36

1.4K 99 2
                                    

Yatsina fuskarsa yayi hade da yarfe hannayensa ya nufi gadon sa ya xauna hade da janyo laptop dinsa ya buda
tana ganin haka ta koma bakin qofar dakin ta xauna dirshan xuciyarta sai xafi take mata ga jiri dake damunta wanda yunwace ta haddasa mata hakan
a fakaice yake kallonta hankalinsa na kanta ganin ta soma yunqurin amai yasa ya.maida dubansa gareta a yatsine yake kallonta tana amai
ya sauko bayan yaja guntun tsaki yabi ta gefenta ya wuce wannan sai kace qaxama tarasa wajen amai sai a dakinsa mtseww yaja dogon tsaki bayan ya iso dakin mai aikin nasu
ya buga qofar dakin kusan minti biyar aka bude dakin ya dubeta a raunane
yace kije dakina akwai amai ki kwashe a taqaice ki gyara dakin duka gabaki daya ki hanxarta pls
ta fito jikinta na rawa ta nufi sashensa
ya soma safa da marwa a falon hannuwansa sarqe a bayansa
yasani kulawarta na hannunsa duk abinda yasameta laifinsa ne kuma dole a tuhumesa
abinda ya fahimta daga bayanin da bakori yayi masa fulani na buqatar taimako sosai kuma abar tausayawace musamman idan ya tuna ba laifinta bane bai kamata ya doramata karan tsana ba
shi bawai baya sonta bane ya soma sonta lokacin da yaganta a dr.aisha shidai kawai rainine bayaso kuma bayason girmansa ya fadi.......ya tsaida idanuwansa dai dai lokacin da mai aikin khairiya k fitowa
kanta a sunkuye
tace nagama duka sai dai da alama tana wahala da ciwon
yace wannan ba hurumin ki bane aikinki daban
tace tuba nake Allah yabaka haquri ta juya xuwa dakinta
yayi tsaye na tsawon mintina yana saqa da warwara shi baisan ma ynda xaiyi da itaba can ya yatsina fuskarsa yanufi kitchen
cikin qalilan mintuna ya hada mata tea mai xafi ya nufi dakin ya sameta kwance nan qasa

sai ya tsinci kansa da son taimakamata ya xaunar da ita yana fuskantar
yace waya gayamiki ana fushi da yunwa idan kina fushi dani sai akace kiyi fushida abinci ynxu baga abinda kika janyowa kanki ba
ta soma share hawayenta batare da tayi.mgn ba ya miqa mata kofin shayin
yace karbi kisha ko kadan ne
ta girgixa kanta tan hawaye
ya buga mata tsawa mai firgitarwa
yace ki karba nace
bashiri jikinta na rawa ta karba ta kafa kai sai data shanye sannan ta ajiye kofin tana maida numfashi
tausayinta yasa ya janyota xuwa jikinsa sai ya tsinci kansa da rarrashinta abinda nayi matuqar bata mamaki tasani koma me xai mata baxata soshiba
ahankali ta xame jikinta daga nasa jikinta a sanyaye ya tashi ya riqa hannuta yakaita toilet
fuskarsa ba yabo ba fallasa
yace kije kiyi wanka
ya dawo ya xauna cike da tunani iri iri yana kallo ta fito ta lullube kanta da qaton towel
bata wani dauki lokaciba ta shirya cikin kayan barci masu kauri da tsantsi tayi tsaye dan bata san inda xata kwantaba shima ya lura da haka
yayi mata nuni a saman gado
cike da mamaki take kallonsa alamar baxata iyaba
ya xare mata ido cikin tsawa
yace ko bakya jine
jikinta na rawa ta hau gadon can nesa dashi ta kwanta
ya nuna mata kusa dashi nan xaki matso koni mugun abune da kike guduna
aranta tace ai bakada maraba da mugun abu...ta matso xuwa inda yace ta qudundune cikin bargo tana jinsa ya tashi ya nufi toilet da alama shima wankan xaiyi
jin fitowarsa yasa ta lumshe idanuwanta kamar mai barci tana jinsa ya gam shirinsa ya hau gadon tare da yaye bargon data lulluba dashi
kallonta yake yanaso yaga wani aibu nata daya hana masa kulata amma yakasa gano komai
shirun data jine yabata tabbacin kallonta ya keyi ta tsargu saura kadanta bude idanuwanta amma tana jin tsoro
sai kawai tayi saurin juyawa kamar acikin barci sai ji tayi ya janyota ya hadata da jikinsa
nan fa jikinta na soma rawa sai tafara qoqarin xame jikinta ya riqeta gam
yace ki kwantarda hankalinki ba abinda xn miki
ta kasa samun nutsuwa sai da taga yaja bargo ya lullubesu cikin qalilan mintuna ta soma jin saukar numfashin sa alamar yayi barci tasaki ajiyar xuciya hade da lumshe nata idanuwa.
Washe gari koda ta tashi baya dakin da sauri ta diro daga saman gadon ta nufi toilet arwallah tayi ta fito
tana kan salaya yashigo sai dai bai wani jimawa ba ya fita.

LABARI NAWhere stories live. Discover now