32

1.4K 112 1
                                    

Mahnoor tabishi da kallo har ya shige dakinsa kafin ta girgixa kanta cike da tausayawa itama tayi nata dakin....
Bayan magrib tana kwance take jiyo hayaniya a falo
ta sauko daga saman gado ta leqa ta qofar dakinta ko suwaye haka suka dameta da surutu
mahaifiyar maryam ce da yayarta halamcy (uwar masifa) tana tsaye taga mahnoor ta tunkaro dakinta da alama ita xataxo kira
ta juya ta koma bakin mirrow tayi tsaye hr mahnoor ta shigo
tace anty fulani kinga sun sake dawowa ko, wlhy basu da kirki ni bansan lokacin da maman maryam ta xama haka ba
fulani ta tabe baki bayan ta janyo dan qaramin gyalenta ta yafa
tace kixo muje mahnoor bana tsoronsu
tun fitowarta suka tsuramata idanu yanda suka xata ba haka suka gantaba axatonsu xasu sami wata babba macece sai suka sami akasarin haka domin fulani yarinyace a yanda suka gani
taku take ahankali yanayin saukowarta daga saman bene ya birgesu har ta qaraso cikin falon
nesa dasu ta xauna a kujerar dake fuskantarsu mahnoor na xaune akusa da ita cike da tsoron abinda xaije yabiyo baya
idanunta akansu ta gaidasu amma sun kasa amsawa illah idanu dasuka bita dashi ganin haka yasa ta dauke dubanta garesu tamaida hankalinta ga t.v tamkar ba'ayi ruwansu a wurin ba
halamcy tayi qarfin halin mgn cikin dakewa da daure fuska
tace munxo mgn akan yar uwarmu ne
sai alokacin fulani tamaida kallonta gareta ta xuba mata idanu cikin nuna wacce yar uwa?
halamcy ta amsa da yar'uwata kuma qanwata wadda kika kashe saboda k kirayu ki mallake mata miji daduk abinda ta mallaka
mahnoor ta langabar da kanta
tace anty halima dan Allah k......ta katseta
k rufamin baki munafuka nagane tuntuni kina bayanta kinmanta alherin maryam saboda kinsami wata banxa ko
sai alokacin fulani tayi mgn
tace idan kina mgnr banxa kece banxa kece kemanta alheri ba mahnoor ba
ta xaburo tana fadin kigayamin na sankine kona taba ganinki wane alheri kika tabamin
idan banmiki alheriba ai nayiwa qanwarki shiyasa nima ta sakamin da nata alherin

wane alheri kika mata meke dakene k wacece mekike taqama dashi
fulani batayi mgn ba ta kishingida da kujerara da take xaune hade da dora qafarta daya kan daya ta lumhe idanuwanta cike da takaici
halamcy tacigaba da fadin duk ynda xakiyi kisan yanda xakiyi kibamu xuciyar yar uwarmu ko ki biyamu kudin xuciyar kamar yanda mukafada da farko
ta ware idanuwanta akanta
tace banyi da maram xn biyata kudin xuciyaba kuma bata sanardani tanada yan'uwan dakeson kudi fiye da itaba
mmn maryam tace kada ki raina mana hankali bamuxo xonan dan jayayya ba munxo ne akan mgn daya ko xuciyar yar mu ko kudin xuciyar
fulani ta girgixa kanta tana fadin
ashe maryam ta siyarmin da xuciyartane ban sani ba......
mtsew halamcy taja dogon tsaki dai dai lokacin marhoom k saukowa daga bene ganinsa yasa mahnoor ta nufesa tana hawaye
tace yaya kagansu sun qara xuwa akan sai anty fulani tabasu xuciyar anty maryam
ya qaraso inda suke yana fadin mama naxata mun qare mgn dake kan wannan case ko
halamcy tayi caraf
tace ba ruwanka badan tana matarkaba xaku hadu ku cutarda maryam dan bata raye dama da hadin bakinka aka kashet........tas kakeji ya dauke fuskarta da mari
duk suka jiyo a tsorace suna kallonsa idanunsa sunyi jawur
fulani tatshi daga inda take xaune
tace menene na duka... wayace ka daketa ..taxo inda nike ba gurin kaba dan haka karka sake, ta maida kallonta garesu
tace kugayamin nawa xuciyar take inbiyaku saboda nafi qarfin wulakancinku akan matacciyar xuciyar yar'uwarku
karya kike ba matacciya bace takice matacciya marar amfani.....keeeee ya daka mata tsaya cike da bacin rai
baxa'a biyaba anqi abaku kudin maryam ai ba siyarda xuciyar tayi ba, k mama ban dauki likitocin dana masu aikin na kaikiki ba suka miki bayani tare da nuna miki takarda da maryam tasa hannu
a sanyaye tace an nunamin nagani kuma na gamsu halima ce tatakurani akan sai munxo
ya maida dubansa gareta yace halima xoki fice min daga gida munafuka
ta tunxure bakinta hade da daukar gyalenta da makullin mota ta juya tana kallon fulani
tace xamu hadu dakene dan baxan kyaleki kici bulus ba sai kin bada xuciyar kota qarfi da yaji ne ta juya tafice tana fadin ina jiranki a waje mama
ya girgixa kansa cike da takaci
yace mam kinfita hankali bai kamata kina biye mata a irin wadannan abin ba
tace nasani amma nima abin namin ciwo yanda maryam xatayi abu batare da saninmu ba ina tuna raina baci yake ta kyautarda xuciyarta ga wani bare
fulani ta tabe baki kawai
yace duk wannan yakau ynxu addua yakamata kumata yafi wannan tashin hankali da kuke saboda nida fulani bamai laifi nima maryam bata sanardani ba sai ranar aiki haka bata sanarda fulani ba sai da akamata dashen xuciyar aka gayamata
mama ta girgixa kanta tana hawaye
tace ba komai ta juya ta fice mahnoor tasaki ajiyar xuciya
ya juyo da kallonsa ga fulani itama shi take kallo kowane fuskarsa a tamke ba walwala kafin ya juya yabar falon itama tayi sashen ta cike da bacin rai.

LABARI NAWhere stories live. Discover now