42

1.5K 121 4
                                    

Dan xamansu ta fahimci kowaye marhoom
yanda take kallonsa da xafi ashe ba haka bane ko
farkon qiyayyar daya nuna mata saboda maryam
ne
abinda ta fahimta garesa mutum ne mai sauqin
kai mai son anuna masa kulawa sai dai ta lura
yafita miskilanci bai fiye surutuba kamar da dama
mahnoor ta taba gayamata miskiline batasan
meya cnxa xuciyarsa yadawo mai xafi ba
duk da bawani sakin jiki tayi dashi sosai ba tana
samun kulawarsa tana kula dashi kamar yanda
momy tayi mata nasifa amma har lokacin takasa
ganewa xuciyarta tana son marhoom ko bata
sonsa koda yaushe acikin jiran xuwan ummanta
take taxo taje da ita saboda tanason aikinta
fiyeda xamanta a sudan
akai akai mahnoor na xuwa yimata yini tana
tayata xaman kadaici kafin marhoom yadawo

koda ta tashi yau
wata iri takejin kanta sukuku kasancewar wata
biyun sun cika tayi waya da ummanta a gobe
xataxo sudan ta koma da ita nigeria
duk wani movement dinta akan idanunsa ya rasa
meke damunta yaganta tayi sanyi kamar mai
dauke da damuwa
ya riqo hannunta lokacin da ta kawo masa
wayarsa ya xaunar da ita a qafafunsa
yace meke damunki ko bakida lfy ne naganki
wata iri yau ya fada yana taba jikinta ko yayi xafi
tayi shiru ta sunkuyarda kanta qasa nan da nan
kwallah na soma xubo mata
ya rungumota jikinsa a sanyaye
yace an wuce wurin ynxu fa fulani inaji kindade
rabon danaga kin xubar da hawayenki kigayamin
konamiki wani abun ne daban
tayi saurin girgixa kanta tana hawaye
yace tor menene
tayi shiru
ya sa hannu ya dago fuskarta tana fuskantarta
yace ko hr ynxu bakya so nane?
tmbyr taxo mata a baxata ta dubesa fuskarta da
mamaki idan ma tace bata sonsa ai shima bai
taba furta mata kalmar so ba sannan ayanda tayi
sabo dashi ynxu wani abu ne mai nauyi ta furta
kalmar qi agaresa
hakan yasa tayi saurin girgixa kanta
a'a fa fulani i knw qiyayyata ce kawai kesaki
xubar da hawaye bayan shi bansan namiki wani
laifin ba daxai saki kuka
amma dan adam ajixi ne idan nayi ne kiyi haquri
kibar kukan bana so
ta fashe da kuka ta rungumosa shima ya
rungumeta cike da tunanin dalilin wannan kukan
nata
batasan meyasa ayanxu bata san rabuwa dashiba
wanda yaxame mata dole ta rabu dashi saboda
tana son aikinta
tana son ta nuna masa kamar ynda yasha gaya
mata ya tsaneta itama ta nuna masa tata ta
hanyar rabuwa dashi wanda ummanta kadai xata
iya taimaka mata da wannan
ta qara shigewa jikinsa tana shaqar qamshin
jikinsa tasani akwai abubuwa da yawa daxatayi
kewa daga garesa amma duk xata jure ta
mantasu idan ta koma aikinta...
da dare sai faman juyi take ta kasa samun
nutsuwa ballantana tayi barci hr ynxu batasan
hukuncin da xuciyarta na yanke mata ba akan
marhoom
lokaci lokaci take kallonsa yadade da yin barci sai
saukar numfashin sa kawai takeji a hankali
ta hada hannunta da nasa ta saqale cikin wani
irin yanayi mai wuyar fassaruwa
da safe duk abinda takeyi batada wani kuxari
haka ya janye tulin takardun dake gabansa
ya.buga tagumi yana binta da kallo
sai ta tsargu da kallon ta dubesa fuskarta dauke
da murmushin dabai kai xuciya ba
tace duk wannan kallon na menene?
ya dauke taguminsa yana yatsina fuskarsa
yace nima ban sani ba
tayi murmushi tashige dakinta
suna tare a falo da rana kiran ummanta ya shigo
sai da gabanta ya fadi cikin rawar jiki ta dauki
wayar
tace fulani mun iso ke kadai nake jira
tace tor ta tsinke wayar cike da tashin hankali dai
dai lokacin wayar marhoom tasoma qara
ganin kiran momy ne ya daga da sauri
tace marhoom kuxo ynxu kunyi baqi daga nigeria
yace shikenan gamu xuwa ya tsinke wayar
ya tashi yana fadin kinji momy tace munada baqi
daga nigeria ki dauko hijabinki muje bansan ko su
waye bane
ta tashi jikinta a sanyaye ta nufi dakinta dama ta
gama hada komai jiran umman kawai take
yana harabar gida yaga ta fito da qaramar trolley
ya kalleta da mamaki
yace ina xakije da trolley kuma
tace saqon sune xn basu ne
yace au daman kinsan da xuwansu kinsan kosu
waye sukaxo kenan
ta gyada kanta batare da tayi mgn ba ya amshi
trolley din ya sanya a booth kafin su shiga motar
suka bar gidan

LABARI NAWhere stories live. Discover now