Matuqar sanyin da ake ya tilasta mata sanya suwaita baqa,
sanye take da dogon wando baqi na jeans
hular sanyinma baqace ta rufe kanta da shi yayin da jelar gashinta ya tsaya dai dai rabin bayanta
tana tsaye bakin window tana kallon fararen tsuntsayen dake saman bishiya tana matuqar sonsu suna birgeta
ta lumshe idanuwanta tana son tuna wani lokaci da itada marhoom sun fito wanka sun gama shirye shiryensu suka kwanta
marhoom ya xauna ya kunna fitila yana kallonta
taja bargo ta gyara kwanciyarta
ya janye bargon
ta kalleshi tana murmushi
me kuma akayine?
ya tallafota
xo nan kibani labari wai ke baki fara ko dan irin amai da tashin xuciyar nan da mata keyi bane
tace akan mexnyisu bayan lfyta qalau
yace kina nufin wai ke hr ynxu bakida cikine
ta kyalkyale da dariya
me kakecine na baka na xuba kabari akwai lokaci yana xuwa kasan komai da lokacinsa kuma sai Allah ya nufemu da cikin ko?
ya gyada kansa jikinsa a sanyaye
yace gskyne kinsan inason yara da yawa
inason haihuwa sosai
maryam bata gayamiki haka ba
tayi shiru tana kallonsa
ya janyota xuwa jikinsa
.yace dan Allah karki barni Aisha kibani yara ina sonsu da yawa sune ginshiqin rayuwata koda yaro dayane kibani idan kikamin haka kin gamamin komai a rayuwata
ta kwantar da kanta a qirjinsa
tace karka damu Allah xai bamu mu roqesa yabamu masu albarka
ya sumbaceta suka kwanta
ta goge hawayen dake xubo mata
batasan ta shaqu da marhoom ba sai ynxu
batasan tana masa wani mahaukacin soba sai ynxu har gani take soyayyar marga garesa qaryane
ba macen da xata xauna da marhoom bataji tana sonsa ba ya iya tattalin mace da riritata gashida biyewa duk shagwabar mace kuma yanada kula sosai yakan danne damuwarsa yafifita ta matarsa tana ganin da wannan marhoom yaci galabar xuciyarta hrtake sonsa haka
tana cikin haka umma ta shigo cikin wani irin yanayi
tace fulani kixo muje jidda ynxu hadixa ta kirani jikin anwar yatashi suna jidda (mijin qanwar umma)
ta dan yatsina fuskarta
tor umma sai naje ne
tace eh sai kinje, maxa kifito muje dan baxan iya barinki anan ba tunda abbanki bayana
ta gyada kanta kawai ta juya tana cnxa kayan jikinta....
YOU ARE READING
LABARI NA
Historical FictionA Heart Touching Story Of a Young Girl Dr. Fulani Gafai..... (true life story)