26

1.4K 113 1
                                    

Washe gari bayan tagama hada brkfst dinta ta
sanarda mahnoor xataje asibiti
cikin mintina qalilan tagama shirinta ta fice cikin
sabuwar motarta da abbanta ya siyamata
lokacin da take qoqarin shiga office din bakori sai
tasoma jin hayaniya kamar ana fadane
tana qoqarin shiga taga anbude qofar da qarfi
hafsat taga ta fito tana kuka ta fice hakan yasa
ta fasa shiga musamman datajiyo muryar
suleman aciki
kai tsaye tajuya ta nufi nata office din
bayan ta xauna
masinjanta ya matso
ahankali yake mgn
yace ranki shi dade kinga amanarki ta soma fita
daga dr.hafsat da dr.suleman tun daxu suke fada
hrda aibata junansu

ta dan yatsina
fuskarta kafin tace patient din yau suna da yawa ne
a'ah amma dai akwai wani babban mutum da
xaki fara dubawa shugabane a efcc
dam gabanta ya fadi indai ba marhoom bane
tace inga file dinsa
jikinsa na rawa ya ciro ya miqa mata
ta tsurawa sunan ido tabbas marhoom ne, to
meke damunsa
duk sai ta rude wanda yaso masinjanta ya
fuskanceta
yace dr. lfy kuwa
ta girgixa kanta cike da rudani tabbas idan
marhoom yasan itace xata dubasa baxai tsayaba
hassalima xai wulaqanta kamar yanda yasaba
tace baba wannan case baxaka kaiwa dr.bakori
ba ya dubasa bane
yace ai inajin matsalarsa ba akan fata bace kece
likitar da xaki dubashi tunda kikaga file dinsa
anan
tayi shiru kafin dabara ta fado mata
ta gyara rolling din gyalenta yanda fuskarta
baxata fito sosai ba ta sanya space dinta dark ta
boye idanuwanta
tace baba kace ya shigo
ya fita cike da mamakin abinda yagani daga
gareta baijima da fitaba marhoom ya shigo shima
fuskarsa a murtuqe idanunsa boye cikin dark
space kamar nata
tunda yaji ance mace xata dubashi ya soma hade
rai danma yasan ba fulani bace ya barota gida
da baxai shigo ba yaji wannan ankirata da
dr.Aisha
kallo daya yayi mata yaji gabansa ya fadi
axuciyarsa yana qiyasta kyawunta dogon
hancinta da bakinta kadai daya gani sun birgeshi
ya jinjina wa qaramar yarinyar
ahankali ya sami wuri ya xauna a inda yake
fuskantarta
da kyar ta tattaro nutsuwarta da hankalinta xuwa
garesa cikin kakkausar murya
tace sannu ko
ya amsa fuskarsa ba yabo ba fallasa
gabanta na faduwa
tace can i help u?
ya gyada kansa batare da yayi mgn ba
ita kuma duk ta qosa taji matsalarsa kuma tana
fargabar ya gano ta
shiru harna wani lokaci kafin yace x too late, nayi
jiranki tun daxu baki xoba gashi ynxu lokacin
aikina ya kusa i can't waste my tym
jikinta na rawa
tace amma lafiyarka ai tafi office ko kuma fuka
duka baxaka wuce minti goma anan ba
ya dan dubeta bayan ya xare madubin idanunsa
yace am sorry 2 say baxan iya qara minti biyu
anan ba , gobe xn shigo idan kin shigo da wuri
xaki iya dubani inkuma ban samu ba agobe xn
cnxa asibiti
cikin rawar murya ta amsa xa xa xama kasamu
insha Allah
ya juya batare da yayi mgn ba yafice tabi
bayansa da kallo
kusan minti goma tayi kafin tadawo hayyacinta
hartagama duba patient dinta bata cikin
hankalinta tana son sanin meke damunsa wanda
xuciyarta ta takurata akan wannan
da yamma ta isa gida inda ta riski wani tashin
hankali
mahnoor k sanarda ita wai marhoom yace karta
sake fita aiki sai da ixininsa idan kuma ta sake ta
fita xata xabi daya ko aure ko aikinta
ranar kuka tayi sosai har idanunta suka kumbura
itama mahnoor ganin irin kukan da fulani k yi
yatada hankalinta har itama take tayata kukan
da dare ta kira bakori ta sanardashi xata dauki
hutun 2wks saboda wata yar matsala bai
takurataba yabata hutun itakuma tayi hakane
saboda tanada yaqinin cewa kafin lokacin xata
roqesa har ya sassauto yabarta takoma aikinta
a bangaren sa tun bayan dawowarsa gida bashida
wani tunani sai na dr.Aisha ta shiga xuciyarsa
lokaci daya har yakejin dama itace maryam tace
ya aura ba wannan ficakar yarinyar ba fulani
daren kasa barci yayi sai faman juyi yana
tunaninta xuciyarsa ta amsa da son dr.Aisha take
kuma shima ya yarda da hakan
washe gari Allah Allah yake qarfe tara tayi yabar
gidan tunma takwas yafita lokacin fulani na bakin
window tana kallonsa duk da batasan inda
xashiba amma tayi mamakin fitarsada wuri haka
tasaki labulen window bayan ta xauna abakin
gadonta tasoma wani sabon kuka
shi kuma tunda ya isa asibitin yake faman jiranta
har qarfe goma ba ita ba alamarta
hankalinsa yayi matuqar tashi lokacin dayaji
masinjanta na sanardashi yanajin baxata fitoba
tunda takai har wannan lokacin bata shigoba qila
sai gobe
jikinsa a sanyaye yafito daga asibitin ya nufi gida
shigowarsa falon yayi dai dai da saukowar fulani
daga stairs kallo daya yayi mata yaji ransa ya
qara baci fiye da yanda ya shigo gidan
yaja guntun tsaki bayan ya dauke dubansa gareta
ya nufi sashensa..

LABARI NAWhere stories live. Discover now