16-20

2.4K 158 4
                                    

Tun bayan fitowarta gidan yau gabanta k faduwa sai ta la'anta dacewa qila dan xataga maqiyanta ne
ganin damuwa nason yimata yawa yasanya tasa waqa a motarta tanabin waqar ahankali dai dai lokacin da ta iso check point tayi mamakin go slow yanda yayi yawa ayau
kusan minti biyar baa sakesu ba taja dogon tsaki bayan ta juyo da fuskarta wani gefe
carab suka hada ido wanda lokaci daya xukatansu na buga
subhanallah ta fada cikin tsoro bayan tayi saurin dauke duban taga saurayin dai dai lokacin aka basu hannu
da sauri tabar wurin tana hawa babban titi ta soma gudu sosai kamar xata tashi sama
tana isowa asibitin agaggauce ta fito ta nufi cikin asibitin kai tsaye office din dr.bakori ta nufa tasanar dashi ta shigo kafin taje nata office ta ajiye kayanta
masinjanta sai rawar jiki yake uwargidansa taji sauqi tadawo duk inda tayi yana bayanta
ward round tayi tana duba patient dinta databari wasu duk tasamu an sallamesu wasu kuma sai ace mata sun mutu
cike da jimami ta ke girgixa kanta dayawa majinyata da nurses sunji dadin dawowarta
kasancewarta mai sanyin hali da faraa musamman akan patient dinta da kuma staff dindake qasanta duk da ta girmesu takan basu girmansu yanda ya dace shiyasa suke damuwa da ita suke nuna kulawarsu akanta
a gajiye tadawo office dinta ta xauna tasoma duba files dinda aka shigo mata da su
masinjan ya shigo
ranki shi dade kinada baqo a waje
ta maimaita baqo kuma baba
ya gyada kansa
tace ba patient bane
yace banga alamaba amma yace ynxu da safe kuka hadu ko a check point
dam gabanta na fadi tuna saurayin data gani sai taji hankalinta naneman fita daga jikinta
tace olryt tor kashigo dashi
masinja yafita yakirashi

tayi hanxarin sauya gilashin idonta taga fari xuwa prada mai duhu tacire mai hasken
gabaki daya lokaci daya bayan shigowarsa office dinta ya dauki wani qamshi mai sanyin dadi
lokacin data xuba mishi idanuwanta taganshi saurayine qarshen gaye duk ilahirin jikinta ya mutu yana rawa cikin daburcewa ba kyaun shi ya raxanataba tsabar kwarjininsa da kamalarsa da cikar xatinsa na raxanata
rana ta farko datasoma jin bugun xuciyarta da tashin hankali dataci karo da wannan saurayin dan ko suleman bata taba tsintar kanta acikin irin wannan yanayinba

17

har yaxauna a kujerar dake fuskantarta bata cikin nutsuwarta
inda ta godewa Allah na dabarar sanya darkspace dinda tayi da tuni ya fahimci weakness dinta
gaisuwar da yayi mata yasa tayi saurin dawowa hayyacinta tadan yatsina fuskarta kafin ta amsa bayan ta qara gyara gilashinta
shi kuma tsananin mamakin wannan yar mitsila yarinya amma cikakkiyar likitace gsky ya jinjinawa iyayenta he is exteremely impressed!
tun dayaganta wajen check point yaji yakasa samun nutsuwa ajikinsa yarinyar tatafi da imaninsa gata fara kyakkyawa kuma qaramar yarinya mai matsakaicin jiki
ya dawo daga curfin tunanin da yake bayan tabigi teburin gabansa
tace malam kayi shiru meke tafe dakaine
kai tsaye batare da fargabar komai ba cikin kakkausar murya
yace UMAR FARUK is in luv...........pls doctor save a lyf
kyam ta xuba mishi idanuwanta kafin daga bisani ta daure fuskarta tamau bayan ta tuna yaudarar suleman
tace idan wannan ne yaxo dakai office dina pls get out ta fada tana nuna masa qofar fita
ya boye mamakinsa
dan baiga laifinta dan ta wulakanta mai sontaba saboda tatara abubuwa da yawa daxata iya dogara dasu
ya tashi tsaye idanunsa akanta
Aisha!!!!!!!!! ta juyo da kallonta xuwa gareshi a raxane ko ina yasan sunanta
seriously ina sonki banxo dan na yaudareki ba nabaki kwana biyu rak kiyi tunani akaina da xuciya daya naxo gareki kuma xnxo har gida na ji sakamako ya juya ya fice ta bishi da ido cike da mamaki

ko ina yasan gidansu da xaije
tayi saurin kawar da tunani tacire space din fuskarta taja gauron numfashi bata so amaimaita abin farko shiyasa take son ciresa daga tunaninta kafin yakai ga xuciyarta
sallamar maryam ta katse mata tunani
ta tarbeta fuskarta a sake
sun dan jima suna gaisawa kafin tace maryam wace mgn kikeson muyi wane taimakone xn miki
maryam tayi shiru jikinta a sanyaye tace dr. xn baki LABARI NA
tace meyasa xaki bani lbrn ki bayan aikina bai danganci hakaba
tace inajin labari na shine xai taimaka miki ga taimakon da xaki min
fulani ta gyada kanta bayan ta kishingida tace shikenan maryam go ahead inajinki
nan take maryam ta xaiyana mata komai na rayuwarta da matsalar datake ciki tana kuka
itama fulani cike da tausayamata take hawaye
tace maryam kusan matsalar mu daya dake amma ni baxan baki LABARI NA ba
meyasa ? maryam ta tambaya tana kallonta
tace saboda baxai amfaneki da komai ba kuma baxaki taimakamin da komai ba
maryam tace taimakon me kikeso fulani
kai tsaye tace XUCIYA itakadaice matsalata a rayuwata sai ta soma kuka sosai
nan take hankalin maryam na tashi tace kidaure kigayamin ko kadan ne daga cikin lbrnki
batare da gardamaba fulani ta gayamata
maryam taja numfashi tace amma fu......ta katseta tace kibarshi muyi abinda keda muhimmanci garemu karki damu da matacciyar xuciyata (sunan littafina na gaba)
maryam tace yanda marhoom yaci burin haihuwa akai na shiyasa nakeson ki taimakamin
tace dame fa
tace inaso kibani takardar shaida inada ciki xnjewa marhoom amatsayin mai ciki idan lokacin girmansa yayi xn riqa boye kaina garesa ina ciko musamman ma tunda baya xama a gari baxai gane ba
tace tor idan lokacin haihuwar nayi kice dashi me tunda babu
maryam tayi jim kagin tace xamuxo tare dashi nan asibiti haihuwa saiki karbi labour dina sai kisamamin mataccen jinjiri kibashi a xuwan na haihu yaron baixo da rai bane
ido fulani taxaro tana kallonta kafin tace gsky baxan iya wannan ba

LABARI NAWhere stories live. Discover now