
ya dubi umma muryarsa a tausashe
yace ki kwantarda hankalinki umma fulani xata sami sauqi idan ta farfado damuwa baxata mata yawa ba sai dai baxata qara samun qarfin xuciyaba
duk wani abu mai xafi karta sake cinsa hakama mai sanyi sosai kamar ruwa drinks ko qanqara ta daina sha
adaina barinta tana kadaicewa ita kadai saboda gujewa tunanin da xatayi
ynxu xuciyarta takai wani limit mai tsananin gske wanda Allah kadaine xai iya fitarda ita

inaso idan ta tashi duk wata hanya da xata sanyata farinciki amatashi amantarda ita suleman da hafsat
12
umma tace tor wannan aman jinin fa ?
yace banaso.na gayamiki komai akansa saboda hankalinki xai tashi
cikin faduwar gaba da tsananin rudani
tace dan me xaka boye cutar ya'ta gareni

dan Allah kagayamin
yasani baxai iya gayamata ba dan ita kanta umman tana gab da kamuwa da hawanjini
yace umma wannan aman da tasoma lokaci lokaci xata riqa tari mai jini wanda xai xame mata jiki a ynxu kuma matsalace babba sannan idan ta sake wannan aman na jini(ya girgixa kansa fuskarsa da alamar tausayawa kwallah na taru idanunsa)banajin fulani xata cigaba da rayuwa hawayen dayake maqalewa suka xubo masa
itama umman tasoma hawaye ba kakkautawa
yace anjima xn shigo na dubata insha Allah xata sami sauqi
suka juya suka fice gabaki dayansu

LABARI NAWhere stories live. Discover now