44

1.2K 98 1
                                    

koda suka fito falon fulani na jikin umma tana
kuka sai abin yayi matuqar daure masu kai
momy tace fulani lfy ko kuma duk shagwaba ce
dan anga umma
umma tayi murmushi tana fadin ai shagwaba ta
qare tunda da ita xn koma gida
a firgice marhoom da momy suka kalli juna kafin
su maida hankalinsu ga umma cikin rashin sanin
inda mgnrta ta dosa
tacigaba da fadin
dama naxo xn tafi da fulani hrna tsawon wani
lokaci kafin na dawo da ita
meyasa ? marhoom ya tmby idanunsa akanta
cike da mamaki
dalili kake tmbyta ko laifine dan na dauki ya'ta
naje da ita
a sanyaye
yace a'ah amma dan Allah kiyi haquri kibarta
umma
ta tashi tana fadin baxan bartaba , suma duk
suka tashi sai alokacin umma tayi mgn
tace nasan komai baayinsa sai da dalili tor
meyasa xaki dauketa kije da ita alhali tana da miji
umma tace miji idan yaji baya iyawa sai ya
saketa mana
duka sun tsorata da kalamanta bakamar fulani ba
da tasoma girgixa kanta tana hawaye
umma tace kiduba kiga yanda ya'ta ta koma duk
ta rame batada wata walwala hr hasken ta
yasoma disashewa dama bada yawuna akayi
aurenba amincewar mahaifintane da xuciyar
maryam amma ita kanta fulani ba sonsa takeyi
ba
xuciyar momi na bace ta tsuke fuska
tace sai ynxu kikayi mgn data dace da amsar da
xn baki
bamuda wata alamar talauci takura ko tsanani
axaman takewarmu
masu aikinmu ki dubesu kigani kowacce na cikin
kwanciyar hankali kuma jikinsu alhmdllh babu
wacce take tareda yunwa ballantana ita matar
ubangidansu datake da iko akan komai na gidan
kada ayiwa gidanmu sharri da yunwa domin yarki
ta kasa kwantarda hankalinta ta xauna agidan
aurenta amma tunda kina ganin haka shiyafi kije
da ita ki gyarata da xuciyarta kibata duk wani
abu da muka rasa bata tunda an raina arxikinmu
umma tace shikenan xnje da ita din kuma inaso
marhoom ya aikomata takardar sakinta
momy tace insha Allahu xakiga takarda indai
marhoom nina haifesa inada iko akansa xaibar
yar'ku tunda ba ita kadai bace mace a duniya
dama bayaso aka aura umarni yabi kuma umarni
xaisa yabarmaku yar ku
fulani ta fashe da kuka

tace umma dan
Allah kiyi haquri nafasa xuwa xn x......tas kakeji
ta dauke fuskarta da mari
tace kedin banxa hr kin isa ki toxartani kacokan
nataso saboda k amma kikeso wulakantani kinyi
kadan kuma sai kinbar gidan
ta fisgeta suka juya
marhoom ya yunqura xai bisu
momy ta riqe masa hannu fuskarta a murtuqe
tana kuka tana waigensa
suna gab da fita falon
tace ina sonka marhoom.....umma ta fisgeta da
qarfi suka fita
jikinsa na soma rawa hawaye nason xubo masa
yace momy kiyi wani abu akai ki taimakamin
ta dubesa cike da bacin rai sai dai takasa furta
masa kalma ko daya tabar falon tayi dakinta
yana ganin haka yafito falon da saurinsa lokacin
sunja motar da qarfi suka bar harabar gidan.....

LABARI NAWhere stories live. Discover now