40

1.4K 104 5
                                    

Aisha kema kiyi haquri kijure duk wani bacin rai daga garesa watarana sai labari dama haka aure ya qunsa xomu xauna xomu saba dole sai da haquri
xan gayamiki abubuwa kadan kamar yanda nagayawa marhoom
1. na farko shine kiji tsoron Allah duk abinda xakiyi ga xaman takewar aurenki to kiji tsoron Allah
2.ki xama kamar baiwa ga mijinki sai shima yaxama kamar bawa agareki
3.kada ki nisance shi domin nisanta dashi xai iyasa ya mantaki yaxamo baya damuwa dake
4.ki kiyaye masa lokacin cin abincinsa da barcinsa domin yunwa tana hassala mutum kuma gurbata masa barci xaisa ya fussata
5. kikiyaye masa gidansa dukiyarsa da danginsa domin sunada muhimmanci agaresa
6.ki girmamashi matuqa shima xai girmamaki fiyeda yadda kowa xai girmamaki
7.kada ki juya masa baya yayinda ya kusantoki
8.kada ki fiye naci da fushi alokutan da kike neman wani abu daga garesa tor lallai xai qosa dake
9.daga qarshe dan girman Allah kiyi haquri ki xamo shimfida ga mijinki xai xamo rumfa agareki har qarshen rayuwarki
Allah yayi maku albarka
kanta a qasa tana sharar hawaye momy ta daureta da maganganunda baxata iya juresuba musamman yanda xata kula da marhoom tunda batasonsa
amma xata kwatanta iyayinta tareda jurewa xuciyarta ta kula dashi kafin ummanta taxo ta raba auren
ta goge hawayen fuskar tana kallonta
tace nagode
momy tayi murmushi taja hannuntabta bude.mata motar ta shiga shima marhoom ya shiga
suna tsaye itada mahnoor suna daga masu hannu har suka fice daga gidan

Tunda suke tfy ba wanda ya tanka acikinsu kowane da saqe saqen xuciyarsa akan nasifar momy har suka iso gidan
batayi mamakin girman gidan da kyansaba idan ta tuna watake aure
da hannu ya nuna mata sashenta kafin ya juya ya nufi nasa
komai ya birgeta har axuciyarta taji dadi musamman tsarin falonta haka ta nufi dakinta duk abinda take buqata akwai a dakin
sai dai xuciyarta na cike da fargabar maciji har ynxu tsoron bai fita xuciyartaba shiyasa ta kasa xama ta fito main falo tayi xaune kawai
da dare dole tasanya ta nufi dakin tana dube dube tana tafe tana tsalle tsalle harta shigo dakin
caraf idanunta nakai akan gadonta wani abu tagani baqi
tasaki qara hade da juya wanda yayi dai dai da fitowarsa dakinsa jin ihunta
a hanxarce ya nufota
yana fadin menene
jikinta na rawa harta soma hawaye
tace maciji
maciji ya fada idanunsa a waje
ta gyada kai tana hawaye
har xaije ya kira mai gadi sai kuma ya juyo ya riqo hannunta suka nufi dakinta
yace a ina yake
da hannu ta nuna masa yana isa wurin sai yaga baqin dan kwalline na after dress mai yiwuwa ma ita ta yardashi nan amma ta tsorata
ya juyo yaga yanda ta qanqameshi ta rumtse idanuwanta tana hawaye sai yayi shiru kawai ya xubamata narkakkun idanuwansa yana kallonta..........

LABARI NAWhere stories live. Discover now